Results

YAR BARIKI book 2 page 25

Haris ya sunkuyar da kansa
"Eh,ta kwana biyu saidai baiyi wannan tsananin har haka ba sai yau. Nan ma kicin muka sameta kamar dai yanda na shaida maku."
Kallonsa tasleem tayi cikin jin bakin ciki,harma yana da bakin had'a zance haka? Alhaji yace "Subhanallah,toh Allah Ya bata lafiya."

Basu jima sosai ba,anti arya da juwairiyya suka shigo suma. Akarshe dai,Juwairiyya tace zata kwana,Haris yace sam, a barshi zai iya. Haka dai Abba yace a kyaleshi shi da matarsa.

Babu wata mu'amalar arziki data kasance tsakaninsu a daren. Yana kwance saman kafet tana saman gado,duk da fitila a kashe take,tana hangen fuskarsa sakamakon hasken farin watan daya hasko ta labulen dakin. Kwarai ba bacci yakeyi ba,ya kurawa silin ido kawai ne cikin tunanin da batasan ko na menene ba. Muskutawa tayi ta juya mishi baya a hankali kuma ta soma gyangyadi bacci ya sureta.

Washegari saida yamma aka sallamesu. Ita kam ji tayi kamar kada ta koma. Babu dai yanda ta iya,don batason surukanta su fahimci komai. Abbanta ma yazo,hakanan sunyi waya da Yasmeen sun kuma gaisa da Kb duk ta wayar Haris din don yanzu komai ya wuce tsakaninta da KB.
Kwana biyar da yin hakan ne,Haris na zaune cikin ofis dinsa cikin tsananin damuwa da tunanin matarsa yaji an kwankwasa kofa. Yayi umarnin a shigo,sakatariyarsa ce,ya sanar dashi yayi bak'o. Haris ya dubeta

"Please Linda,ki bashi hakuri,banajin zan iya saurarar kowa yanzu,kice ya dawo gobe."

Ta fita bayan ta amsa a ladabce,can sai gata ta dawo. Ya dubeta fuska daure,dakyar ta had'a haruffa
"Sorry Sir, yace ne maganar nada muhimmanci kuma idan ka bari ya tafi bazaka k'ara gan insa ba."

Haris ya dubeta na 'yan sakanni kafin ya jinjina kai
"Kice ya shigo."

Minti daya da fitar Linda, wani matashi yayi sallama cikin ofishin. Haris yayi tsai yana dubansa,kamar dai yasan wannan fuskar saidai kuma ya mance a inda ya santa. Matashin ya mik'awa Haris hannu yana mai yin sallama gareshi. Haris ya mik'a mishi sukayi musabaha sannan ya zauna.

"Nasan baka sanni ba ko?"
Haris ya gyada kansa
"Hakane,saidai kamar ba yau ne farkon ganina da fuskarnan ba. Kamar dai na sanka acan Badawa."

Matashin yayi dariya kadan
"Tabbas hakane,nidai sunana Hamza,dan nijar ne ni saidai ina aikin wanki da guga anan gidan dake makwaftaka da naka, gidan Alhaji Rabi'u Hassan."
Haris ya saki fus ka kadan

"Ok,na gane gidan,lafiya dai ko?"
Yayi tambayar cikin mamaki. Hamza ya numfasa
"Lafiya yallab'ai,saidai nazo maka da wani batu ne wanda tun sadda na aikata yake damuna kuma ya hanani sukuni,yanzu haka anjima kadan motarmu zata tashi zuwa nijar domin ziyarar yan uwa. Banaso na tafi ban nemi gafararka ba Yallabai."
Haris jin wannan batu ya k'ara gyara zama yana mai duban Hamza

"Fadamin kai tsaye,meka aikata gareni mai girma haka alhalin ma ba wata sanayya ko alak'a data shiga tsakaninmu?"
Hamza ya sadda kai ya soma magana
"Hakane,ina mai bakin cikin sanar maka cewar harda sanya hannuna a shiryawa matarka tuggu bayan daukar kusan sati biyu da mukayi muna neman hanyar hakan."
Haris fuskarsa ta sauya,cikin kausashshiyar murya yace
"Kayimin bayani dalla dalla yanda zan fahimta."

"A wataranar Talata ne,ina zaune bakin kofar gidan Alhaji ni d'aya,farko tare muke zaune da dan jummai maigadin alhaji sai ya tashi domin ya zagaya. Anan ne kuma sai ga wani matashin saurayi saman mashin yazo ya faka,bayan ya karewa area din kallo ya sauko saman mashin dinsa saida ya fiddo karan sigari ya kunna ya soma zuk'a kafin ya karaso gareni. Mukayi musabaha,kafin ya tambayeni
"Don Allah malam tambaya nakeyi?"
Na dubeshi kafin na bashi amsa
"Na'am,ina sauraronka."

"Gidan Haris Aliyu Kazaure nake nema."
Kamar yanda mukasan mafi akasarin mazauna wannan area din da kuma zaman hira da mukeyi wataran da ma'aikatan wajen ya sanya nasanka,ina dariya nace mishi

"Toh ai ga gidan nan kazo,wannan mai kallonka."
Na nunamishi da yatsa,ya daga kai ya kalla kafin yayi murmushi ya zauna gefena.
"Nagode abokina,idan babu damuwa akwai wani d'an karamin aikin da nakeso na sanyaka."

Kafin nayi magana ya zura hannu aljihun wandonsa ya fiddomin da bandir na kudi sabbi yan hamsin hamsin,ya sanyamin a tafin hannuna. Gaba daya na rude ganin wannan makudan kudaden,tunda nidai kam Allah Ya yoni da son kudi na kata'i,na dubeshi kafin na dubi hanya, unguwar shiru ba mutane,hakanan nasan Dan jummai bai isa ace ya fito daga bahaya yanzu ba,wannan yasa na dubeshi da sauri


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 25"

Post a comment