Results

YAR BARIKI book 2 page 26

"Kai kuwa abokina wane irin aiki ne zan maka?"
Yayi murmushi ya fesar da hayakin daya zuk'a kafin ya dubeni
"Kada ka damu,ba wani mai chaza kwakwalwa bane " Yasa hannu a aljihu ya fiddo wayarsa,saida yayi danne dannensa kafin ya mikomin

"Kasan wannan?" Na amshi wayar na kurawa hoton ido,nayi mamaki kwarai ganin hoton matarka kuma cikin kananun shiga bawai don ina k'are mata kallo bane don wata manufa daban,a'a saidai don kawai idan kun fito cikin mota nakan hangeta. Saida na kammala kallon kafin na mikamishi wayar ina gyada kaina
"Kwarai,na santa, matar Alhaji Haris din dai daka ambata a baya ne,mai wannan gidan "(Nayi nuni da gidan.)
Yayi murmushi

"So nakeyi ka samomin lambar mijinta inda hali duka numbers din nasa,na biyu kuma ka dunga sanarmin kowane shige da ficenta,duk sadda ta fita ka sanarmin ta waya."
Na dubeshi tsam,kafin nace
"Bangane ba. Me hakan zai amfaneka dashi?"
Yayi murmushi

"Sanya kudin nan a aljihu tukunna,banaso mutane su gane wani abu."
Nabi umarninsa kafin kuma ya warwaremin komai. Banyi wani ja inja ba na amince don na gode Allah ba kisan kai zai sakani ba.

Banci wuyar samun lambobinka ba wajen ma'aikatanka ba,nayita fakon Hajiya,da zarar ta fita zan sanarwa Manu,kamar yanda yacemin sunansa kenan. Har wajen sau uku,ana hudu ne nayi kiransa nace mu hadu. Bayan mun zauna na nemi sanin abunda yakeyi da fitarta,farko ya boyemin karshe ya tabbatar min gidan abokinsa ne babu nisa da nan kuma dole hanya daya ce ta fita daga layin nan,dole kuma motar ta fice ta hanyar gidan abokin nasa kamar dai yanda kasani lungun hanya daya a toshe take bata b'ullewa. Acewarsa akwai wani gagarumin laifi da tayimishi kuma ya rantse sai ya dauki fansa,na tsorata da jin haka domin a zatona kasheta zaiyi. Yayi dariya ganin yanayina,yace kada na damu ba wani abun bane mai hatsari. Ya karamin kudi yace na daure na cigaba na kuma yi hakuri don duk fitar da takeyi baya wani cin nasara don wani sa'in gidansu take nufa shi kuwa bayason kowa ya ganshi a wadanda ta sani gudun rugujewar aikinsa.
Akarshe akayi nasara rannan Hajiya ta fito,nayi kiransa na sanarmishi. Tun daga wannan lokacin shiru bai kara nemana ba sai washegari ya kirani cikin nishadi yayimin godiya yace ya kammala aikinsa,nikam jikina yayi sanyi na rasa menene ya aikata saidai inda hankalina ya kwanta ganin dawowar Hajiya a ranar kuma lafiya lau. Saidai ranar da lamarin ya faru na gobara data kusan tashi,bayan tafiyarkune asibiti,baba maigadi ke labartamin daman fa sun lura kwana biyu hajiyartasu babu walwala hakanan ma maigidan. Sun rasa gane abunda ya kawo wannan chanji a gidan."

Hamza cike da nadama ya dubi Haris
"Wallahi tun anan nasha jinin jikina,nayi nadamar aikata wannan abu kuma nake zargin kaina da lalata farincikin gidanka....!! Banci wuyar samun lambobinka ba wajen ma'aikatanka ba,nayita fakon Hajiya,da zarar ta fita zan sanarwa Manu,kamar yanda yacemin sunansa kenan. Har wajen sau uku,ana hudu ne nayi kiransa nace mu hadu. Bayan mun zauna na nemi sanin abunda yakeyi da fitarta,farko ya boyemin karshe ya tabbatar min gidan abokinsa ne babu nisa da nan kuma dole hanya daya ce ta fita daga layin nan,dole kuma motar ta fice ta hanyar gidan abokin nasa kamar dai yanda kasani lungun hanya daya a toshe take bata b'ullewa. Acewarsa akwai wani gagarumin laifi da tayimishi kuma ya rantse sai ya dauki fansa,na tsorata da jin haka domin a zatona kasheta zaiyi. Yayi dariya ganin yanayina,yace kada na damu ba wani abun bane mai hatsari. Ya karamin kudi yace na daure na cigaba na kuma yi hakuri don duk fitar da takeyi baya wani cin nasara don wani sa'in gidansu take nufa shi kuwa bayason kowa ya ganshi a wadanda ta sani gudun rugujewar aikinsa.

Akarshe akayi nasara rannan Hajiya ta fito,nayi kiransa na sanarmishi. Tun daga wannan lokacin shiru bai kara nemana ba sai washegari ya kirani cikin nishadi yayimin godiya yace ya kammala aikinsa,nikam jikina yayi sanyi na rasa menene ya aikata saidai inda hankalina ya kwanta ganin dawowar Hajiya a ranar kuma lafiya lau. Saidai ranar da lamarin ya faru na gobara data kusan tashi,bayan tafiyarkune asibiti,baba maigadi ke labartamin daman fa sun lura kwana biyu hajiyartasu babu walwala hakanan ma maigidan. Sun rasa gane abunda ya kawo wannan chanji a gidan."

Hamza cike da nadama ya dubi Haris
"Wallahi tun anan nasha jinin jikina,nayi nadamar aikata wannan abu kuma nake zargin kaina da lalata farincikin gidanka....!!*******

Fuskar Haris tayi jazur yayinda idanunsa suka kad'a kwarai tsikar jikinsa ta tashi. Ya dafe kansa saboda yanda yaji yana sarawa.
"Allah da ManzonSa s.a.w,sun hanemu da zargi. Yakan kawo mutuwar aure kwarai dagaske,kada ka yankemin hukuncin abunda bani da hakki ciki,kada ka zargeni my king. Ashe daman son da kakeyimin iyakarsa lebba? Ashe zaka iya zargina bisa abunda baka da tabbas? Ina rantsuwa da..."
Bai mance sadda ya yanke maganarta ba ta hanyar daka mata tsawa

"Keep quiet you stupid! Kina daukana sakarai ne?! Kina daukana wanda baisan abunda yakeyi ba?! Wallahi nafi karfin ki rainamin hankali Tasleem."

Bai mance sadda ta koma kuryar dakinsa a guje ba tabar falon,a ranar bai runtsa ba.
Yana kaiwa nan ya bugi tebur da karfi
"No!!!!" Ya fada cikin daga murya wanda ya kad'a hantar cikin Hamza dake zaune yayi tsuru da ido. Ya mike a tsorace saidai ba zato yaji Haris ya cakumi wuyan

rigarsa,cikin kausassan murya yace
"Meyasa kuka cutar dan i har haka? Don ubanka wanene shi? Har nawa ne dashi da zai baka abunda zaisa ka cutar da rayuwata dana iyalina?!" Hamza ya rude ya hau had'ashi da Allah da ManzonSa s.a.w akan ya tuba bazai sake ba. Dakyar ya turashi ya zube k'asa gefen kujera. Haris ya juya yana tunano ire iren rashin mutunci da cin kashin da ya dunga yi mata duk akan abunda bai kai ya kawo ba! Ya runtse ido,sai ga hawaye sun zubo. Ya juyo a fusace ya dubi Hamza wanda yakeji kamar ya saki fitsari a wando

"Kasan gidan abokin nasa?"
Hamza ya gyada kai  da sauri

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 26"

Post a comment