Results

YAR BARIKI book 2 page 27

"Na sani yallab'ai,saidai don Allah kayimin alfarma na kaika na juya na tafi,wallahi ya gargadeni akan kada na sanarwa kowa,muddin kuwa ya ganmu tare zai iya yimin komai."
Haris ya harareshi
"Kasan da haka ka aikata tun farko? Wallahi kafata kafarka."
******

Bayan sun soma tafiya,kai tsaye Haris bai zarce ko'ina ba sai police station. Wajen wani dan uwan abokinnan nasa ya nufa a ofishin,inspector Bashir,bayan sun gaisa ya sanarmishi abunda ya faru,Inspector Bashir cike da mamaki yace "Ya Salam,wannan masifa dame tayi kama? Abubuwa kala kala har haka?"
Inspector ya dubi Hamza

"Da gaskiyar Haris,ya zama lallai ka zauna agarinnan har sai komai ya kammalu,tunda yace ya yafemaka tunda ka nuna kayi nadama shikenan. Amma dole ka tsaya har sai Manu yazo hannunmu."

Daga haka ya dubi Haris
"Haris,kayi hakuri har zuwa safiyar gobe sai muje gidan,a yau akwai case na wasu kadangarun bariki da zamu mik'a kotu ne,in sha Allah I promise you,wannan yaron zaizo hannunmu za kuma a hukuntashi. Shi kuma wannan dole ayau ya kwana hannunmu gudun samun matsala. Cool your mind please, everything will be okay in sha Allah."

Haris wanda kallo daya zai tabbatar maka baya a hayyacinsa,ya gyada kanshi.

"Ba damuwa Bash,Allah Ya kaimu."
Daga haka sukayi sallama,Haris ya tafi yabar Hamza wanda yakeji kamar ya fashe da kuka adalilin kwanan kaso da zaiyi.

Shi kuwa Haris a mota ya tarar da missedcalls din Abba har uku wanda ya tabbatar mishi cewar lallai ya fahimci yabar ofis. Niyyarsa ya zarce gidansa domin burinsa na tozali da Tasleem ya nemi gafararta,saidai sanin da yayi sunada meeting mai zafi yasa dolensa ya koma ofis din nasu......!!

Ba shine yaje gida ba sai bayan magrib,kasancewar ranar Alhamis ce yana azumi. Farin ciki sosai yakeyi na kasantuwar ranar Tasleem keda girki. Kai tsaye ya nufi samansa,duk da yaji rashin dadi da bai isketa a falo ba kamar yanda takeyi mishi a baya ba,saidai ya dan ji sanyin da yaga bata fasa girka mishi kayan bud'a baki ba duk kuwa da cewar kwanakin nan ta daina yi mishi girki sakamakon koda tayi baya ci hakanan take daukewa. Da safe ma ko kayan karin kumallo baya kalla. Haka dai yana tunaninta yana rage suturar dake jikinsa,don kuwa yayi sallah yaci dabino uku a hanya ya kuma sha ruwa.

Tausayin matarsa ya mamayeshi,wayarsa ya dauka ya danna mata kira. Lokacin tana karatun Alkur'ani mai tsarki ga kuma hawaye kwance saman fuskarta,ta d'an dubi wayar kad'an,ganin lambarsa ta dauke kanta ta cigaba da karatunta yayinda zubar hawayenta ya k'aru na tausayawa rayuwarta. Wai yaushe zata daina ganin 

wadannan jarrabobin ne? Yaushe ne haske zai mamayi rayuwarta? Ta sani,akwai wadanda suka fita shiga mawuyacin hali,akwai wadanda idan da ace yau zata gansu ta kuma ga halin da suke ciki kwarai sai ta fahimci nata bama wani tashin hankali bane ba. Ina wadanda rayuwarsu ke k'arewa a masifu? Ina wadanda Allah bai basu shiriya ba har zuwa mutuwarsu? Ina kuma wadanda basu samu koda kwatan gatan data samu ba?

Hawayenta ya karu ainun har bataji murd'a k'ofa da shigowar mutum ba,saidai kawai ji tayi an tallafo fuskarta da hannu biyu. Saida ta razana,ganin shine ta sauke ajiyar 

zuciya,hawaye taga suna fita daga idanunsa,sukayiwa juna k'uri da ido cike da wannan boyayyen sirri na kauna da soyayya. A bangare daya tsananin mamaki ne ya cika zuciyar Tasleem,bata farga da cewar ba'a cikin mafarki hakan ke kasancewa ba har saida taji fatar bakinsa na gogayya da nata. Kamar wacce lantarkin wuta yaja,ta mike zumbur cikin 

tsananin fusata. Ta rungume Al-kur'anin dake a hannunta tana cigaba da zubda hawayenta yayinda take binsa da kallo na bacin rai.
Daga shi sai singilet da dogon wando na Adidas,ya mike yana nufota yace
"My Queen please.."

Tayi azamar nunashi da yatsa
"Ina maka rantsuwa da Allah idan ka matso inda nake sai nayi maka rauni HARIS! Fitarmin daga d'aki! Bana sonka! Bana kaunar ganinka!"

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 27"

Post a comment