Results

YAR BARIKI book 2 page 28


"Ba damuwa Bash,Allah Ya kaimu."
Daga haka sukayi sallama,Haris ya tafi yabar Hamza wanda yakeji kamar ya fashe da kuka adalilin kwanan kaso da zaiyi.
Shi kuwa Haris a mota ya tarar da missedcalls din Abba har uku wanda ya tabbatar mishi cewar lallai ya fahimci yabar ofis. Niyyarsa ya zarce gidansa domin burinsa na tozali da Tasleem ya nemi gafararta,saidai sanin da yayi sunada meeting mai zafi yasa dolensa ya koma ofis din nasu......!!

Ba shine yaje gida ba sai bayan magrib,kasancewar ranar Alhamis ce yana azumi. Farin ciki sosai yakeyi na kasantuwar ranar Tasleem keda girki. Kai tsaye ya nufi samansa,duk da yaji rashin dadi da bai isketa a falo ba kamar yanda takeyi mishi a baya ba,saidai ya dan ji sanyin da yaga bata fasa girka mishi kayan bud'a baki ba duk kuwa da cewar kwanakin nan ta daina yi mishi girki sakamakon koda tayi baya ci hakanan take daukewa. Da safe ma ko kayan karin kumallo baya kalla. 

Haka dai yana tunaninta yana rage suturar dake jikinsa,don kuwa yayi sallah yaci dabino uku a hanya ya kuma sha ruwa.
Tausayin matarsa ya mamayeshi,wayarsa ya dauka ya danna mata kira. Lokacin tana karatun Alkur'ani mai tsarki ga kuma hawaye kwance saman fuskarta,ta d'an dubi wayar kad'an,ganin lambarsa ta dauke kanta ta cigaba da karatunta yayinda zubar hawayenta ya k'aru na tausayawa rayuwarta. Wai yaushe zata daina ganin wadannan jarrabobin ne? Yaushe ne haske zai mamayi rayuwarta? Ta sani,akwai wadanda suka fita shiga mawuyacin hali,akwai wadanda idan da ace yau zata gansu ta kuma ga halin da suke ciki kwarai sai ta fahimci nata bama wani tashin hankali bane ba. Ina wadanda rayuwarsu ke k'arewa a masifu? Ina wadanda Allah bai basu shiriya ba har zuwa mutuwarsu? Ina kuma wadanda basu samu koda kwatan gatan data samu ba?

Hawayenta ya karu ainun har bataji murd'a k'ofa da shigowar mutum ba,saidai kawai ji tayi an tallafo fuskarta da hannu biyu. Saida ta razana,ganin shine ta sauke ajiyar zuciya,hawaye taga suna fita daga idanunsa,sukayiwa juna k'uri da ido cike da wannan boyayyen sirri na kauna da soyayya. 

A bangare daya tsananin mamaki ne ya cika zuciyar Tasleem,bata farga da cewar ba'a cikin mafarki hakan ke kasancewa ba har saida taji fatar bakinsa na gogayya da nata. Kamar wacce lantarkin wuta yaja,ta mike zumbur cikin tsananin fusata. Ta rungume Al-kur'anin dake a hannunta tana cigaba da zubda hawayenta yayinda take binsa da kallo na bacin rai.

Daga shi sai singilet da dogon wando na Adidas,ya mike yana nufota yace
"My Queen please.."
Tayi azamar nunashi da yatsa
"Ina maka rantsuwa da Allah idan ka matso inda nake sai nayi maka rauni HARIS! Fitarmin daga d'aki! Bana sonka! Bana kaunar ganinka!"

Tana wannan furucin ne cikin tsawa da kuka,bai dauka da gasken takeyi ba duk da dai kirjinsa ya danyi nauyi na jin ta kirayi sunansa kai tsaye,"Haris?" Ya maimaita a ransa, ya k'ara takowa yana nufarta
"My Queen,nasan ni Haris mai laifuka...aush!!"

Sauran maganar ta kasa fita sakamakon karamin flower vase da tayomishu wurgi dashi wanda cikin sa'a sai a goshinsa,ba shiri ya tsaya yana mai rike goshinsa gami da sakin karamin ihu. Da gudu tayi dakinta ta saka mukulli tana kuka sosai. Haris ya kwareta,ya sakata cikin kunci da bakin ciki. Tana jinsa yana bubbuga kofar har ya gaji ya daina ya zube shima a bakin kofar yana maganganu.

"Ki yafemin Queen,ki gafartamin,nayi maki gagarumin laifin dana cancanci hukinci fiye da haka. Na b'ata miki farincikinki alhalin baki da hakki cikin abunda zargi ne kawai nakeyi,domin Allah Queen kiyimin aikin gafara ki bude kofar ki saurareni."
Tasleem ta share hawayenta saidai tuna wasu hawayen suka maye gurbun wadancan,tana mai girgiza kanta kamar yana ganinta tace

"Babu sauran abunda ya rage naji ko kuma na gani daga gareka,babu abunda yayi saura wanda zaka sanarmin harma na yarda dakai. Ka bani mamaki Haris,ka bani mamaki kwarai dagaske,banyi zaton zaka iya yimin wannan cin fuskar ba,ban kuma tab'a sanin baka gama yarda dani ba dari bisa dari kamar kake yawan ikrari."

Ta girgiza kanta tana mai daga yatsanta guda sai kace yana kallonta
"Rana d'aya kawai! Komai ya chanza,daga ganin hotuna,ba tare daka nemi jin ta bakina ba,ba kuma tare daka nemi jin dalilin zuwana shopping ba,ka gaggasamin maganganu. 

Toh ni kuma inason sanarmaka da cewar na gaji da zama tare dakai. Bazan iya cigaba da zama da mutumin daya kasa yarda dani ba. Mutum irinka mai saurin zargin iyalinsa,wanda bai yarda cewar iyalinsa zasu iya tsare mutuncin aurensu ba a ko'ina. Bazan iya zama dakai ba,na gaji ka barni na koma gidanmu!"
Buga kofar da yayi, ya tsorata
"Karya kikeyi Tasleem! We can't leave without each other! Wallahi bazan sakeki ba har mutuwata! Ina sonki! Ina sonki!!" 

Yana maganar a fusace,sai kuma ya sassauto don kansa
"Please Queen karki barni na mutu! Please ki budemin,ki yafemin Queen, ki yafemin."
Tasleem kuka takeyi kamar ranta zai fita, a zuciyarta godewa Allah takeyi kawai daya amshi addu'arta,Ya tona asiri. Da Ya wanketa bisa wannan zargin da mijinta yakeyi gareta. 

A gefe guda matsanancin so da kuma kauna ta gaskiya ta mijinta ne ya mamayeta,ga tsananin tausayinsa. Saidai kuma tunano da yanda ya dunga gasa mata munanan kalamai yasa ta fasa niyyarta na bude kofa,ta mike ta ajiye Al-kur'anin ta fad'a band'aki.

Koda ta fito bataji motsinsa a wajen ba,daman tasan bazai juri zaman jiranta ba,mutumin da yayi azumi? Kuma ta tabbata ko abinci baici ba. Sallarta ta tayar, bayan ta idar tayi shafa'i da wutri kafin ta hau godiya ga Mahaliccinta da kirari agareShi.( Bashakka ya dace mata da maza su gane,domin a wannan zamanin ma daidai da mazan sukan kauce hanya da bin bokaye domin neman bukatunsu,toh wallahi idann da ace zasu gane su tashi tsaye da kansu suyita rok'on Allah,su hana idanuwansu bacci,toh alal hakika babu wani abu da yafi karfin Mahaliccinmu,komai daren dad'ewa Allah zai amsa musu. Domin kuwa ba'a samun biyan bukata ta sauki har sai an mike tsaye da ibada. Wataran komai zai zama labari! Allah Ya datar damu,amin.!)

****
Koda ta kammala,ta bud'e kofar a sannu sannu,babu kowa a falon,wannan ne ya bata damar fitowa gaba daya. Saidai me? Hab'ar mutum taji saman kafadarta ta dama,ya zagayeta da hannunsa. A sannu kuma taji ruwan hawaye yana zubowa bisa kafad'arta,cikin murya raunanniya kamar bata jarumin Haris ba ya soma magana
"Kirjina zai tarwatse Tasleem,ina neman zaucewa,ki taimaka ki tausayawa rayuwata,ki gafarceni. Dukkan wani dan adam ajizi ne,ban tab'ayi maki irin haka ba,ki daure kiyimin uzuri. Ki yafemin please and please."

Lumshe ido tayi cike da jin tsananin tausayin mijinta, saidai komai ya kwance mata sadda ta tuno da irin hargitsin data shiga duk a sanadiyyarsa. Take ta sanya hannuwanta ta dauke nashi,kafin ta goce bata yarda ta dubeshi ba ta koma saman kujera ta zauna. Ba tare da gajiyawa ba ya biyo bayanta,gwuiwoyinsa dukufe a kan kafet,yayinda tausasan hannuwansa suke a saman cinyoyinta. 

Duk yanda yaso na ganin sun hada idanu wuri daya amma hakan bai samu ba. Kanta yana k'asa hawayenta suna zuba saman hannayensa. Cikin dusashshiyar muryarta kamar mai fama da mura tace
"Ka jima kana azabtar dani,ka jima kana sakani cikin kunci da bakinciki."

Sai lokacin ta dago kanta ta dubeshi gami da daga yatsunta biyu 
"Saboda dalili d'aya tak na kaddara! Wanda bai wuce fad'awa kan kowa ba? Saboda kasancewata YAR BARIKI a baya? Ashe daman idan mutum ya tuba yayi aure bazai daina fuskantar kalubale dangane da abunda ya riga ya wuce ba? Abun bakin cikin ma ya kasance mijinka wanda kake fatan ku kasance har abada tare shine mai zarginka harma yake fadin daman yasan mai hali bai fasa halin..."

Hannu yasa cikin matsanancin tashin hankali ya rufe bakinta,kai kawai yake girgiza mata. Dakyar ya samu damar magana
"Ina rantsewa da Allah ban tab'a so da kaunar wani abu ba kamar yanda nakeso da kaunarki Tasleem. Wallahi alokacin da nayi wadannan munanan kalaman gareki bana cikin nutsuwa da hayyacina,Tasleem meyasa bazaki fahimci cewar ina tsananin kishinki ba? Meyasa bazaki gane idan babu ke babu amfanin rayuwata bane? Ya kamata zuwa yanzu ki gane Haris naki ne,Haris yafi gaban kowane dan adam awajenki. 

Akanki banajin zan iya hakuri,tasleem I trust you more than how I trust myself. Saidai wallahi sadda naci karo da hotunan nan,yanda wai matar da nakeso nake kauna ce ta tsaya bainar jama a tare da abokin watsewarta na baya suke hira abun it pains."

Tasleem tayi murmushi mai ciwo kafin ta kauda kanta gefe,cikin nutsuwa ta labarta mishi dukkan abunda ya faru bata k'ara ko kuma rage komai ba. Saida ta dasa aya kafin ta dubeshi

"Ko acan baya,Baaba baya cikin irin mazan da zanyi tarayya dasu, ballantana yanzu kuma da nake da aure nasan mutunci da kimarsa."

Haris ya numfasa,sai lokacin ta lura da durkuson da yayi,hannunta tasanya cikin nashi ta dagoshi,ya zauna gefenta ya karkato gabadaya yana fuskantarta. Yayinda ta cigaba da magana
"20th April,rana ce ta birthday dinka idan baka manta ba King,fitar da nayi domin ba siyo maka gift ne."

Ta mike da azama ta nufi daki,can sai gata ta fito da leda. Zazzage kayan cikinsa tayi,agogo ne a cikin gidansa ruwan silver mai kyawun gaske,sai takalmi mai kyau,da flower da kuma cards. Ta dubeshi yayinda ya tsurawa kayan ido cike da nadama tsantsa na abunda ya aikata gareta.

"Idan baka manta ba,koda ka shigo sashena a ranar fitilu a kashr suke,da ace ka lura zaka ga kwalliyar da nayi dominka King,da ace kuma ka saurareni da zaka gane cewa bani da laifi. Saidai duk hankalinka baikai nan ba,ta inda ka shiga.."
Katseta yayi inda ya shiga aikamata da zafafan sakonni,batayi yunkurin hanashi ba domin bata da wannan kuzarin. Don kansa ya bari ya sanyata jikinsa,a sannu yake shafa gashinta,sai kuma ya soma magana

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to " YAR BARIKI book 2 page 28"

Post a comment