Results

YAR BARIKI book 2 page 29

"Nayi babban kuskure Queen,tuba nakeyi in sha Allah bazan k'ara ba. Ayau ina zaune a ofis ne.."
Ya labarta mata yanda ya gano gaskiya da kuma shigar da case din hannun hukuma da yayi. Ta jinjina zancen,ta dago kanta ta dubeshi cike da mamaki

"Ikon Allah kaga kuwa nama mance da marinsa dana tab'ayi,domin idan ban manta bama,ranar kaine ka batamin rai, inda kaketa bibiyata a hanya randa na hau motar KB azatonka shine aciki. Toh ranar ne yaban haushi na mareshi. Wallahi na manta anyima hakan."

Haris yayi murmushi
"Rabu da dan iska,mugodewa Allah da bai rabamu ba adalilin hakan,yayi saurin bayyana mana gaskiya."
Ta gyada kanta tana mai hamdala,tsakanin fa mata da miji sai Allah. Nan suka sasanta akarshe dakyar ta jashi zuwa sama domin yasha ruwa...!

A wannan daren sun tabbatarwa da kansu lallai sunyi mugun kewar junansu,haka kuma bazasu iya rayuwa ba tare ba. Domin kuwa ba Tasleem ba,daidai da shi kansa Haris din,yayi wata iriyar rama ainun fuskarnan tasa ta k'ara sirancewa sai hancinsa ya k'ara fitowa d'abas. Ta tallafo hab'ansa bayan data kammala taimaka mishi da sanya takalmi
"Ka rame sosai my king."
Ya kama hannuwanta
"Kin fini rama my queen,kodai kin samo mana baby ne?"

Tayi murmushi kafin cikin wasa ta harareshi
"Nikam banida komai."
"Shine kalmar da ni kuma na tsana my queen, nafiso kiyi komai."
Ya k'arashe yana kai hannu cikinta,tana murmushi tace

"Sai mu cigaba da addu'a my king,komai lokaci gareshi. Allah Ya kawo masu albarka,Ya sauki sisna lafiya."
Ya amsa da amin kafin su jera su fito falon.
******

Kai tsaye Haris police station ya soma nufa. Cikin sa'a kuwa ya hadu da inspector yana jiranshi. Su biyu ne a motar,sai Hamza cikon na uku. A bayansu kuwa motar jami'an tsaro ne guda daya, suna tafe bisa bin umarnin ogansu,ko jiniya basu kunna ba.

Inspector Bashir ne ke bawa Haris labarin case dinsu na jiya
"Wato ita wannan mai suna Momi,itace shugabansu,ita keda alhakin had'asu da manya manyan dattijan banza na nahiyar nan,masu ji da dukiya. Wallahi wata idan ka ganta sai abun ya baka haushi,don kuwa bata wuce ace tana gidan mijinta ko kuma tana karatu ba wallahi. Toh yanzu dai matsalar da suka samu,bai wuce na kashe Alhaji Kwangila ba,na nan hanyar kasuwa ba,sanadin haka asirinsu ya tonu.

Sun hadashi da yarinya mai kanjamau,yace zai dauki fansa akan ita yarinyar da Momi din,shine wasu tantirai wai Dalal da Hibba suka bada shawarar a kasheshi,yanzu bayan ya mutu mukayi nasarar cafkesu. Alkali ya yankewa Samuel din da yaransa hukuncin kisa, ita kuwa Momi da jama'arta hukuncin shekaru a gidan yari da horo mai tsanani. Saidai kuma a jiyan dai muka samu labarin ita Hibbar ta mutu ne bayan da wani saurayi yayi amfani da ita harma ya fiddamata sassan mamanta guda. Haka dai mutuwar wu lakanci."

Inspector Bash yana kaiwa nan ba tare da ya lura da yanayin dake saman fuskar Haris ba na d'imuwa ya girgiza kai
"Toh menene amfanin haka? Mutane suna kai kansu ga halaka da kansu,cases iri daban daban gasunan muna gani lamarin saidai du'ai."
Hamza ya amsa da cewa
"Hakane yallabai."

Haris kuwa ya girgiza da jin wannan labarin,lallai Tasleem ta k'ara godewa Allah da hakan bai zamo harda ita a ciki ba. Yanzu Hibba ta rasu? Allahu Akbar,duniya abar tsori ce,shakka babu!

Haka dai har suka karasa ga gidan abokin Baaba(Manu) kamar yanda Hamza ya sanar dasu. Bayan sunyi fakin,Inspector ya umarci yaransa akan suyi jiransu kada su fito. Su uku ne suka soma shiga gidan. Anan farfajiyar gidan sukaci karo da wani matashi yana shirin shiga mota, ganinsu yasa ya fasa ya zubamusu ido,kwarai ya gane Hamza saidai ya basar. Bai kawo jami'an tsaro bane,don kuwa Inspector bai sanya uniform ba. Hannu suka mik'amai,sukayi musabaha.

Ya dubesu
"Lafiya dai ko?"
Hamza ya dubeshi
"Lafiya kalau,Nura baka ganeni bane?"
Matashin da aka kira da Nura ya dubeshi kad'an,kafin ya girgiza kanshi yana murmushi na 'yan duniya


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 29"

Post a comment