Results

YAR BARIKI book 2 page 30

"Ikon Allah,gashi dai da alama ka sanni tunda har ka ambaci sunana saidai kuma ni koda wasa bansanka ba."
Haris ya dubi inspector, inspector yayi murmushi kafin ya dubi Hamza
"Wannan shine abokin Manu?"
Hamza ya gyada kai
"Kwarai kuwa Yallab'ai,shine Nura abokinsa."

Nura ya yamutse fuska
"Wanene kuma Manu? Bani da aboki mai wannan sunan."
"Idan bakasan Manu ba,bana tsammanin zaka kasa sanin Baaba ko?"

Cewar Haris,gaban Nura ya fad'i,toh shi kuma wannan ta yaya yasan sunan Baaba? Ya daure ya girgiza kansa
"Nifa kun sakani a duhu,duk bani da masaniya game da maganarku."

Inspector Bash ya jinjina kai kafin ya juyo yakai mishi naushi a baki,sai a police station!
*****

Nura zaune yayi jina jina,yayinda inspector bash yake saman kujera zaune,ga Hamza gefensa. Haris kuwa,inspector ya mishi umarnin komawa bakin aikinsa tare da alk'awarin komai zaizo karshe.
Inspector ya dubi Nura wanda hanci da bakinsa ke fidda jini yace
"Ka shirya fadamin gaskiya ko kuwa sai na illata kafafunka?"

Nura baya fatan dukan da inspector yayi mishi yafi wannan,dole ya sanar mishu gaskiya,akan cewar da hadin bakinsa komai ya shiryu. Shine ma ya bawa Baaba shawarar chanza suna,hakanan shine ya samo mishi wani yaro mai suna Tasi'u domin taimaka mishi wajen yin hotuna,a karshe suka biyashi ya tafi.
Inspector ya jinjina kai

"Ok,yanzu ina kake ganin zamu samu Baaba?"
Nura yayi shiru kafin ya dubi inspector yace
"Ina da tabbacin yana garin nan,kuma yafi zama a Tahir Guest Palace. Fitar da kuka tarar zanyi ma,wajenshi zan nufa saboda ya sanarmin ya samar mana wa su bebs."

Inspector ya tabe baki
"Bebs? Kune masu lalata yaranmu ko? Ok,tashi muje."
****
Basu ci wuyar cafke Baaba anan hotel din ba. Haka dai Baaba yayita hararar Hamza mai wanki,shi dai Hamza lamarin yayi mishi dadi sakamakon sallamarshi da inspector bash yayi suna komawa station.


Haris yana tasowa daga gurin aiki ya nufi station din. Ya tabbatarwa da inspector lallai shine dai na jikin hoton, yayinda ya koma motarsa ya kawo hotunan ya damkawa inspector.

A karshe sukayi sallama bayan inspector ya tabbatar mishi lallai za'a horasu. Jin haka Baaba ya shiga neman gafara saidai bakin alkalami ya riga ya bushe!
*****
BAYAN WUYA....!
Tun daga wannan ranar,komai na rayuwa ya chanjawa wadannan ma'auratan,komai yayi musu dadi. Hakanan,a fannin ita Tasleem da Zahra,kai ka rantse ba kishiyoyi bane ta yanda kowannensu ya rik'i dan uwansa da zuciya d'aya. Cikin wannan zama ne,KB da Yasmeen sukazo Kano. Kamar hadin baki,sai ga Yaya Abdullah da Hasina kai harma da Hindatu sunzo hutun karshen mako. Nan fa suka hadu a gidan Daddy,akayita hira ana dariya.

 Yasmeen sam bata rik'e Tasleem azuciya ba,gaba d'aya saita watsar da komai. Zahra tuni cikinta yakai watanni biyu,sai tsokanarta Tasle takeyi. A karshe dai su Daddy suka shigo, nan aka hadu akayi zaman cin abinci anayi ana hira kafin daga bisani su Yaya Abdullah sukayi shirin tafiya,nan dai sukayi musu sallama. Sai bayan da sukayo musu rakiya ne,Hasina ke bawa Tasleem labarin wani saurayi daya fito yanason Hindatu,shima iyayensa anan Abuja suke hakanan yanzu lecturer ne acikin jami'ar ta Abuja. Tasleem ta jinjina lamarin

"Karatun fa?"
Hindatu tayi dar iya kadan

"Ai sunyi magana da Yaya Abdullah,yace da zarar na kammala degree sai ayi magana,shi bashi da damuwa sai na k'arasa a dakina."

Tasleem taji dadi tayi mata fatan alheri.
Bayan tafiyarsu suma sukayi sallama dasu Daddy suka nufi gidajensu. A mota Zahra ta matsa tanason cin shawarma,dole Haris ya karkata kan mota ya nufi L&Z. Tasleem tana ta dariya.


Saida ya shiga ya siyo sannan suka nufi gida.
*****
Zumunci sosai ya kankama tsakanin Hamida da Tasleem tamkar babu wani sab'ani da ya tab'a shiga tsakaninsu. Addu'o'i sosai tasleem ta bawa Hamidah,a yanzu kam bata wasa da ibada cikin ikon Allah abubuwa da dama sukayi sauki gareta har taji nutsuwa ta ziyarci zuciyarta game da mijinta. Hakanan kishiyoyinta sun daina shiga harkarta,kowa tasa ta fishsheshin

Hakanan ga Abban tasleem,ya warke sumul ya cigaba da aikinsa,shi kansa yaso Tasleem ta karasa karatunta na shari'ah saidai bai zurfafa ba ya hakura jin cewar Haris baya ra'ayin hakan.

Cikin Zahra yana da watanni hud'u,akayi bikin juwairiyya diyar waziri,budurin da akayi ba kadan bane,domin daidai da Mamma ta samu halarta. Humaira ta k'ara wayo kamar wacce sukayi shekara basu hadu ba. Taslewm don farincikin ganin Mamma rasa inda zatasa ranta tayi.

Kwana biyu da kammala bikin ne,Mamma ta nemi da Tasleem tayi mata rakiya wani wuri,Tasleem ta nemi iznin Haris yayi na'am. Itace take jan motar yayinda Mamma ke kwatanta mata inda zasuje cikin unguwar Tarauni. Tasleem tana son tariyo wajen wacce ta sani a area din saidai da ta kasa tunanowa,hardai ga mamakinta taga mamma ta umarceta data faka kofar wani gida. Kwallah suka cikawa Tasleem ido,ta washe baki

"Kulu? Mamma ai nan gidansu Kulu ne."
Kwarai nan dinne kuwa,domin babu abunda ya chanza. Mamma ta jinjina kanta

"Banajin gidansu Kulu zai b'acemin,nayi mamakin yanda kuka yada zumunci da matar data rikeku bisa amana."
Tana fadin haka ta bude motar ta fita. A sanyaye Tasleem ta fito sannan ta budewa Humaira itama ta fito. Tuni Mamma ta shige, suka rufamata baya da sallama. Mutanen gidan suka amsa,kamar ma wani taron akeyi bisa la'akari da taron mutane sunci ado. Ganin bak'in fuska yasa suketa binsu da kallo,suna cikin gaisawa ne,saiga matar d'an gidan kulu ta fito. Wata tace
"Ga mai jegon nan ma."

Suka dubeta,tabbas Tasleem bata mance fuskarta ba,Sadiya ce diyar d'an Kulu. Suka gaisa,Mamma tayi mata barka kafin ta tambayi Kulu. Tayi musu jagora har dakin Kulu. Nan dinma cike yake da mutane,abunda ya bawa Tasleem mamaki,bai wuce na yanda Sadiya ta durkusa a ladabce ta shaidawa Kulu tayi bak'i ba,alhalin yanda a baya ta rainata take wulakantata. Kulu na ganin Mamma,suka rungume juna sai kukan murna. Kallo ya dawo kansu,kafin ta saki Mamma ta kamo hannun Tasleem har jikinta yana rawa
"Ikon Allah kenan,kada dai wannan Tasleem ce?"
"Ni ce Kulu."

Cike da farin ciki ta jasu ciki. Nan fa hira ta b'arke bayan mutanen dakin sun basu waje,tayi kuka sosai jin labarin abunda yasa Tasleem gudowa daga gidan mahaifinta tazo wajenta da kuma abunda ya kasance a rayuwarta na baya. Saidai jin tayi aure abun yayi mata dadi kwarai tayita hamdala. Nan ma ta jiwa Mamma dadin auren da tayi. Ta kuma jinjina yanda rayuwar Raliya da yaranta suka k'are. Alheri mai yawa Mamma tayi mata,akarshe ta karb'i lambarta,hakanan itama Tasleem tayi mata alkawarin zuwa jefi jefi,a inda tace har yau uwa take awajenta. Haka dai suka rabu bayan sun shiga sunga yaro sunyiwa mamansa alheri.
*****

A kwana a tashi babu wuya wajen Ubangijin al'arshi,sai gashi har Zahra ta shiga watanta na tara cif. Kulawa kuwa,sai a rasa wanda yafi wani tsakanin surukai da mijin da kuma abokiyar zamanta,Tasleem. Don sai ace ma ta fisu rawar k'afa da d'oki,hakanan saboda tsananin kaunarta da yara yasa kodayaushe itama addu'arta Allah Ya bata ciki ta haihu. Komai na aiki ta hana Zahra,duk da dai zuwa lokacin akwai yarinyar dake tare da ita, hakan baya hana Tasleem taimaka mata.

Wata ranar asabar da yammaci,suna zaune a falon Haris da rana bayan kammala cin abinci suna hira da dariya inda Zahra ke basu labarin wata mai ciki data bata tausayi tana nakuda. A sannu Tasleem tana aikin tausa mata k'afafu,Haris yana daga kishingide yana kallonsu cike da sha'awa.

Can kuma Zahra ta hau cije cijen lebbanta,hakan yasa hankalinsu yayi kanta

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 30"

Post a comment