Results

YAR BARIKI book 2 page 32 end

Tasleem itama sharar hawayen takeyi
"Kinga rayuwarmu yanda ta juye a karshe ko? Yanzu mun taba tsammanin kawunanmu zasu rarrabu haka? Ba shakka Bariki ba hanyace ta huce bacinrai da takaici ba illah k'ara jefa kai ga halaka. Ki yafemin Manal, har zuwa yanzu inajin kaina mai laifi kwarai bisa yanda ba jefa rayuwarki cikin halaka. Na tabbata da ace na baki shawara ta gari,da duk hakan bata kasance ba."

Manal tayi murmushi
"Haba baby,wallahi komai ya wuce. Na dauki komai bisa kaddara,haka Allah Ya kaddaro lallai kuma babu mai chanjashi. Da izninSa kuma zamu cigaba da tsare kanmu da mutuncinmu a ko'ina. Na baya suma munayi musu fatan Allah Ya shiryesu,Ya ganardasu. Kinsan fa mutane suna kuskure daya,idan sunga kana aikata b'arna bazasu iya yin addu'ar shiriya gareka ba saidai suyita aibataka suna masu kyamatarka. Ki godewa Allah da Ya hadaki da Haris har ya zamto fitila mai haskaka rayuwarki."

Tasleem tayi dariya
"Gaba dayanmu zamu hadu muyita godiya ga Allah daya fiddamu daga BARIKI."
Sukayi 'yar dariya,ranar dai kamar kada su rabu. Sai magriba Manal tayimata sallama akan zata koma gidan kanwar Alhaji Ubale inda anan ne tayi masauki sakamakon bikin da za'ayi a danginsa. Sukayi musayar lambobi tare da alkawarin idan tasleem ta haihu zatazo.

Sun jero sai ga motar Haris ta shigo. Dole Manal ta tsaya don su gaisa. Tunda ya doso su yakeyiwa Manal kallon bakuwar fuska don alal hakika ya manceta. Har dai ta gaisheshi bai ganeta ba,saida Tasleem tayi mishi bayani. Ya dan saki fuska har ya tambayi maigidanta,akarshe yayi mata alheri tayi gaba. Tana tafiya,tasleem ta turo baki tayi ciki aguje. Da sauri ya rikota adaidai kofar dakinta ya zaro ido
"Baki lura da cikin dake jikinki ne? Wane irin gudu kike haka?"
Ta ture shi kadan

"Kaima kasan laifinka ai,haka kawai ka hanani zuwa bikin kannena."
Ya ja hancinta
"Ba gashi sanadin hakan kinyi babbar bakuwa ba?"

Tayi murmushi tana mai sanya kanta saman kirjinsa
"Kuma fa hakane my king,naji dadin ganin Manal cikin shigar mutunci,kuma da aure."
Ya jata zuwa sama
"Hakane maman yasmin,mu k'ara godewa Allah."
Sukayi samansa.
****
Bayan Watanni Bakwai

Zaune yake a falonsa ya dora baby yasmin saman cinyarsa yana mata wasa tana dariya,kamshin turarenta ya soma shiga hancinsa kafin ita da kanta ta karasa shigowa falon. Sanye da wata doguwar rigar bacci wacce ko cinyoyinta bai gama rufuwa ba,hakanan saman wuyanta rabi a waje suke kai kace ba'a bawa baby yasmin komai ba. Ya dubeta ta gefen ido kafin ya tsaida idanunsa ga takalmi mai tsinin data sanyo. Murmushi yayi baice uffan ba,saima ya cigaba da yiwa baby wasa. Kwas kwas ta shiga takunta har ta karaso ta zauna kusa da baby.

"Karyani zakiyi?"
Tayi murmushi cike da marairaita murya tace
"Shine ko ka yaba kwalliyata my king,nidai ina kishi da wannan 'yar."
Ta dangware kanta kadan,ya matse hannunta

"Akanta fa zan iya zaneki fa. Maza tashi."
Tak'i koda motsi,karshe ma ta zubamishi ido tana murmushi wutar so da kaunarsa na k'ara ruruwa cikin ransa.
Ya daga mata gira duk da shi d'inma ya gama harbuwa don babu ranar da sonta bai kara samun matsuguni a zuciyarsa
"Hey,karki ciny eni fa."

Tayi wal da idanuwa,tunano abunda ya faru a washegarin daren farkonsu inda yake sha mata kamshi. Murmushi tayi
"Kada dai ka manta ka shagala gobe akwai daurin auren abbanmu da anti sa'a(yar uwace ga waziri,kuma budurwa saidai karatun data tsaya kammalawa yasa batayi auren wuri ba,ashe rabon Abbanmu ce..lol)
Kafin kuna ta mike tana tukunta na manya ta shige daki. Ta yaya zai jure ne? Ya sab'i baby yasmin a kafada ya kashe fitilu ya mara mata baya.

Tammat bi hamdulillah...! Taku har kullum RUFAIDA OMAR…..Ga duk mai gyara kofa a bude take,hakanan tambaya. Dan adam ajizi ne,babu wanda baya kuskure...A gafarcemu… omarrufaida@gmail.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 32 end"

Post a comment