Results

BASARAKE 2


BASARAKE
Koda ficewar su barsus sai waziri Sha,aran ya dubi akwatun da jaruma sulaiza ke ciki gami da KWARI DA BAKAnta kawai sai ya sake bushewa da dariyar mugunta akaro na biyu kawai sai ya sanya hannunsa daya da nufin ya bude murfin akwatun kwatsam bazato babu tsammani said ga yaga wani zabgegen saurayi ya bayyana agabanta tsulum! Tamkar an jefosa daga sama jarumin yana sanye cikin bakaken tufafi tun daga kasa

har sama ya rufe fuskarsa da bakin yanki idanuwansa kadai ake gani a gadon bayansa yana rataye dawata sharbebiyar takobi mai kaifin gaske sa,adda waziri Sha,aran yayi arba da jarumin sai yayi wuf ya mike tsaye ya zare wata takobi adamtsen cinyarsa sannan ya dako wawan tsalle ya asama ya kaiwa saurayin wani wawan sara akafada cikin matukar zafin nama saurayin ya kare harin da takobinsa wani irin

tartsatsin wuta ya tashi sannan suka ruguntsume da azababban yaki mai matukar muni ban tsoro,ban al,ajabi da tashin hankali suna kaiwa juna miyagun hare-hare cikin JURIYA DA BAJINTA tagaban kwatance daga inda dakaru da kuyangin gidan ke tsaye suna iya hangen bakin artabun da akeyi da bokon jarumin sakamakon hasken fitulun acen dasuka haskake ko ina agidan wohoho! Tab as masu iya magana sunyi

gaskiya da suka ce kyan fada akwana anayi kuma idan kaga ki gudu to say gudu ne baizoba said gashi waziri da bakon jaruman sun shafe sa,a days suna fafatawa dayansu bai samu nasarar lakutar jikin abokin fadansa ba da takobi duk wannan artabu da akeyi har yanzu jaruma sulaiza ta kwance acikin wanan akwatu tana sharar barci bata San me yake faruwa sakamakon hodar banjun da barde barsus ya busa mata ba.
Daga mai debe muku kewa ako ya u she
MANSUR USMAN SUFI
08137237071

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "BASARAKE 2 "

Post a comment