Results

CIKIN WAYE page 51 to 60


🤰CIKIN WAYE?🤰


   ❤❤❤❤
         ❤❤
            ❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)
____________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


Bismillahir rahmanir rahim🅿5⃣1⃣-5⃣2⃣


Yana nuna Naanah da hannu,"ke...!ka...Haj...!ya...!,muryarsa rawa take da kyar ya iya cewa"Hajiya duba kiga ikon Allah wannan ba Firdausi bace,gaba d'aya mutanan farlour kallo ya koma gun Naanh,

K'arasowa tayi ta zauna kusa da Abba tana cewa"Abba munyi bak'i ne,gyad'a kai yayi alamar eh don ya shiga rud'u,Mamee tace"babu tantama wannan Firdausi ce,da sauri Didiy ya koma kusa da ita ya rungume hawaye na zubar masa,itama sai takama kukan,kafin tace"wai Abba meke faruwa ne?,

Da sauri Zainab tayi gida ta kira Hajiya da yah Marwan,Daidai shugowarsu Didiy yace"'Yata Firdausi ta 6ace shekaru goma sha shidda da suka wuce kuma ina kallon wannan 'yar na tabbatar 'yata ce,ya d'aga hannunsa sama👏"Allah na gode maka da kadawomin da farin cikina,Mamee da Fareeda tuni suka fara kukan farin ciki suka rungume Naanah,

Abba yace"Allahu Akbar Allah me girma da d'auka ikon Allah yana da dama yanzu daman Alhaji Mukhtar Naanah 'yarka ce,Alh Salis tuni ya fara godewa Allahu yana cewa"Ikon Allah kenan daman Firdausi tana kusa damu Allahu akbar,Momy kuwa itama tuni ta koma gurin Naanah duka suka ruk'umk'umeta,

Abba yace"amma Alh Mukhtar ya'akayi Firdausi ta 6ace daga gidanka,hawaye suka zubo masa wanda daga gani na tsantsar farin ciki ne yace"bak'ar rana agareni wacce bazata ta6a 6acemin ba wato ranar da Firdausi ta 6ace"Munje Igabi bikin yaron babban yayan mu domin asalinmu 'yan Igabi ne bayan angama biki da komai don satinmu guda acen nida iyalina,muna hanyarmu ta dawowa Fahat yayan Firdaisi ya ishemu fitsari yakeji,banza muka masa bayan maganata da farko da na masa cewa yayi hakuri saimun kai gida amma yaron nan ya dunga kuka bamu kulasaba, ganin da gaske yake kuka yake sosai yana cewa"Didiy don Allah mu tsaya nayi wallahi ya matseni,ganin yaro na niyyar suk'ewa dole nasa direba ya tsaya,Fahat ya sauka yayi fitsari lokacinmma har mun shugo cikin Kaduna,

Muna Tudun wada,bayan yayi Mameensa ta masa tsarki suka shugo direbanmu yajamu zuwa gida,ashe rabon ayi tsautsayi ne ya tsayar damu,domin muna zuwa gida aka nemi Firdausi sama ko k'asa aka rasa,nan fa hankalinmu yayi mugun tashi,waya muka farayi Igabi ko mun barota cenne akace'a'a,nan take muka koma gurin da Fahat yayi fitsari amma babu ita babu alamun ma me kama da ita,

Sosai hankalina yatashi nan take na bada sanarwa gidajen Radio da Tv,kai abu fa yayi nisa kwana d'aya biyu uku babu Firdausi hankalin mu yatashi sosai gaba d'ayanmu duka Family domin Firdausi kowa a Family na k'aunarta domin yarinya ce mai saurin shiga rai nashaku sosai da Firdausi ko a cikin yarana ita tadabance Allah ya sani ina k'aunar Firdausi sosai haka Mameenta da sauran 'yan uwanta,mun shiga tashin hankali sosai na rashinta sanadiyyar hakan na kamu da ciwon zuciya ga hawan jini saboda ya waita tunanin da nake,har zuwa wannan lokacin bamu sake ganin me kala da itaba saiyau,

Gaba d'aya gurin akasa ka kabbara "ALLAHU AKBAR,Abba yace"ni kuwa wata rana mun dawo sallar la'asar ni da Ameen lokacin bai dad'e da kammala secondry ba yana k'ok'arin shiga jami'ar Ahmadu Ballo dake Zaria,shine ya fara ganin yarinya,yace"lah Abba jibi wata yarinya cen sai kuka take,waigowa nayi mukayi ido hud'u da ita nace"kai Aminu ka cika jajibe jajabe ina ruwanka da ita haka kawai daga ganin yarinya kasani ma ko aljanace,jibeta fa,saboda shigar dake jikinta ta wata 'yar kanti me tsada gashi kanta tasha kitson kala me kyau yarinya kyakkyawa,

Haka muka wuce Aminu sai waigen ta yake najasa muka shiga gida,

Bayan mun fito sallar magrib har zuwa lokacin yarinyar na nan,yace"Abba har yanzu yarinyar cen bata tafiba,harararsa nayi najasa muka wuce,har muka dawo isha'i ta nanan da yake idan mukaje sai mumyi isha'i muke dawowa,

Nan Ameen harda kuka yace"kai Abba yarinyar nan daga gani takasa gane gida ne don Allah mu dauketa mutemaka mata Abba,nace"Ameen kayi shuru yarinyarcen da kake gani k'ilama aljanace ni ban yarda da ita ba,

Haka muka wuce gida,ranar Ameen baiyi barci ba da tunanin yarinyar ya kwana,koda asuba da naje tadasa muje masallaci zaune na iskesa yana kuka"lafiyarka Ameen,na tambayesa,yace"Abba yarinyar nan da ita na kwana araina,naja tsaki"kai kasani wuce muje masallaci,

Haka yabini,mukaje damuka dawo muka iske yarinyarnan kwance a gurin tana kuka sosai,ashe da zamu duhune yasa bamu ganta ba,ai da gudu Ameen yayi kanta ya d'auketa "yi hakuri princess.....


Kuyi hakuri da wannan wallahi kwana biyun nan ina busy ne amma karku damu😉

Fateenku ce😂👇

           Ummu Affan✍🏽✍🏽✍🏽
🤰CIKIN WAYE?🤰


   ❤❤❤❤
         ❤❤
            ❤

Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)
____________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


Bidmillahir rahmanir rahim🅿5⃣3⃣-5⃣4⃣


"Yi hak'uri princess,nan ya fara jijjigata alamar tayi shuru,kallona yayi idanuwansa cike da hawaye"please Abba don Allah mu temaki yarinyar nan,numfashi naja nace"tom shikenan,muka nufi gida da yarinyar wacce ta kwanta kafad'ar Ameen zuwa lokacin tayi shuru,

Da sallama muka shiga,Umma wacce ke kitchin tana had'a abin kari ta fito,shak'ek'e tabi Ameen da kallo kafin tace"meye haka me zan gani haka,Ameen ya aje yarinyar gaban Umma yace"Wallahi Umma abin tausayi haka muka tsinci yarinyar nan sai kuka take,harara ta banka masa"kai dai Ameenu kaciga jajibe-jajiben tsiya daga ganin yarinya kuma saiku d'auka me ruwanku da ita wayasani ma ko aljana ce,

Ganin fad'an da Umma keyi tasa yarinyar run gume Ameen tana cewa "nidai bansonta Yaya kakaini gida,cike da mamaki suka kalli yarinyar jin ta iya magana amma ba sosai ba,

Umma tajawota taja kunnanta nan take tasaki kuka tace"kujimin kinibabbiyar yarinya nice bakiso don ubanki saidai kik'i iyayenki dasuka yarda ke wayasani ma ko shegiya ce,kuka sosai yarinyar take,

Ameen ya amsheta hannun Umma yace"haba Umma yarinyar nan me tasani,rik'e baki tayi"ehye to maza ka kwasheta ka mayar inda ka d'aukota bazan iya ba,Abba yace'yarinyar nan dai tsintarta mukai zataci gaba da zama gidan nan har Allah ya nuna mana 'yan uwanta,

"Wanne gidan Umma ta fad'a cike da karaji,Abba yace "wannan gidan wallahi Karimatu ki fita idona inason ki dauki yarinyar nan tamkar 'yar da kika haifa da cikinki banson ko da wasa tasan ba mune iyayenta ba duk ranaar kuwa da kika sanar da ita bamune iyayenta ba to abakin auranki,

Wata kururuwa Umma tayi tace"ikon Allah yau daga k'arfin hali to wallahi bari kaji na tsani yarinyarnan ban sonta ban kaunarta kuma bazan ta6a sonta ba har abada,

Ameen ya rungume yarinyar yana hawaye yace"Umma don Allah kiyi hakuri kiso yarinyarnan karki cutar da ita,tsaki taja ta wuce kitchin tana masifa,

Kallon yarinyar yayi"meye sunanki?shuru tayi kamar ba itace tayi magana d'azunba,Abba yace"kawai mu dunga kiranta Naanah tunda ko wacce mace Nana ce,Ameen yace"haka ne,

Bayan Umma ta gama abin karyawa,duka suka had'u domin karyawa,Rahma da Sakina suka kalli Naanah cike da mamaki,Sakina tace"Umma wannan wacece,tsaki taja kafin tace"shegiya ce iyayenta suka yar amma Abbanku da Yayanku sun kwaso,Shuru sukayi suna hararar Naanah ba halinsuyi magana don sosai suke tsoran yayansu Ameen bai musu da sauki,

Kowa aka sama abin karyawa banda Naanah Ameen ya zaunar da ita jikinsa ya fara bata nasa,sosai taci saida ta k'oshi sannan yaci ragowar,Umma ta rik'e baki"Ameenu kana son in sa6a maka wallahi akan yarinyarna kuma yanzun nan zata bar gidan nan,

Kallon Umma yayi cikin hawaye"Umma idan har kika matsa sai yarinyar nan tabar gidan nan to saidai ki rasani domin zan dauketa mu tafine,duka suka kallesa yace"Umma inhar kina son farin cikina to ki rik'e Naanah don Allah,

Batason ta rasa Ameen don sosai take kaunarsa hakan yasa tace"naji na amince amma kusani har abada bazan ta6a sontaba hakama yarana bazasu sota ba,

Shi baidamu da wannan ba yasan indai Naanah na gidan dole wata rana tasota,

Dakansa ya shiga kitchin yasa ruwan zafi yawa Naanah wanka,hardasu shafa sudai iyayensa na kallonsa,da rana ya amshi kud'i gurin Abba yasayowa Naanah kayan gwanjo don ta dunga cenji,idan an mata wanka,

Sosai Ameen ke kula da Naanah wacce suka saba sosai shine wankanta shine bata abinci a baki saita k'oshi yakeci,komai shike mata wanka wanki wanke bayan gida idan tayi yakaita kitso da kunshi domin Umma ta rantse bazata mata komai ba,

Sosai suka saba,da yasami kud'i nan take zai k'arar dasu akan Naanah saya mata kaya takalma da kayan kwad'ayi su sweet choculate da dai sauransu,Umma na matuk'ar jin haushin wannan abu tayi masifar da bala'in amma abanza,

Suna zaune a barandar gidan suna shan iska Ameen na tsefewa Naanah kitso yace"kan nan naki ya tsufa Naanah kusan sati biyu dayinsa ni inason ki dunga yawan kitso kar gashinki ya lalace,cikin shagwa6a tace"kai yah Ameen nifa banson kitso babu abinda kaina yayi sai ka tsefemin,dariya yayi"ke kuwa kinga yadda kanki ya tsufa,tace"uhmm uhmm kaidai kawai kafison me kitson nan ta matseni ina kuka tamin,

Yace"kai!kai!!badai matsemin princess take ba,dariya ta tuntsere tace"matseni take ni kuma na cijeta,rik'e baki yayi yana murmushi"haba dai princess kidena cizo idan ba haka ba zan dena sayamiki choculate tace"sorry Yayanah na dena,

Haka dai Naanah take rayuwa a gidan bata samun kulawar Umma da yaranta Rahma da Sakina tsakaninsu sai hantara da tsawa,lokacin da yah Ameen ya tafi Zaria karatu a lokacin Naanah ta shiga kuncin rayuwa sosai ake takura mata ni kad'ai take samun sauki ta gurina,sai ko idan yazo hutu ko wani abun ya kawosa,

Naanah nada shekaru biyar Ameen yasa makarantar boko da islamiyya ta masu kud'i,haka yake buga-bugarsa ya sami kud'in karatunsa dana Naanah sai temakon da yake samu agurina abun dai bayawa saboda ba hali gareni ba,

Da haka ya samu yayi digirinsa,cikin ikon Allah kuma bai dad'e da gamawa ba Allah ya had'asa da Alh Salis Sada kuma yad'aukesa aiki,cikin lokaci k'ank'ani da fara aikin Ameen rayuwar gidan nan ta sauya,saboda ruk'on amanarsa har ka k'ara masa muk'ami mai girma a campanyn ka hakan yasa muma rayuwarmu cenzawa yasake gyara gidan nan dakomaima namu yadawo kansa hatta kasuwa ya hanani zuwa,

Yaci gaba da basu labarin duk abinda yacigaba da faruwa da Naanah da rayuwar gidan har zuwa wannan lokacin da aka had'u,

Gaba d'aya gurin akasaka kabbar"ALLAHU AKBAR,Naanah kuwa kuka take kamarme yayin da Umma ta zamto tamkar munafuka takasa d'aga ido balle ta kalli mutanan dake gurin,Zainab tace"Naanah ba kuka zakiyi ba ki godewa Allah da ya had'aki da ahlinki,

Hajiyarsu Zainab tace"ina tayaki farin ciki Naanah yau ranar farin cikice a gareki,kowa ya rik'e Naanah musamman iyayenta da Fareeda sun tausayawa rayuwar da tayi,Didiy yace"wannan Cikin da ba asan ko CIKIN WAYE?ba shine kaddararki Naanah Firdausi yana cikin rubutacciyar kaddararki shiyasa hakan ta faru min yarda da kaddara fatanmu Allah ya rabaki da cikin Nan lafiya,gaba d'aya aka amsa da Amin

Yah Ameen da Marwan lokaci guda suka had'a baki cewa sukayi"ina da magana🗣,hankalin kowa ya dawo kansu yayinda Ameen ya kalli Marwan shima Marwan ya kalli Ameen jin maganarsu ta fito iri d'aya.......


WhatsAPP No 08104335144TOFAH😯ni kuwa Fateemah me zasu fad'a?🤪

Fateenku ce😂👇            Ummu Affan✍🏽✍🏽✍🏽
*🤰CIKIN WAYE?🤰*


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


*Story and written by*
 *Fateemah Sunusi Rabee'u*
*(Ummu Affan)*

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


_*Gaskiya masoya littafin nan inayinku over wannan page d'in sadaukarwa ne ga duk wani maison CIKIN WAYE?Ina godiya sosai🙏*_

_*Special gift to Anty Hauwa*_


Bismillahir rahmanir rahim


🅿5⃣5⃣-5⃣6⃣

Abba yace"tom muna sauraronku,jin dukansu sunyi shuru yasa ya fad'i hakan,

Ameen tashi yayi ya duk'a gaban iyayensa tare da rik'e hannayen Naanah,nan take hawaye suka zubo idanuwansa yace"ku yafeni Abba Naanah kiyi hakuri ki ya feni wallahi ba laifina bane kaddara ce cikin jikinki CIKINA NE!,

Ai gaba d'aya gurin aka d'au salati,sosai Naanah take kuka cikin kuka mai tsanani tace"yah Ameen ka fad'i gaskiya kar kamana sharri wallahi tunda nake banta6a aikata zina ba kaima nasan baza kayi hakaba meyasa zaka d'aura mana abinda bamuyi ba,

Shima cikin kukan yace"wallahi Naanah cikin jikinki nawane,nayarda da maganarki ke bakisan komai ba nima banta6a aikata zina ba tsautsayi ne da k'addara ki yafemin a shirye nake da auranki da zarar kin hauhu,

Abba saboda tsabar takaici ya kasama magana,Ameen yaci gaba dacewa"ana sauran kwana biyu zanyi tafiya nazo gidan nan da niyyar yiwa su Abba sallama na iske su Umma suna tashiri zasu gidan suna kanwarta ta hauhu,

Bayan mun gaisa nake sanar da ita"Umma zanyi tafiya k'asar England akan harkar kasuwancin Daddy ya wakiltani kan komai,tace"tom Allah ya bada sa'a muma gidan Sahura zamu yau suna ta haihu ne,yace"Allah yaraya,ta amsa da amin,

Bayan sun gama shiri nace"suzo na saukesu,daga nan inbiya gurin Abba kasuwa muyi sallama duk da na hana Abba zuwa kasuwa amma yakanje suyi hira da abokanansa don yace zama guri d'aya lalura ne,

Bayan sun fito nace"Umma ina Naanah ne nasha dukanku zakuje,danaga ga Rahma ga Sakina,harara ta tayi "to ba inda zani da ita mu kad'ai zamu,Rahma tace"ai shiyasa ma nasa mata maganin barci cikin Freesh milk na bata tasha don karma tace zata bimu tanacen tana barcin asara sainan da awa uku zata farka,

Harararta yayi"ke saboda tsabar mugunta,to inama kika sami maganin,nan ta fara uhmm uhmm,Umma tace"karfa ka takura mata wai ina ruwanka ne idan bazaka kaimu ba babu lalai ba dole sai muhau motar haya,gaba yayi"Allah ya baki hakuri Umma amma gaskiya dole yaran nan a gyara musu zama,tace"kaji dashi kuma,

Bayan ya kaisu yashiga yawa Antyn tasa barka yamata alkhairi sannan ya fita,kasuwa ya wuce yawa Abba sallama nan yayi ta kwarara masa addu'a,yaji dad'i sosai sannan ya wuce,har ya doshi hanyar gidan Daddy sai kuma ya juya ya nufi gidansu don yana son suyi sallama da Naanahrsa,bayan yayi parking ya shiga ciki,d'akinta ya wuce,

Kwance take cikin kayan barci riga ce iyakarta gwiwa me shara-shara gaba d'aya cinyoyinta a waje suke,haka ma girjinta ya fito sosai gashin kanta a barbaje,tunda yake bai ta6a ganin Naanah a haka ba kallonta kawai yake ba ko k'iftawa zuciyarsa na bugawa da k'arfi yayin da jikinsa gaba d'aya yahau rawa,

Da sauri ya juya farlour zaunawa yayi kan kujera tare da dafe k'irjinsa,ba abinda zuciyarsa ke hange sai kyawawon surar Naanah ya runtse ido da k'arfi baison tana masa gizo a cikin irin wannan hali,

Amma ina zuciyarsa na k'ayata masa surorin Naanah tare da shed'an da ya ke k'ara ingizasa,a gigice ya tashi ya koma bedroom d'in Naanah cikin wani mawuyacin hali,gaba d'aya tunaninsa da natsuwarsa suka d'auke a wannan lokacin haka ya haik'e mata😭,

Ita kuwa saboda k'arfin maganin nan da tasha batasan abinda ke faruwa,shima ga bad'aya hankalinsa ya gushe,baimasan duniyar da yake ba,sai da ya gama aika-aikarsa sannan da hankalinsa ya dawo yaga 6arnan da yayi,nan kuma hankalinsa ya tashi salati ya fara,ya akayi hakan ta faru?yake tambayar kansa kuka sosai yayi yanacewa"wallahi Naanah ba hali na bane ke kanki shaidace innalillahi wa'inna ilaihir raju'un wai yau Naanah nawa haka kaichona me yasa zuciya da sharrin shedan kuka kaini ga aikata hakan,

Nan ya dinga bawa Naanah hakuri wacce ma barasan me yakeba,nan ya gyara mata kwanciya duk dai ya gyara gurin,hatta zanin gadon saida ya cire yasa wani kamar wani mahaukaci haka yake abu sauri-sauri saida ya kimtsa komai sannan yabar gidan ko da yakoma gida yana shiga bedroom ya fad'a toilet hawaye kawai yake zubarwa lokacin dazaiyi wankan tsarki,wai yau shine zaiyi wankan tsarki batare da yayi aure ba,yanayi yana kuka yana istigifari,Naanah kawai ke fad'o masa,

(Masu karatu idan baku mantaba a cen baya na fad'a muku lokacin da Naanah ta farka barci kasa tashi tayi har kuka ta dunga idan baku manta ba nace da kyar ta rarrafa tasa ruwa a hita sannan tayi wanka)kuma ta kwana biyu tana cin wani iri jikinta da k'asanta,

Koda yah Ameen yayi tafiya kullum yana cikin tunanin Naanah da halin da ya barta,kuma ko kad'an baiji sonta ya ragu a zuciyarsa ba saima k'aruwa da yayi,

Lokacin da ya dawo akasanar dashi Naanah nada ciki kuma ba'asan ko CIKIN WAYE?ba,ba k'aramin tashin hankali yashiga ba,dalilin kwanciyarsa asibiti kenan don yana tunanin ta wanne hali zai sanar da iyayensa da Naanah cewa CIKINSA NE!,

Yaci gaba dacewa kullum ina cikin wannan damuwar domin ni nasan Naanah bada saninta na aikata hakanba sannan a shirye nake da auran Naanah da zarar ta haihu kuma......bai k'arasa ba sakamakon kyakkyawan marin da Abba ya masa kafin ya d'ago yasake zuba masa wani,

Shi kansa Abban hawaye yake yace"Ameenu kai ka aikatawa yarinyarnan haka innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Ameenu kanka kacuta kuma inaso kasani daga yau bani baka kum.....bai k'arasa ba yayi shuru saka makon k'arar da Naanah tasaka,

"Wayyo cikina bayana marata wayyo mutuwa zanyi,tasaki k'ara sai kuma ta zube a gurin gaba d'aya akayi kanta,Umma ce farkon isa,

Ameen ya rungumeta yace cikin kuka"Naanah kece rayuwata don Allah ki tashi karki barni ba laifina bane k'addara ce kuma duk mairai bai haurewa k'addararsa kiyi hakuri ki yafemin don Allah Naanahta ki tashi........
WhatsAPP no     08104335144Tofah muje zuwa😉
Karkumance
Fateenku ce😂👇


          Ummu Affan✍🏽✍🏽✍🏽
🤰CIKIN WAYE?🤰


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


Story and written by
 Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


*Am Sorry my fans for my absence some tin came of but am back,Karku damu ana tare ina ji daku my fans,Musamman wad'anda suka biyoni PC da wad'an da suka kirani nagode🙏*

*Didicate to Hussaini 80k*

*Special gift to Anty Hauwa,ina yinki over Antynmu maganin kukanmu,Allah ya k'ara d'aukaka ki🙏*

*Gaisuwa gareku d'aukacin members na kungiyarmu me tarin Albarka Arewa writers,'yar gatan arewa na gaishe ku😂*
Bismillahir rahmanir rahim


🅿5⃣7⃣-5⃣8⃣

Hankalin kowa yatashi a gurin ganin Naanah ko numfashi batayi,nan fa Ameen ya kinkimeta sai mota akayi asibiti da ita,

Gaskiya sun shiga cikin wani hali musamman Ameen duk yayi wani iri haka Abba da iyayen Naanah,da kawa ta gari Zainab haka su Hajiya da Marwan,

Jini kawai Naanah ke zubdawa ta wahala sosai tunda ta farfad'o sai kuma wani irin nishi tun tanayi da k'arfi har ta galabaita sosai,domin sunce nak'uda take,hankalin kowa fa ya tashi,

Ameen kuka yake kamar wani k'aramin yaro,shi kansa ka kallesa abin tausayi ne,likita yace dole sai an k'arawa Naanah jini leda uku,Na Ameen aka dauka domin jininsa mai k'arfine zai iya bawa kowa jini,leda biyu aka dauka,

Didiy ya kira Sayyeed a waya yace"kana ina,jin yanayin muryar Didiy nasa yace"Didiy lafiya,yace"lfy kalau kana inanace,"ina hanya zan koma gida daga makaranta,

Yace"to kazo asibiti yanzun nan,ya fad'a masa sunan asibitin,"me yafaru Didiy,ya fada a rikice don yanayin da yaji muryar Didiy kuma yace yazo asibiti,baibasa amsa ba ya kashe wayar,

A rikice Sayyeed yayo kwana,yana zuwa ya gansu a Reception,yanayin da ya gansu yasa shi kasa fassara waye ba lafiya tun da yaga iyayensa yaga 'yan uwansa,Didiy yace"suje a d'ibi jininsa domin jininsu d'aya yake dana Naanah bayan an gwada aka d'iba shidai binsu yake da kallo cike da rud'u don yakasa gane meke faruwa,kuma ba fuska bare yayi tambaya,

Kwanan Naanah biyu a asibitin amma duk mai imani ya ganta saiya tausaya mata abin tausayi duk ta fita haiyacinta abin ba sauk'i,

Ganin tana tashan wahala likitoci sukace gaskiya saidai a mata aiki,a cire abinda ke cikin,haka Didiy yasa hannu cike da tashin hankali aransa yana addu'ar Allah ya sa ayi lafiya,

Cikin ikon Allah da yardarsa har angama shiri za'a tafi da Naanah d'akin Tiyata sai tayi wani nishi mai k'arfi nan take sim6ulelan kyakkyawan yaro sak Ameen ya fad'o kamar yayi kaki ya tofar,Allahu akbar Allah kenan waye zaiyi hakan bayansa,

Bayan an gama gyara yaron Ameen ya amshesa ya k'amk'ame yana kuka sosai daman yana Labour room d'in kusan tare akayi amsar haihuwar dashi,fitowa yayi da yaron yana hawaye,Abba ne ya kar6esa yana hararar Ameen shidai k'asa yayi da kansa sannan ya koma d'akon haihuwar inda ake gyara Naanah,har fad'a akayi da Ameen akan shiga d'akin haihu da yake dole suka rabudashi don yace basu isa sumasa iyaka da Naanahrsa ba,

Kallon yaron kawai suke wanda baida maraba da Ameen,addu'a aka masa sosai inda Abba ya masa huduba da sunan Didiy wato Taheer


08104335144

Amin afuwa da wannan idan na sami lokaci anjima zakujini😂

Fateenku ce👇


Ummu Affan✍🏽✍🏽✍🏽
*🤰CIKIN WAYE?🤰*


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


*Story and written by*
 *Fateemah Sunusi Rabee'u*
*(Ummu Affan)*

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim


🅿5⃣9⃣-6⃣0⃣


Bayan an gama gyara Naanah aka dawo da ita d'akin hutu Alhamdulillah jikin da sauk'i domin cikin ikon Allah tana haihuwa sai ta dawo nomal saidai abinda ba'a rasa ba,

Domin tak'i kallon kowa tunda suka shugo kanta ak'asa yake ta kasa had'a ido da kowa,

Jinta take ta to zarta wai itace da d'a kuma wanda aka haifa batare da aure ba,to CIKIN WAYE?,

Wata k'ara ta saka da ta tuno abinda yah Ameen yace"CIKIN dake jikin Naanah CIKINA NE,

Tak'ara sakin k'ara tare da fashewa da kuka,gaba d'aya sukayo kanta,Abba yace"Naanah lafiya me ya faru,Cikin kuka tace"Abba kace ya fita banasan ganinsa Abba ya fita,

Tun kafin Abba yayi magana Ameen ya fice da sauri,ta kwanta jikin Abba tana kuka yace"Naanah kiyi hak'uri Ameen kansa ya cuta kuma zaiga sakaryar abinda ya miki ai abinda kashuka shi kake girba,

K'amk'ame idona nayi ko photon fuskar yah Ameen banso na hango,

Likitoci sun bamu sallama ganin babu wani abu dake damuna,kai tsaye gidan Daddy aka wuce dani,A bedroom d'in Momy aka saukeni,har zuwa lokacin banga abinda na haifa ba kuma bama nason na ganin,

Zuwa lokacin tuni Sayyeed yasan abinda ke faruwa haka 'yan uwa duk sunji labari na kusa sai zuwa ganin Naanah suke sunawa juna barka da arzikin ganinta da akayi yayin da na nesa akayi ta waya dasu suma sunce suna hanya zuwa gobe,

Nan Momy ta yimin wanka mai rai da lafiya,ta gyarani fess sannan ta kawomin lafiyayyen tuwan semo da miyar ku6ewa d'anya dataji bushasshen kifi sai kular ferfeson kan rago me romo da yaji tarugu sosai,

Haka na zauna naci sosai na k'oshi,sannan na kwanta kenan saiga Momy ta shugo hannunta da jariri,mik'omin shi tayi tana cewa "amsarsa Naanah yasha yaron ma yana da hakuri wallahi,

Kwanciya nayi tare da zuya mata baya nace"ni Momy bana sonsa don Allah ki fita dashi,sakin baki tayi tana kallona"Naanah meye haka shime yasani don Allah karki d'au hakkinsa,

Kuka tasaki tare da birgima akan gadon tanacewa"ni bana sonsa kuma ba'abinda zan basa,zaunawa Momy tayi bakin bed tare da dafa Naanah cikin sigar rarrashi tace"Naanah wannan yaron da kike gani baisan komai ba karki d'au hakkinsa ba laifinsa bane domin daza atambayesa wallahi zaifi kowa bak'in cikin me yasa yazo ta wannan hanyar amma kaddara ta riga fata,kiyi hakuri wata rana sai labari ki ringumi d'anki daman Allah ya rubuta hakan sai yafaru dake shiyasa kika 6ace har suka tsinceki suka raineki daga baya hakan ta faru meyasa bazakiyi tawakkali ba,

Jikin Naanah yayi sanyi amma ita har ga Allah bata k'aunar yaron nan dashi da ubansa,Momy ta mik'o mata shi,ta amshesa,bayan fitar Momy ta k'ura masa ido yayi kama sosai da yah Ameen,

"Ba tare da aure ba fa kika haifesa Naanah,zuciyarta ce ta fad'a mata hakan da sauri ta sakesa kan gano ta fashe da kuka,shima yaron ya tsandara kuka don yadda ta sakesa abin ba kyau,

Da gudu Momy ta shugo kallon Naanah tayi ta kalli yaron da gudu ta d'agosa,cikin fushi tace"Naana baki da hankali ko?to meye hakan kike?ko kin isa ki cenza ma kanki rayuwa ne haka Allah ya kaddaro miki me zaisa bazaki rungumi k'addararki da hannu biyu ba,haba Naanah wannan wanne irin rashin hankali ne,

Cikin kuka tace"Momy ki yafeni karkiyi fushi dani narasa gane ya zanyi ne amma ina rok'onki👏don Allah ku shayar da yaron nan da madara bazan iya basa Nono na ba please Momy👏,

Kallonta Momy tayi cike da takaici kafin tace"Naanah meke damunki ne amma bari na kira iyayenki tunda ni ban isa dake ba,zata fita na ruk'ota "kiyi hak'uri bazan sake ba,

Mikomin yaron tayi "to kar6i ki basa ina gani,amsarsa nayi tare da rintse idona ta fara basa,

Ai wani zafi da naji yasa na cire masa da sauri nace"wayyo Momy da zafi,kiyi hak'uri da sannu zaki saba,batabar d'akinba saida ta tabbatar yaron yanasha sannan tafita,

'Yan Igabi san iso washe gari yayun Didiy da matansu da yaransu nan gidan Daddy suka sauka haka akayi ta murnar gani na,lokaci guda muka saba da Salma d'iyar Baba Auwalu da kuma Hafsat d'iyar Baba Sani,domin mu sa'anni ne,muka hadu da Zainab akayi ta hirar zuminci,

Yau kwana shida da haihuwata,kullum sai Momy ta tsareni nikebawa yaron nono,tun tanamin fad'a yanzun ta dawo rarrashi,

Zaune muke,inajinsu yadda suke tashirin abinda za'ayi gobe suna,abin yabani mamaki araina,ganin shege kuma harda wani suna za'ayi,nidai na zama yar kallo,

Sayyeed yace"amma fa Naanah ya kamata musawa yaronmu wani sunan daban tunda sunan Didiy yaci,ta6e baki nayi bance komaiba,Zainab tace"rabu da ita kawai aini tuni nawa d'ana suna,yace"yauwa my zeey me kikasa masa,tace"Muhsin nasan Naanah tanason wannan sunan,Salma tace"wow gaskiya sunan yayi dad'i Muhseen,Hafsat tace"daga yau sunan yaronmu Muhseen,

Da gudu Fahat ya fita yana fad'awa mutane da Muhseen za a dunga kiran yaron,

Washe gari Mutane sosai aka taru a masallaci wajen rad'in suna sosai Daddy da Didiy sukayi gayyata don masallacin ya cika sosai,

Ameen da Marwan duk sunzo Abba yana kusa da Didiy,bayan gama rad'in sunan sai kuma sukaji wata maganar da ban,

👂👂👂kasa kunne nayi don naji kamar aure akeson d'aurawa 👂👂👀nidai banji sosaiba ban ganiba mu had'u page na gaba donji me za'ayi a masallacin bayan rad'in suna da akayi,


Fateenku ce😂👇

        Ummu Affan🖊🖊

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "CIKIN WAYE page 51 to 60"

Post a comment