Results

CIKIN WAYE page 61 to 70

🤰CIKIN WAYE?🤰


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


Story and written by
 Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim


🅿6⃣1⃣-6⃣2⃣


Bayan gama rad'in sunan aka fara d'aura aure,kan kowa ya kwance a gurin mamaki ne fal ran wasu daga cikin jama'ar dake wajen ciki,harda Abba,Ameen,Marwan,

Aure ne aka d'aura tsakanin Al-ameen Isma'il Muhammad,da Naanah Firdausi Taheer Sada,sai Marwan Ibrahim da Salma Auwal Sada sannan Sayyeed Taheer Sada da Zainab Ibrahim,

Gaba d'aya kallon kallo suke musamman Ameen da Marwan,hawayen farin ciki kawai Ameen ke zubdawa Allah yajika masa burinsa yau Naanah ta zama mallakinsa,zuciyarsa ta buga da yatuno ya Naanah zata d'au wannan maganar domin yasan kamar yadda baisan da maganarba yasan itama batasan komai ba,

WAITO YA HAKAN TA FARU nifa duk sun sani a duhu🤔Kufah😂,

Abinda ya faru,bayan zuwan yayun su Didiy,Alh Auwalu wanda shine babbansu sai Alh Sani sannan Daddy k'araminsu ne Didiy,kafin muji ya akayi bari muji tarihin ahlin

Alh Sada Igabi shine sunan mahaifinsu,mahaifiyarsu Maryama wacce akafi sani da Baaba Mero,su dukansu haifaffu Igabi ne k'aramar hukumar Kaduna,tun a wancen zamanin Alh Sada mutum ne mai arziki wanda ya riki sana'arsa ta noma da kiwo yana da son karatun boko tun wancen lokacin hakan yasa ya tsaya tsayin daka yaransa duka saida sukayi karatu,duka su hud'un maza ne basu da mace kuma mahaifinsu Baaba mero ce kawai matarsa,

Auwalu shine kawai ya tsaya iya secondry inda yaci gaba da sana'ar mahaifinsa bayan rasuwarsa,ganin burin mahaifin nasu nasan suyi ilmi mai zurfi yasa ya tsayawa k'annansa saida sukayi karatu sosai boko da islama,daman tuni shi yayi aure yana nan zaune gidansu na gado,

Sani ya fara gamawa inda yasami aikin gwamnati anan Igabi,shi kuwa Salis da yake Business ya karanta sai ya bud'e wani k'aramin kamfani a Kaduna cikin ikon Allah lokaci k'ank'ani Campanynsa yayi suna wajen k'era kayan d'aki da na wuta,hakan yasa ya bunk'asa sosai inda yayi wani babban campanyn sosai yayi arziki,

Shi kuwa Taheer babban lawya ne mezaman kansa,ya shahara sosai wajen aikinsa,Allah ya amshi ran mahaifiyarsu sunyi kukan rashi inda suka d'auki Alh Auwal ya zame musu uwa da uba mutum ne na gari,Alh Auwal da Alh Sani a Igabi suke zama,Inda Salis da Taheer suke Kaduna,daman tuni duk kansu sukai aure matan Alh Auwal uku yanzu,su kuma dukansu d'aid'ai sun tara iyali sosai saidai shi Alh Salis Allah bai basa haihuwa ba,daman kunsan wannan tun abaya,

Tarihinsu kenan,cigaba,daman tun zuwansu Alh Salis ya sanar dasu dukkan abunda ya faru sun tausayawa Naanah Alh Auwal yace"k'addararta kenan mu bazamuja da hukuncin Allah ba tabbas Ameenu bai kyauta ba amma sanin da muka masa na yaron kyirki yasa mun yafe masa saidai tabbas zamu had'a auransu tunda yaron na sonta,Fareeda dake zaune gefe tace"nayarda Baba Ameen nason Naanah sosai bai iya kula ko wwacce mace saboda k'aunar da yake mata,

Nan ta basu dukkan labarin abinda yai ta faruwa a tsakaninsu saboda son da yakewa Naanah,Alh Salis yace"kwarai kuwa nima shaudane don yasha bamu labarin ta,nan suka yanke hukuncin ranar suna za'a d'aura auransu amma karwanda yasanar musu,Daddy yace"ko Abbansa bazamu sanarwa ba saboda yad'au fushi dashi sosai idan yaji bazai yarda ba,kowa ya gamsu da hakan,

Sayyeed yace"wallahi saidai a had'a dani nima k'awarta Zainab nakeso don tayimin,gaba d'aya aka d'au salati Didiy yace"mun shigesu zamani yanzu ya sauya Sayyeed mukake fad'awa aure kakeso,

Alh Salis yace"rabu dashi zamani ne ai gara da yasanar damu da yaje yana aikata wani abun fa?zanga Alh Ibrahim ai abokina ne,Fareeda tace"yanzun ni ina matsayin mace amma har k'anina namiji zai aure yabarni ga kuma autarmu,sai kowa ta basa tausai Baba Alh Sani yace"'yata ki kwantar da hankalinki aure lokaci ne da naki yazo zakiyi,tace"haka ne,

Nan akayi addu'a awashe gari Alh Auwal da Alh Salis suka sami Alh Ibrahim yayi murna don kowa zaiso had'a zuriya da Familynsu Naanah saboda nagartarsu,nan yake sanar dasu ai Marwan ya sanar dashi yanason Naanah,

Hak'uri suka basa cewar ammata miji,Alh Auwal yace"Amma akwai Salma sa'anni suke da Naanah idan yanasonta to,nan take Alh Ibrahim ya amince inda suka tsaida maganar ranar suna xa'a d'aura auran,

To koda yasanar da Hajiya taji dad'i sosai itama tace"karsu sanar da yaran idan an d'aura sai suji,

To kunji yadda abin ya faru,amma ku ya kuke ganin Naanah zata d'auki maganar auran zata yarda da yah Ameen kuma zata amshesa a matsayin miji ko ya?

Marwan kuwa fa shin ya zaiji akan rashin Naanah shin zai amshi Salma yayi auran huce haushi ko ya?

Zainab kuwa fa shin Sayyeed ya ta6ama cewa yana sonta,ga burinta na ganin tayi karatu mai zurfi kuma ga auran Sayyeed ya zataji,

Wai ya batun Umma nifa kwana biyu bana jinta kota gudu ne koya abun yake ne🤣🤪

Uhmmm duk amsoshin nan sai kunci gaba da biyo Ummu Affan muje zuwa Ina alfahari daku musamman fans d'ina na Facebook nagode🙏

Fateenku👇

         Ummu Affan🖊🖊
🤰CIKIN WAYE?🤰


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


Story and written by
 Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim


🅿6⃣3⃣-6⃣4⃣


Bayan andawo daga masallaci wajen d'aurin aure k'ayatacciyar walimar cin abinci a ka gabatar a harabar gidan Daddy,gaba d'aya nan suka kawo bak'insu,

Cikin gida kuwa Fahat ne ya shiga ya tsegunta abinda ya faru,mutane da yawa sunyi mamaki domin basusan da zancen ba,Momy tace"kayi shuru kar Naanah taji zancen nan daman da k'yar ta yarda aka shiryata don haka kowa yayi shuru nasan akwai abinda suka taka da kansu zasu sanar mata,

Hakan yasa kowa yayi shuru,ita kuwa daman Naanah tun safe tana cikin bedroom da k'yar ta yarda aka mata kwalliya tasa kayan da Ameen ya mata akwati guda na suna babynsa ma nasa daban,

Bataso saka kayan Ameen ba amma Momy ta dage dole ta hakura akan yasa tace"bazata fito farlour ba,tunda kowa ya tsaneta komai suce Ameen,

*****************

Kwana yau biyar da sunan Muhseen yaro kyakkyawa,idan Naanah tana kallonsa kuka kawai take,yauma hakan ta kasance zaune take kan bed ta gama karyawa da had'in da Momy ke mata,yaron ya tuntsere da kuka,

Ahankali ta juyo ta kallesa,ganin yadda yake kuka sai kawai itama tasaka kukan ta kasa d'aukarsa hannunta rawa kawai yake,

Sosai ta saki kuka tanacewa "me yasa?meyasa kazo ta wannan hanyar?meyasa baka jiraci zuwanka ba sai lokacin da yadace?meyasa kayi gaggawar zuwa lokacin da bana maraba dakai,

Ameen da yashugo tun farkon jin irin kukan da yaron yake don ko kad'an baison yaji yana kuka,tsayawa yayi yana kallonta dajin kalamanta wani irin so da tausayinta yacika masa zuciya,ya k'araso gurin da take tare da dafa bayanta,

Da sauri ta juyo don ta tsorata tayi tunanin ko Momy ce ganin Ameen yasa tayi saurin ture hannunsa a jikinta tare da wata muguwar harara da ta banka masa,

"yace"duk abinda zakimin Naanah nasan na cencenci haka amma inason kisan wani abu guda ni Ameen mai k'aunarki ne a ko wanne irin hali kika tsinci kanki,sannan kiyi hakuri da abinda ya faru k'addara ce wacce ta riga fata kimin afuwa Naanah nima ba ason raina na aikata miki hakanba,

Hawaye ne ya gangaro akan fuskarta ta kallesa cike da tsana tace "Ameen na tsane ka bana kaunarka kuma bazan ta6a k'aunarka ba ka cuceni ka 6atamin rayuwa Ameen ka cutar da zuciyata kamin abinda bazan ta6a ya fe maka ba,

"Kiyarda da k'addara mana Naanah meyasa kike abu kamar wacce batace islamiyya ba,mik'ewa tayi cike da takaici tace"tunda ka cuceni dole kace haka mana to banjeba kuma bazan yarda da kaddarar ba NA TSANEKA YAH AMEEN banson ganinka please kafitarmin daga d'aki,

Da sauri ya toshe kunnensa kalma kenan mafi muni agaresa,da sauri ya juya ya koma nasa d'akin"NA TSANEKA YAH AMEEN,kalmar dake ta yawo a dodon kunnansa,saiga yawaye yana bin kuncinsa,

A fili ya furta"haba Naanah me yasa bazaki yarda da k'addara ba ni me sonki ne har abada,

Fareeda ta shugo wacce duk taji abinda ya faru,kallon Naanah tayi tace"wallahi Naanah baki da wayau,yanzu miji kamar Ameen ya k'ask'antar da kansa yace yana kaunarki har kidinga ya6a masa irin wadannan mugayen kalaman haba Naanah,

Kuka ya saki tace"me yasa duk abinda nayi sai adunga ganin laifina ku bakwa duba abinda yayimin,Fareeda ta k'araso tare da rungume 'yar uwarta cikin sigar rarrashi tace"tabbas bai kyauta ba amma idan zakiyi tunani ba halinsa bane kaddarace wacce duk kan wani mumini dole yayarda da ita Naanah Ameen me kaunarki ne ki duba irin halin da kika shiga a gidansu amma ki duba jajircewarsa Allah ne ya rubuta hakan zai sameku shiyasa kika 6ata har kika fad'a hannunsa AMEEN yacika dukkan wani abu da za'aso na nagarta,bayan nan kuma shi me kaunarki ne da be kaunarki wallahi don ya miki wannan abun ko kallo baki ishesa ba,kiduba fa Naanah maza da yawa idan sun sami abinda sukeso gurin mace shi kenan sai su rabu da ita ko wanne hali zata shiga babu ruwansu indai sun sami biyan buk'atarsu amma ke jibi yadda ya jajirce akan ke yake kauna kuma babu namijin da zaki aura kisami kwanciyar hankali irin Ameen,

Da sauri ta d'ago ta kalleta tace "me yasa kikace haka Anty Fareeda,murmushi Fareeda tayi tace......


Fateenku ce👇


       Ummu Affan🖊🖊
*🤰CIKIN WAYE?🤰*


        ❤❤❤❤
              ❤❤
                 ❤


*Story and written by FATEEMAH SUNUSI RABEE'U*
*(UMMU AFFAN).*

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

🅿6⃣5⃣-6⃣6⃣

Tace"Saboda shine ya fara saninki a mace,shin kina tunanin zaki auri wani ya sameki ba cikakkiyar budurwa ba har kusami zaman lafiya da kwanciyar hankali,AMEEN shine yadace dake domin bazai ta6a wulak'antaki ba domin yasan shine silar komai kuma bada saninki ya aikata miki hakanba kinga dole ya girmamaki kuyi zamanku lafiya koda ba dan wannan ba d'anku da kuka haifa kurik'e abunku kubashi tarbiyya bazai ta6a tunanin bada aure kuka haifesa ba,

Kuka sosai ya k'wacewa Naanah tace"Anty Fareeda Marwan duk yasan da wannan yasan duk abinda yasameni ni nasan idan na auresa zan sami kwanciyar hankali zai bani duk kulawar da tadace,

Fareeda tace"Naanah ke har yanzun yarinya k'arama ce amma nan gaba zaki fahimci abinda nake nufi nidai inason kimance da komai ki rungumi k'addararki hakan zaisa ki sami kyakkyawan rabo nan duniya da ranar gobe k'iyama,

Tana gama fad'ar haka tayi waje,Naanah ta tura kanta tsakankanin cinyoyinta tana kuka sosai daman Fareeda ta fita tare da Muhseen,

Baku tambayeni ina Umma ba?,

Ai Umma Karimatu tun ranar da abin ya faru taji ko wacece Naanah sai taji duk ta muzanta,haka tayi kai da k'asa sai kace bak'ar munafuka,bayan sun tafi kai Naanah asibiti lokacin da ta fad'i,ita ma ta had'a yanata nata sai gidansu Rahma dama cewa tayi bazata ba,da Sakina tazo ta sanar mata abinda ya faru tabi bayan Umma inda ta sameta duk ta rame ta zama wani iri,saboda daman iyayenta tuni duka suka rasu sai Kawunta agurinsa ma ta girma shiya aurar da ita,to zaman gidan dai ba dad'i Matansa sun sa mata ido ba halin tayi abu yanzun za'a fara mata gori abincima basa bata,nan fa hankalints ya tashi duk kud'in da Ameen yake bata adashi takeyi taje gurin me adashin amsar kud'in suka hau tsiya domin ta cinye kud'i,Umma tayi kuka kamar me tayi da nasanin abinda tawa Naanah yau ga ranar k'in dillaci,duk ta zama wata irin sanyi kamar ba Umma ba,

Ranar da Sakina tazo wankau ta iske Ummar nayi,ta gaishe da matan gidan suka shiga d'an akurkin d'akin da Ummar take wanda shirgine ciki don acikinsa matan gidan ke ajiyarsu ta kayan abinci da duk wasu tsummokaransu,

Cikin hawaye Umma tace"Sakina nayi takaicin abinda na aikatawa Naanah yanzun taya zan fuskanceta ashe daman Ameenu ne ya mata ciki nayi takaici duk wannan abun da nake ashe CIKIN NA D'ANA NE,jikana ne nayi da nasani kaicona ni Karimatu ashe duk dukiyar da mukeci duk ta iyayen Naanah da wanne ido zan kallesu,

Sakina taja numfashi uhmm tace"ai duk irin abinda nake gaya miki ne Umma amma kika k'iji yanzun ga irinta nan amma me yasa kike wankau,tace"dole ne tasa Sakina idan banyiba wa zai ciyar dani abinci ni ke saya,

"Amma me yasa baki sanar damu ba,Umma duk lalacewarki ke uwarmu ce babu yadda zamuyi dake yanzu idan yah Ameen yaji wannan abun zaiji dad'i ne,tace"ya kikeso inyi Sakina dolene fa tasa,tace"to meyaraboki da gida sanake ko lokacin da Abba yasakeki baki bar gidanba har ya mayar dake sai yanzu haka kawai kibar gida,

"Wallahi Sakina kunya nakeji da wanne idon zan kalli Abbanku da yayanku balle iyayen Naanah,Sakina tace"ai duk abinda ya faru ya riga ya faru ki had'a kayanki mukoma yanzu don bazan bari ki kuma kwana a gidan nan ba,

Haka suka koma tare da Sakina,ta kasa koda had'a ido da Abba,sai zubewa da tayi gabansa tana basa hakuri"kayafe ni Malam nasan nayi kuskure amma in Allah ya yarda daga yau zan fara gyara kuskurena,yace"nagode Allah da kika gane kuskuranki amma ke don Allah yanzu ba'abin kunyarki bane da kikaji ko CIKIN WAYE?CIKI nad'anki ne to yanzu wanne irin hukunci kika tanada dazaki tunda kin dad'e kina son jin CIKIN WAYE?Umma ta fashe da kuka tace"nayi nadama nayi da na sani wacce akecewa k'eyace,

Nan dai yafita yabarta tana kuka,Rahma dake taunar chingam ci kake k'as!k'ass!!tace"ke Umma kece da d'aurawa kai shiga uku kika sani ko yah Ameen d'in k'arya yake don ya kareta kinsan fa yarda yake sonta meye bazai mata ba,

"Dolla cen rufemin baki shashasha,Umma ta fad'a cikin tsawa,Rahma ta gallawa Ummar harara tace"a'a ni karki cikamin kunne da tsawarki wallahi banso kika dawo gidan nan ba ke Sakina dad'i uwa kinje kin kwasota,Umma tasaka kuka tace"nashiga uku Rahma nikoke gayawa irin wannan maganar,tsaki Rahmar taja tabar gidan jikinta shigar da ba mutumci,

Sakina tace"Allah na gode maka da ka shiryani tunda wuri kuma ka aurar dani,Umma ga irinta nan bazanga laifin Rahma ba don irin tarbiyyar dakika bamu kiken,ni kinga tafiyata zan koma d'akin mijina idan kin lalla6a Abba kun zauna lafiya ke kika sani idan kuma zakici gaba da abinda kike tom ga fili nan ga mai doki,tana gama fad'a tayi waje abinta,

Umma tasa kuka tana fad'in kaichona yau ga abinda na shuka 'ya'yana na cikina ke gayamin irin wannan maganganun,ya Allah ka shiryu masu irin halina kabamu damar yiwa mazajenmu biyayyar aure kabamu ikon tarbiyyar yaranmu,

Haka ta dunga lalla6a Abba har ta samu ya d'an sakko sosai yanzu take girmamasa da masa biyayya Rahma kuwa sai abinda yaci gaba yanzu ta d'aura k'awance da duniya,

Sakina ta riga Naanah haihuwa ta sami yarta mace Sakinatu,akasha suna,batayi arba'inba Naanah ta haifi Muhseen,tun Naanah na asibiti Umma taso zuwa Abba ya hanata,haka da takoma gida taso zuwa Abba yace ta bari,gashi tanason ganin jikan nata amma da Abba ya hanata saita hakura,shi kuwa yana sake gwada tane yaga da gasken ta gyara ko kuwa,

Ranar sunan da al'ajabi ya dawo gida yake sanar da UMMA abinda ya faru''hawaye suka zubo mata tace"lallai iyayen Naanah sun nuna mana halacci naji dad'in wannan had'in Allah ya basu zaman lafiya,Abba ya amsa da amin domin tabbas yaji dad'i amma duk da haka sai ya nunawa Ameen kuskuransa,

To kunji abinda ya faru da Umma kenan,cigaba,

Babban farlourn bak'i na Alh Salisu Sada cike yake da ahlin wannan gida kowa yazo haka 6angaransu Ameen su Abba da Umma sunzo harda Sakina,haka wajensu Marwan mahaifinsa Alh Ibrahim da Hajiya sai Zainab,tarone da Alh Auwalu yace yana neman kowa don sanar dasu wata muhimmiyar magana,

GYaran muryayi bayan an bud'e taro da addu'a sannan ya fara dacewa".......


Saimun had'u a page na gaba karku manta


Fateenku ce😂👇          Ummu Affan🖊🖊
🤰CIKIN WAYE?🤰


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


Story and written by
 Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


Kwana biyu ba kujini ba amin afuwa,na gode da nuna kulawa,

Didicated to my FansBismillahir rahmanir rahim


🅿6️⃣7️⃣-6️⃣8️⃣


Ya fara dacewa"Alhamdulillahi mun gode da irin ni'imomin da Allah ya mana,yaci gabadacewa,"Mun yanke hukunci ba tare damun shawarce kuma domin munsan komai muka fad'a muku baza ku bamu kunya ba,musammanke Naanah Firdausi da fatan zaki kar6i za6in da muka miki kuma ki rik'e hannu biyu bamuyi hakan da nufin cutarki ba sai gani da mukayi hakan shine mafi daidai agareki,

Tuni gabanta ya buga da k'arfi tun kafin asanar mata meke faruwa ta fara hawaye,tayi k'asa da kai k'irjinta na bugawa da k'arfi,

Alh Salisu yace"ba kuka zakiyi ba Naanah ni nasan zakiyi alfahari da za6inmu anan gaba,ya kalli Ameen yace"kai kuma karkaga mun baka ita kaga kanar wani abu muke nufi cancanta da mukaga kunyi yasa muka yanke wannan hukuncin,yace"Daddy karkayi haufi akaina ni mai kaunar Naanah ne wani naga zaiwa Naanah wani abu sai inda k'arfina ya k'are bare ni da kaina,

Naanah ta d'ago kai ta cilla masa harara domin tuni ta gane inda maganarsu ta dosa so suke su had'a auranta da Ameen to bazata yarda ba,jin abinda Alh Sani kecewa yasa ta d'ago kai cike da tashin hankali,

A wajen rad'in suna aka daura auran Ameen da Naanah,Marwan da Salma,sai Sayyeed da Zainab,ai kusan lokaci guda duk kansu suka d'ago kai,Ameen da Marwan suka zubawa Naanah ido,yayin da Sayyeed da Zainab suke kallon juna cike da mamaki,

Hawaye kwance akan idanuwan Naanah,a hankali tayi k'asa da kanta hawaye na tsiyaya,nan dai akayi musu fad'a sosai sannan taro yatashi,

Da gudu Naanah tashiga bedroom d'in Ameen sakamakon Hankalinta da yatashi ta d'auka nata tashiga saman gadonsa ta fad'a tana kuka,cike da mamaki shugowarta ya shiga,kallonta yayi yanajin tausayin Naanah saboda abinda ya aikata mata amma yanaso ta basa dama domin kankare abinda ya mata,

Zaunawa yayi bakin bed ya d'agota tasha Fareeda ce saita k'amk'amesa tana kuka,fad'i take "ni bana sonsa bazan iya zama tare da shiba,da k'arfi ya runtse idonsa don yaji zafin kalmar bata sonsa,

Naanah jin shurun yayi yawa sai bubbuga mata baya da ake alamar rarrashi yasa tasha jinin jikinta,jin sanyayyen k'amshin turaren yah Ameen da kulum take ji atare dashi yasa ta d'ago kanta dake kan faffad'an k'irjinsa,

Ai da sauri ta fara k'iriniyar kwace jikinta amma ya rik'eta katamau,Wata harara ya banka mata yace cikin muryarsa mai dad'i da sanyi"lokacin da kika rik'eni wa yasaki?sannan me ma yakawoki d'akina alamu ya nuna kinason ki tare gidan mijinki ko?,

Da sauri na sake kallonsa idanuwansu suka sark'e da juna,dukansu kowa najin bugun numfashin kowa,masifar da zata masa sai tanemata ta rasa nan kuma muryarta ta fara rawa"ni...ni...ni dai yah Ameen ka cikani na wuce"ank'i,ya fad'a yana kashe mata ido d'aya😉,

Da sauri tasake k'asa dakai"me yah Ameen d'in nan yake nufi?,ta fad'a aranta ashe maganar ta fito fili yace"komai ma nake nufi,hannunsa yasa saitin la66anta yana zagayawa dasu,cikin sanyi murya yace"Naanah ina sonki da yawa,

Da sauri ta ture hannunsa ta turo baki gaba cikin shagwa6ar da batasan tayi ba tace"nidai banso ka sakeni na wuce,

Shima yayi kamar yadda tayin"ni kuma inaso,

Kallonsa tayi sai kuma ya bata dariya"kai yah Ameen sai kace wani yaro,murmushi yayi cikin jin dad'in dariyar da yaga tayi yace"ai ni nafi yaro yarinta ko Muhseen albarka,gaba d'aya sukasa dariya,

Rik'e hannunta yayi"to muje na rakaki ciki ko?,tace"a'a nagode bari naje,girgiza kai yayi ya zuba mata manyan idanuwansa yace"a'a sai na rakaki,

Zatayi magana saijinta tati sama yah Ameen ya sun gumeta,zaro ido tayi😯"kai yah Ameen,nan ta fara tsalle tsalle ajikinsa tana bugun k'irjinsa"nidai ka saukeni banso,bai kulata ba yayi waje da ita,

Suna fitowa Momy na sakkowa kan bene,ido ta zaro cike da mamaki,yayinda Naanah taji wata muguwar kunya ji take kamar k'asa ta tsake ta shige ciki,sai ta tusa kanta cikin k'irjinsa tana goga fuskarta,ai tuni Ameen yaji wani irin yarr!,amma ganin Momy ya share tare da direta akan kujera,yana sosa k'eya,ai ganin haka momy ta wuce batabi ta kansu ba yana ganin ta wuce da sauri ya zauna kusa da Naanah tare da rik'o hannayenta........


Fateenku ce😂👇           Ummu Affan✍️✍️✍️
*🤰CIKIN WAYE?🤰*


       ❤❤❤❤
             ❤❤
                ❤


*STORY AND WRITING BY FATEEMAH SUNUSI RABEE'U*
*(UMMU AFFAN).*

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim


🅿️6️⃣9️⃣-7️⃣0️⃣

Harara ta banka masa"kaga malam cika ni meye hakan,kallonta yayi da idanuwansa da suka cenza launi"haba Naanah kefa matata ce yanzun,

Mik'ewa tayi ta kallesa wani shek'ek'e tace"a inda ba matar kenan gara tun wuri ka nemi matarka bani ba,tana gama fad'a tayi ciki,dole ne ta gasa yah Ameen domin yasan tana da 'yanci gashi ya bata kunya agaban Momy yanzu me zatace don Allah,

Shi kuwa binta yayi da ido har ta 6ace,rumshe rinannun idanuwansa yayi yanajin wani shauk'i,amma shima yasan dole ya bita a hankali har ta gane shi mai k'aunarta da gaske ne,

Zainab ta Sayyeed kuwa tuni suka fara fahimtar juna saidai tace masa inhar yanaso ta sosa dolene karya buk'aci ta tare gidansa sai lokacin da ta kammala karatunta,ya amince don yana matuk'ar sonta,

Marwan kuwa da Salma tundaga ranar Salma bata sake ganinsa ba,itam ma tana gidan Momy nan aka barta tare da Naanah,ita ko ajikinta don don mancewa ma take da wani Marwan,

Cikin ikon Allah Didiy ya nemarwa Naanah Admission a Kaduna State University KASU,Ta fara karatunta cikin sa'a kuma ta sami fannin da take so,Alhamdulillah karatunta na tafiya yadda ya dace domin Muhseen anan gida take barinsa gurin Momy,yaron tubar kalla bazakace watansa shidda alokacinba sai kace ya shekara yaro kyakkyawa kowa kaunarsa yake,daka ta6asa ya wangale baki yana dariya,

Karatun Naanah na tafiya yadda akeso haka ma Zainab dukda ba makaranta d'aya sukeba amma masha Allahu suna yawan had'uwa domin k'awancensu sai abinda yayi gaba balle yanzun sun d'inke sun ma zama 'yan uwa,

Ta 6angare guda Yah Ameen na damunta da nacinsa,idan zataje makaranta sai yace shi zai kaita,batabin takansa tunda yanzun Didiy ya saya mata mota kuma tuni aka koya mata,dukda dai ba wani iyawa sosai tayi ba😜🤪,

A gajiye yau ta dawo mkrnt,kan kujera ta fad'a tana sauke numfashi saida numfashinta ya daidaita sannan ta mik'e ta bud'e fridg ta d'auko ruwa mai sanyi na gora,

Tuttulawa tayi a cup ta kafa kai saida ta shanye sannan ta aje,bedroom d'inta ta fad'a tashiga toilet wanka tayi tare da d'auro alwara ta zura doguwar riga sannan tagabatar da sallar la'asar,

Mai kawai ta shafa ta fito kitchin ta shiga tasa abinci makroni da miyar kwai,ta d'auko gorar ruwan da tarage da cup,kan carpet ta zauna ta don zatafijin dad'i ta fara cin abincin,

Sallamar yah Ameen taji bata dagi kaiba har ya k'araso,dire Muhseen yayi dake hannunsa hango Naanah da yayi ya fara zillo,

D'ago kai tayi a hankali ta kallesu,d'aure fuska tayi ganin kallon da yah Ameen ke mata"lafiya?ta tambayesa cikin izgilanci,d'an murmushi yayi yace"lafiya kalau my haert❤️

Harara ta banka masa tare da sadda kai k'asa taci gaba dacin abincinta,sakkowa yayi shima yazauna kusa da ita yace"abin ko tayi babu,d'agowa tayi fuskarsu ta had'u da ta juna,ta sake tamke fuska"meye haka,rausayar da kai yayi"a baki nakeso ki bani,

Tashi daga gurin tayi niyyaryi ya funcikota,saigata ta zube a jikinsa,zaro ido tayi ganin ya gad'e bakinta da nashi,wani irin zazzafan kissing yake aika mata yayin da take k'ok'arin turesa ta kasa,

Kukan da Muhseen ya tun tsira yasa ya saketa da sauri,ita kuwa harda hawayenta tace"ban tafeba,niyyar kamota yayi ta ruga a guje,da sauri ya d'auki Muhseen ya kaiwa Momy shi,

Tace"sanake naji uwarsa ta dawo ka kaimata shi nono ya keso,sosa k'eya yayi Momy ki basa madararsa naga kamar ta rufe k'ofar k'ilan tayi barci,girgixa kai kawai Momy tayi aranta tace"Allah dai yashiryaku 'ya'yan zamani kenan kallo suke sunfi kowa wayau,

Yau gidan Abba Naanah ta shirya zuwa don ta gaji da abinda yah Ameen ke mata tayiwa Momy sallama ta wuce bayan ta sa6a Muhseen kafad'a ta d'au karamin akwatinta da kayansu kala biyu ke ciki,

Saman kujerar gaba ta ajiye Muhseen sannan ta zagaya tashiga ta tada,motar dabar gidan......Sai mun had'e da yamma insha Allah😂


Fateenku ce👇


            Ummu Affan✍️✍️✍️

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "CIKIN WAYE page 61 to 70"

Post a comment