Results

CIKIN WAYE page 71 to 80

*🤰CIKIN WAYE?🤰*


       ❤❤❤❤
             ❤❤
                ❤


*STORY AND WRITING BY FATEEMAH SUNUSI RABEE'U*
*(UMMU AFFAN).*

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

🅿️7️⃣1️⃣-8️⃣0️⃣


A hankali take tuk'inta har takai badarawa,bayan tayi parking ta fito,gani tayi gidan ya sauya mata kamar bashiba,tunani ta fara aranta 'anya kuwa gidan ne,gidan da bashi da gate yanzu kuwa naga an fad'ad'ashi,harda wani gida dake kusa da gidan Abba naga bashi da alama an had 'esu ne,

Ina tsaye ina wasiwasi don ina tunanin ko su Abba sun tashine sai naga,"Sakina mijinta ya sauketa a mota,ya juya ganina yasa ta k'araso da fara'a,

"Naanah kece kice tare muka zo,ta fad'a tare da d'aukar Muhseen,murmushi nayi nace"Ai Anty Sakina na kasa gane gidan ne wallahi inanan ina tunanin Anya gidanne,

Dariya tayi tace"gidan ne mana ai yah Ameen ne ya gyarashi ya koma haka harda gidan malam sallau da yace zai sayar sai yah Ameen ya saya ya had'ewa su Abba,

Murmushi nayi harga Allah naji dad'in abinda yah Ameen yayi nace"ya kyauta,tare muka jera ciki,

Abba zaune akan kujera yasha wata shadda sosai yayi kyau ya k'ara haske da k'ima daman shi farin bafullatini ne,ai ina hangosa da gudu nayi kansa cikin tsartsar farin ciki,

"Oyoyo Abbana,shima rik'eni yayi cikin farin cikin ganina yace"Naanahta Naanahr Abba kece,nace"Abba nice Abbana yakake,Yace"lafiya qalau Naanahta,

Kusa dashi na zauna sannan na gaishesa,

Ya amsa cikin fara'a dajin dad'in ganina,

Sakina ma ta gaishesa,

Amsar Muhseen yayi daketa wangale masa baki yace"abokina dariyar ka arha gareta,

Nan muka fara hirar yaushe gamo,

Umma ta fito daga kitchin ganina yasa ta saki fuska,

"Maraba marhabun yau su Naanah ne a gidan,

Naanah ta d'ago cike da mamaki ta kalli Umma,sai tasaki fara'a taje gabanta ta duk'a,

"Umma ina wuni,d'agota tayi ta rungume,ai Naanah kusan suman tsaye tayi tace"Lafiya qalau 'yata ya kika baro mutanan gidan,

Ai Naanah saboda tsananin mamaki kasa magana tayi tana kallon Umma,

Umma ta fara hawaye tace"Naanah na cutar da rayuwarki kiyi hak'uri ki yafemin ko nasamu sauk'in abinda ke damuna tabbas na cutar dake amma naga illar cutar da d'an wani,

D'a na kowa ne kuma idan ka rik'i d'an wani tsakani da Allah kaima sai kaga naka basu wulak'anta ba,don bakasan wataran inda zasu fad'a ba

Naanah ki yafemin wallahi naga illar abinda na miki ko yanzun kece a sama,

Wai ashe duk abinda nake miki iyayenki sune ke tallafawa rayuwarmu,

Kuma d'ana shine yamiki ciki,Naanah ki yafe mana nida Ameen don Allah duk kuskure na ne,

Da sauri na rufe mata baki"a'a Umma ba laifinki a ciki k'addara ce kuma daman cen Allah ya rubuto sai hakan ta faru,

Wallahi ban ta6a rik'eki a zuciyata ba na yafe miki Umma Ke uwata ce wallahi har abada bazan dena kallonki a matsayin uwa ba,

Wannan ranar na dad'e ina jira na ganin nima kin d'aukeni 'ya,to Alhamdulillah Allah na gode maka dakasa Ummata ta gane gaskiya,

Rungumeni Umma tayi tana kuka"nagode Naanah hak'ik'a ke 'ya ta garice da ko wacce uwa xatayi alfahari da samunki Allah ya miki albarka,gaba d'aya muka amsa da ameen,

Yah Ameen da ya shugo duk yaji abinda akace murmushi yayi cikin jin dad'in abinda ya faru sannan ya juya,bai shugoba don karsu gansa,

Zaman da Naanah keyi a gidan Abbanta tanajin dad'inta Umma sai nan nan take da ita,ita da tayi niyyar kwana biyu sai gata har tafi sati daman suna hutu ne,koda suka koma,d'auko abubuwan karatunta tayi taci gaba da zuwa anan,

Momy harda mata tsiya tace"kin gujemu ko?,tace"a'a zan dawo ne momy,

Suna kitchin da Umma suna had'a abincin dare,saiga Rahma ta shugo a bige take tana tafe tana layi,tare da surutai burkitai,

Da sauri suka fito jin k'arar abu ya fad'i,ganin Rahna ce ke karo da kaya yasa Umma sakin kuka,

Tace"Naanah kin gani ko rashin tarbiyyar danawa yarana duk k'ok'arin da Abbanku keyi amma nid'in bana ta tasa a lokacin sai nake gani kamar baison yarana nane yau nayi da nasanin abinda na aikata,

Nace"Umma tabbas kece silar lalacewar Anty Rahma amma Allah gafurur rahimu ne tunda kinyi nadama saikiyi ta istigifari,sannan Rahma addu'arki take nema Allah dai yashirya ta,ta amsa da amin sannan muka koma kitchin mukaci gaba da aikinmu,Rahma kuwa anan ta zube barci mai nauyi ya kwasheta,

Zainab ta shugo da yamma muka fara hira tace"uhmm Naanah naga sai wani kyau na musamman kike k'arawa wa zai kalleki yace kekika haifi Muhseen,

Hararar wasa na buga mata nace"to uwar iya ya son ranki,tace''a'a haka nakeso amma meye sirrin ne,nace"na me?,

Dariya tayi "na kyawun mana ko duk yah Ameen d'inne,ai wani duka na kai mata ta goce"amma Zainab baki da kyirki wallahi,

Tace"to meye a ciki mijinki ne fa,harara ta na mata tace"uhm ni bari in kira my man wallahi yau abin dad'i nake so yasaya min,

IDo Naanah ta zaro😯kafin tayi magana har Sayyeed ya amsa kiran Zainab kashe murya taga Zainab tayi tace"Babyna kana inane,yace"ina wajen liyafar da muke kinsan mun kammala karatunmu,Tace"Alhamdulillah Babyna na tayaka murna amma inason ganinka,yace"karki damu Honey yanzun kuwa zanzo,sake kashe murya tayi"Babyna kazomin da abu me dad'i,

"Me kike so honey?"ai kasan duk abinda nake so,yace haka ne my honey sai nazo,suka yanke kiran,

Da yake speaker Zainab tasa hakan yasa duk Naanah taji hirarsu,

Tace"ehye Zainab yaushe kika kile haka,tace"tun ranar da na rabbatar na zama matar yah Sayyeed,

"Kai amma baki da kyirki haka kika lalata min d'an uwa,

Zainab ta kwashe da dariya"na lalatasa ko ya lalata ni,kedai wallahi Naanah ina sanar da ke kar ki tsaya kallon ruwa kwad'o ya hau miki k'afa idan zaki farka gara ki farka mijinki yah Ameen special ne samun kamarsa wallahi sa kamar wuya ni dai ina sanar miki ki mance komai ki rungumi mijinki


Kallon ta nayi nace.......
*🤰CIKIN WAYE?🤰*


       ❤❤❤❤
             ❤❤
                ❤


*STORY AND WRITING BY FATEEMAH SUNUSI RABEE'U*
*(UMMU AFFAN).*

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "CIKIN WAYE page 71 to 80"

Post a comment