Results

CIKIN WAYE page 81 to 90

Bismillahir rahmanir rahim

πŸ…Ώ️8️⃣1️⃣-9️⃣0️⃣


Nace"Amma baki da kyirki Zainab har kina cewa na mance da abinda yah Ameen yamin taya kike so na mance,nan hawaye ya fara zubar min,

Kusa dani ta matso tace"kiyi hakuri Naanah tabbas yah Ameen ba kyauta miki ba,amma kinsan k'addara tunda tun farko Allah ya rubuta miki hakan to dole ta same ki kiyi hakuri ki mance da komai ki ringumi mijinki da d'anki,

Dogon numfashi naja uhmmmm nace"shikenan zanyi tunani akan maganarki,tace"yauwa 'yar uwats,

Watar Zainab ce tayi k'ara tana dubawa ta mik'e"Sis bari inje Babyna ya iso,

Da sauri ta wuce,Naanah murmushi tayi aranta tace Zainab kenan,

Yau bata da Darasi hakan yasa tashirya tawa su Umma sallama cewa zataje gidan Didiy,

Tashirya kayanta har wajen mota Abba da Umma suka rakata,

Sannan ta wuce,tana isa da Fareeda taci karo da sauri ta amshi Muhseen tace"my son oyoyo,

Suka zube kan kujera,Naanah ta gaisheta ta amsa sannan tace"daga ina haka naganki harda akwati,

"Daga gidan Abba nake wallahi ina su Mameen ne,kan Fareeda tayi magana saiga Mameen na sakkowa daga bene,tace"ehye yau bak'i mukayi,

Murmushi Naanah tayi tace"ai kuwa Mamee,Fareeda tace"k'irik'iri kin guji gidan nan ko,nace"haba dai ya zan guji gudan nan,

Mamee tace"to ko tana nan kwana nawa ne tunda da auranta ko zatayi ta zama ne,

Tashi nayi jin wannan maganar don banso ayita na nufi d'akina dake gidan saman bed na fad'a ina sauke ajiyar zuciya,

Alhamdulillahi lokaci na ta tafiya,yayin da karatun mu keta zurfi sosai,

Shekarun Muhseen uku kenan yaro tubarkalla,kamarsa sak da Abbansa,kowa kaunarsa yake,yau yana wannan gida gobe yana wancen,

Daddy ne yace bazai yuwu ace muna da aure amma muna zaune gida ba,

Kasancewar Saura sati guda bikin Anty Fareeda Daddy yace duka tare za ayi hidimar biki harda tarewarmu,nayi kuka kamar raina zai fita don bana son tarewar nan,

Didiy da Mamee suka zaunar dani suksmin nasiha mai shiga jiki,

Didiy yace"haba Naanah Firdausi kiyi hakuri ki mayar da lamarinki ga Allah sai kiga komai yazo cikin sauk'i meyasa bazaki ya fewa Ameenu ba karki mance irin soyayyar da yaron nan yanuna miki,tabbas bai kyauta ba muma mun sani amma yazamuyi da hukun cin Allah ki zama mai tawakkali Naanah da mayar da Al Amuranki ga Allah,

Mamee tace"inda ke me tunani ce,baki ganin abunda yayi ta faruwa Allah yayi fa sai Ameen ya miki ciki idan ba hukuncin Allah ba babu yadda za'ayi ki 6ace harshi ya takurawa mahaifinsa sai sun d'auke ki kuma kiyi tunani bada son ransa ya aikata hakan gareki ba kuma sannan kiyi duba da yadda mahaifiyarsa taso zubda cikin tayi iya yinta akan sai cikin ya zube amma da yake ba'awa Allah wayau saida CIKIN yazo duniya,(K'alubale gareku iyayen da yaransu sukayi ciki suce dole sai an zubda ko yaran dake k'ok'ari wajen zubar da ciki kusani duk wanda Allah yasa yana da rabon zuwa duniya dole ne yaxo)don ba'awa Allah wayau ko dabara,

Mamee taci gaba dacewa"kiyi hakuri insha Allahu nan gaba nasan zakiyi farin ciki da had'in nan saikin yi Alfahari da samun Al-ameen a matsayin miji,

Jikin Naanah nayi sanyi sosai tabbas maganar iyayenta gaskiya ce,don haka tasawa ranta salama,amma tasan zuciyarta nA mata zafi,

Haka akayi ta shirin auran Fareeda tare da tarewar su Naanah,Fareeda wani attaji zata aura Alh Babale,matarsa daya yara uku,ba laifi yana kaunar Fareeda sosai itama tana sonsa kuma matarsa bata da matsala don tuni sukasan juna,

Momy ta mayar da Naanah wajenta inda take mata wani gyara da musamman da yake 'yar maiduguri ce Momyn tasan sirrin magungunan Mata dana K'amshi,

Wani irin kyau Naanah ta k'ara don sosai Momy ke gyaran d'iyar tata,

Marwan tuni suka daidaita da Salmarsa don yalura kusan irin halinsu d'aya da Naanah dukansu shirye shiryen tarewa kawai ake,

TUni Ameen ya idasa tambatsetsan gidansa da yake gidana,sosai gidan ya had'u sai yabawa ake,

Lokacin da aka zubawa Naanah jeran kayanta kuzo kuga kyau,uhmm wani abun sai manya fad'ama 6ata baki,Aini da nashiga K'auyanci na fara,uhmmm aljannar duniya kenan gaskiya fa ya had'u,

Shima Marwan ba laifi gidansa yayi kyau sosai hakama Sayyeed kasancewar yanzun zai fara aiki yasa Didiy ne ya mallaka masa gida babba mai kyau da tsari,

Dukansu an musu jere har Fareeda ita ma tare suke da uwar gidanta saidai kowa part dinsa da ban,


Akwatina goma sha biyu Ameen ya had'awa Naanah da kayan alfarma aciki na nunawa sa'a,shima MARWAN haka Sayyeed ma,abindai gaba d'aya sai son barka,

Tun saura kwana biyu biki ake shagulgula tuni bak'i na nesa dana kusa suka fara zuwa,ana abubuwa,

Anyi Mother's day,Wato ranar iyaye mata anyi hidima sosai a ranar sannan akazo akayi diner farty wanda shi na angwaye da amarene sai abokai da k'awaye,uhmm abin baya fad'o,ko da yake na hango 'yan CIKIN WAYE Fans,sunsha ankonsu gefe guda suma sunzo taya Ameen da Naanah murna,haka na hango WUSAID DA UWANI HANAN,Wato UWANIN QAUYE,DA Fans d'insu sunzo taya Ameen da Naanah murna,πŸ˜œπŸ˜œπŸ˜‚

Anyi abu agurin na girma da wayewa anci ansha taro ya watse lafiya(Naanah nawa CIKIN WAYE?FANS ban gajiya fatan kowa ya koma lafiyaπŸ˜‚πŸ˜‚)

Washe gari aka d'aura auran Fareeda da Alh Babale,da yamma aka gabatar da k'ayatacciyar walima da aka gaiyato babbar malamar addini,Malama Rabee'atu Safyan Kd,ta gabatar da wa'azi akan ma'aurata,tayi wa'azi sosai da nasiha inda jikin kowa yayi sanyi a gurin,

Wajen k'arfe bakwai na dare aka kai amare gidajensu,

Bayan nasihar da iyayensu Maza sukai musu sosai da kuka aka fitar dasu musamman Naanah da ta k'amk'ame Didiy tana kuka sosai shiya shigar da ita mota sannan aka d'aga da ita tana kuka da waiwaye,

Ahaka har gidan tana kuka,k'anwar Mamee Anty Raliya tace"shiga da bisimillah da k'afar dama,hakan tayi tana kuka,

Kan gadonta aka ajeta,mutane sai yaba tsarin gidan suke,wajen takwas darabi kowa ya watse,daman ba k'awaye garetaba,Zainab ce ita ma kuma tare aka fita dasu tayi d'akin nata mijin

Bayan ta tabbatar kowa ya gama fita mik'ewa tayi tare da cire mayafinta ta kalli ko ina na d'akin sakkowa tayi taje falo ta kalli komai tasami guri kan kujera ta zauna,

Afili tace"ka shugo lafiya ina jiranka zakaga tsiya kuwa,uhmmm wallahi Ameen zaka gane kuranka tunda na shugo gidan nan

Jin alamar shugowar mutum ta gyara zama tare da d'aura k'afa d'aya bisa d'aya tana kallon k'ofar idanuwanta tasssss......

Tofah ku buyoni donjin k'arshen littafin insha Allahu a page na gaba nakesa ran kammala muku wannan littafin

Idan naga ruwan comments zan muku da yamma,idan kuma ban sami lokaciba ko kuma na raina comments d'inku sai tomorrow,

Amma ina son inji sharhin me kuka fahimta acikin littafin nan,wanne irin darasi kuka d'auka,wanne abune mara kyau da za'ayi watsi dashi sai najiku,ina godiya da had'in kan da kuke bani musamman fans d'ina na FACEBOOK,ina godiyaπŸ™

Sai mun had'en,08104335144 whatsAPP me


Fateenku ceπŸ‘‡             Ummu Affan✍️✍️✍️
*🀰CIKIN WAYE?🀰*


       ❤❤❤❤
             ❤❤
                ❤


*STORY AND WRITING BY FATEEMAH SUNUSI RABEE'U*
*(UMMU AFFAN).*

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š

Bismillahir rahmanir rahim

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "CIKIN WAYE page 81 to 90"

Post a comment