Results

CIKIN WAYE page 91 to 100 end

Bismillahir rahmanir rahim

🅿️9️⃣1️⃣-1️⃣0️⃣0️⃣

Da sallama ya shugo hannayensa rik'e da manyan ledoji,ciki-ciki ta amsa don shikansa baiki mai tace ba,ta amsanne ma saboda ladar da takeson samu,

Ganinta zaune tana karkad'a k'afa alamar masifa takeji yasa yad'an saki k'ayataccen murmushinsa,

K'arasowa yayi yace"Sarauniya da girman kujerarki,harara ta banka masa,tare da kauda kai gefe,

Zaunawa yayi kusa da ita da sauri ta mik'e cikin fusata tace"meye hakan,yace"Allah ya baki hakuri kinsan kin zama hukuma saida rarrashi,

Tsaki taja mtuwww ta wuce,ya bita da kallo,Alwala tayi tazo ta gabatar da sallar asha'i da batayi ba tayi shafa'i da wuturi,

Tana addu'a ya shugo,bakin bed ya zauna yana kallonta harta gama,tare suka shafa yace"Allah ya amsa mana,banza ta masa,

Bayan ta nunke daddumar ta ajiye tare da cire hijabin,tace"malam don Allah katashi ka fita zan kwanta,yace"ba komai amma nasan bakici komai ba ga abinci nan kici,ko kallon inda ya nuna mata bataiba,mik'ewa yayi yace"pls Naanahta don Allah kici,murmushin mugunta tayi tace"to angaya maka bazanci bane ai idan nak'i cima ni zan cucikaina,cike da mamaki ya kalleta"ina Naanah ta koyo bak'ar magana haka jinjina kai kawai yayi ya fice,wani murmushin muguntar tayi,aranta tace zaka sani,

Ta d'auko pulet ta bud'e ledar bank'ararriyar kaza ce sai k'amshi da k'yilli take,ta zauna taci ta k'oshi ta kora da freesh milk dake cikin ledar(Wayaga su Naanah an zak'e anci kazar amarci ko kunya babu,uhmm wayaga su UMMU INTEESAR agari,Marubuciyar 'YAR GANTALI,ko kuwa kema Maman Khaleel haka kikayi lokacin naki marubuciyar KISHIYAR ZAMANI 🤣🤣🤣Ana tare 'yan uwa loll)

Tunda tayi sallar asuba bata tashiba sai wajen goma na safe,toilet ts fad'a ta tsantsara wankanta bayan ta fito kan diresin merror ta zauna ta tsantsara kwalliya kai kace gasar kyawu zataje,

Wasu fitattun kaya danaga Naanah ta ciro saida na zaro ido😯Siket da riga ne na kanti,siket d'in saboda kankantarsa har mazaunanta ana hange gashi ya kamata sosai rigar kuwa ko cibi bata rufe mata ba ta d'aure gashin kanta daman akwance yake tasa ribon,ko kallabi bata d'auraba ta saka cingam abakinta ji kake k'as-k'as tayo falo bayan ta zura wani dogon takalmi mai shegen tsini,tana tako d'aid'ai,

Alokacin Ameen na farlour tun dawowarsa masallaci bayan yayi wanka yanawo farlour yana kallon labarai,tunda tafito ya zuba mata ido cike da mamaki yayinda k'irjinsa ke bugawa da k'arfi,ta maza yayi bayan ya daure ya daddage ya kauda fuska yana murmushi,

Gabansa ta tsaya ba gaisuwa tace"kayi mana girki ko don yunwa nakeji,kuma bansjin zan ta6a girki agidan nan,murmushi yasake yace"My sweetheat ko gaisuwa babu to fatan kin tashi lafiya,ya mitsa fuska tayi "daban tashiba zaka ganni,

Yace"to Allah ya baki hakuri ga abinci cen an aiko daga gidan Momy,dinning table ta nufa tana kwarkwasa ta juya mazaunai,binta yayi da kallo,tana zama ta d'ago kai da sauri ya kauda mursa,murmushin mugunta tayi,

Yau satin guda da tarewar su Naanah kullum da sabon salon da take kawowa nasaka kaya iri iri masu matuk'ar tada sha'awa,Ameen bai ta6a cewa komaiba bama daki guda suke kwanaba duk da ba k'aramin gasasa takeba kai harma da suya haka yake daurewa bai ta6a nuna mata yana buk'atar taba,

6angaransu Marwan masha Allah sun fahimci juna ysyin da suke zuba soyayyarsu,sosai yanzun suke son junansu,hakama su Zainab sai fatan alkhairi,itama Anty Fareeda suna zama lafiya da abokiyar zamanta kowa na girmama kowa,

Yau shuru ba akawo abinci daga gidan Momy ba,

Naanah ta fito daga bedroom cikin shigar wasu riga da wando wad'anda suka kamata sosai,tasha kwalliya,

"Yah Ameen nifa yunwa nakeji,ta fad'a cikin tsantsar shagwa6a,idanuwa ya zuba mata cike da sha'awa,hura masa ido tayi,tare da turo baki gaba"magana fa nake maka ka zubamin ido ko baka ta6a ganina bane,

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace"Momy tace tunda munyi sati biyu tadena kawo mana abinci,

Tace"sai katashi kamana ni yunwa nakeji,zaro ido yayi yace"haba Naanah kiyi hakuri ki mana kinsan ni ba iya girki nayiba,turo baki ta yi"aiko kama koya daga yau,

Ganin baida niyyar tashi tasa kukan shaga6a"wayyo cikina yunwa nakeji,zai kasheni ya hanani abinci,da sauri ya mik'e "Allah ya baki hakuri bari na siyo miki a hotal,kuka tasake saki"ni wallahi banso da kanka zakayimin,

Huci ya furzar kai Naanah rigima yace"shekenan bari na miki,rigar jikinsa ta shadda ya cire yabar singilet da wandon,ganin yadda kwantaccen gashin k'irjinsa yafito akan faffad'an k'irjinsa yasa Naanah kauda kai tana harare harare,girgiza kai yayi ya nufi kitchin,tabi bayansa da kallo bafa kushe yah Ameen ya had'u ajin farko ne,

Fama yake tayi,yarasa me zai had'a dame dominshi idan ba ruwan tea ba ba'abinda ya'iya,ya share gumin dake ta feso masa,ruwa ya xuba a tukunya bayan ya kunna gas,sannan ya zuba markad'an kayan miya masu uban yawa da yamarkad'a yazuba uban kishiri da maggi,sai curry,bayan ya gama wannan ya d'auko taliya yasa sannan ya zuba mai🤣🤣🤣daga jin wannan girki zai had'u fa,(Maman khaleel bisimillah),

Daman ruwa kad'an ya zuba nan da nan ya tsotse sai kawai ya sauke,ko dahuwa bataifa,murmushi yay yauwa Alhamdulillah ashe daman na iya girki,ya sami pulet ya juye sannan ya d'auko chokula biyu ya fito,

Tana nan inda yabarta,ai kallo d'aya ta masa ta saki dariya ganin yadda duk ya had'a gumi ga mai a goshinsa wajen share zufa ya goga,amma 6oye dariyarta tayi,a gabanta ya ajiye,kallo d'aya zakawa abincin ka gane na musammanne🤪,

Gyara zama tayi tasa chokali,ai loma d'aya ta furzar da gudu tayi toilet tana kakarin amai da sauri ya bita yana mata sannu,bayan ta gama ta galla masa harara,"haka ake girki,sai kuma tasaka kuka rungumeta yayi yana lallashi"sorry my dear bari na sayo miki,turesa tayi ta nufi d'aki,

Haka rayuwa taci gaba har sukai wata biyu Naanah na gasawa Ameen aya a hannu bata kulasa bata girki kullum shine sayo abinci ga shigar da take ta firgita 'yan maza🤪,

Zainab ce takawo mata ziyara,Sayyeed ya kawota,bayan sun gaisa ya wuce office da yake yafara aiki,shima yah Ameen lokacin baya gida,

Zainab tace "amarya kinsha k'amshi ya amarcin,murmushi nayi"amarci yana gurinku ku amare,harara ta bankamin"ke banson rainin wayau badai haryanzu kina gasa bawan Allah nan ba,

Dariya Naanah ta tuntsure anan take sanar da Zainab duk abinda ke faruwa ta d'aura da cewa"nayi masa hakanne don in gane da gaske k'aunata yake ko sha'awata alhamdulillah yaci jarabawa ni kaina nayi mamakin abinda na aikata masa,

Gaba d'aya sukasala dariya Zainab tace"lallai hakan da kikayi daidai ne,yanzun sai abasa gara ya kwasa,"ke zainab banson iskanci fa,tasa dariya to k'arya nayi don Allah ki tausaya masa haka wallahi ya bani tausayi,sukasa dariya haka sukai ta hirarsu da yamma tare suka shiga kitchin suka shirya abinci mai rai da lafiya abinda Naanah bata ta6ayi ba a gidan girki sai yau,sosai suka gyara gidan ko ina yad'au k'amshi,

Wajen biyar yah Sayyeed yazo yatafi da Zainab bayan fitarsu,toilet na fad'a nayi wanka,saida nayi sallar isha'i sannan na shirya kaina cikin wasu had'addun kayan barci,sosai suka amshe ni,

Tundaga harabar gidan Yah Ameen kejin tashin k'amshi cike da mamaki ya shiga ciki,ai lumshe idanuwansa yayi saboda dad'in kamshin da yashak'a a cikin farlour,

Da sallama ya shugo,Naanah dake zaune a farlour ta taso da sauri ta amshi jakar dake hannunsa "Sannu da dawowa Yayanah,ido ya zuba mata cike da mamaki hanyar bedroom dinsa ta nufa,ganin bai taho ba ta juyo,murmushi ta sakar masa ganin ita kawai yake kallo"kazo muje mana,

Haka yabi bayanta cike da mamaki,guri ta samu ta'ajiye masa jakar office,sannan ta duka,ta kwance igiyoyi ta kalminsa ta zare masa,harzuwa lokacin kallonta yake cike da mamaki,

Mik'ewa tayi,"na had'a maka ruwan wanka,kagama shiryawa kafito abinci yana jiranka,ta wuce,binta yayi da kallo kafin ya mik'e yacire kayan jikinsa,ya fad'a bathroom

Bayan ya gama shirinsa ya fito don saida yayi sallah sannan ya shugo gida,tana ganinsa ta mik'e suka nufi dinning tare,

Ta zuba masa lafiyayyar farar shinkafa da dasu kabeji da biyar zallar naman kaji,ta tsiyaya masa sanyayyen kunun ayan da ta dama,tun kafin yakai baki yake faman had'iye yau sbd k'amshin da ya bid'esa,

Sosai yaci abincin don rabonsa da yaci abinci irin haka tunda Momy ta dena aiko musu da abinci donshi ya tsani abincin saya k'amk'ami garesa,

Bayan sun kammala falo suka dawo,suna kallo,ganin ta fara hamma ta mik'e,"Yayanah sai da safe,ta d'aga masa hannu,binta yayi da kallo tare da had'iye yawu🤪,

Tashi yayi yabi bayanta,kan bed ta fad'a,zata gara kwanciya ta gansa,gabanta ya buga da k'arfi,tace"yah Ameen lfy,

Zaunawa yayi bakin gadon ya ruk'o hannayenta duka biyun yace"please My dear,duk wannan wasan kwaikwayon damuke ya isa haka,kinga yanzun mun ruga munzama d'aya don Allah Naanah kiyi hkr ki mance da komai,

Numfashi taja cike da tsoro ganin yadda yake murza mata 'yan yatsu,tace"shikenan komai ya wuce,da sauri ya rungumeta yace"yauwa Tawan nagode,

Haka suka kwana cikin farin ciki washe gari sai nan2 yake da ita,wajen k'arfe tara ya shugo da leda da ya sayo musu kaza da freesh milk,sukaci cikin farin ciki,

Yace"Babyna kiyo alwala kizo muyi sallah don godewa Allah dayasa muka kasance ma'aurata,gabanta ne ya buga da k'arfi tace"to,asanyaye ta tashi ta dauro alwala,

Nan sukayi sallah bayan sun idar,ya kama goshinta ya mata addu'ar da manzon Allah ya koyar,daga nan saifa zancen ya sauya salo,

Wani irin hut kissing yake aika mata,tun anayi ak'asa har aka koma saman bed,tunifa hankalinsa ya gushe,Naanah kuwa ganin abin bana k'are bane ta fara hawaye,

Kai nima da naga abin yafi k'arfina farlour na koma,gefin asuba na koma jin Ameen na sauke numfashi Naanah kuwa kuka take,tasowa yayi ya rungumeta,

Albarka kawai yake samata,Fad'i yake Naanah ketadanbance wallahi badanni na aikata miki abinda ya faruba wllh da sai ince sharri aka miki,'anya kuwa ke kika haifi Muhseen,

Turesa tayi cikin shagwa6a tace"ban sani ba,

Chak ya d'auketa yayi bathroom da ita dakansa ya mata wanka shima yayi sannan suka fito,

Ai tundaga wannan rana Ameen da Naanah suka d'unke soyayya mai tsafta suke gabatarwa,

Al'amura dayawa sunci gaba da faruwa,

Kammala karatun su Naanah da k'arin girma da Ameen ya samu gurin aiki,

Abindai sai sam barka,Zainab ta haifi yaronta,me sunan Daddy ana kiransa Hanif,itama Salma ta haifi me Sunan Hajiya ana kiranta Khairat,

Rahma kuwa sai abinda Allah yayicdomin abin nata yayi yawa,watarana tayo shaye shayenta,tahau babban titi bata saniba wata mota tazo tayi ciki da ita tabin takan k'afafuwanta,me motar ya gudu,aka kwasheta sai asibiti yanzun dai haka tana gida ba inda take zuwa,kuma ba k'afafuwa,

Zuwa yanzu Yaran Naanah uku harda Muhseen hudu,bayan Muhseen tagwaye tayi duk mata shekararsu uku ta musu kani,me sunan Abba,sunace masa Abiey,

Ameen ne ya shugo gida,ya dawo daga office,da gudu yaran sukayo kansa"oyoyo Abbanmu,d'aya bayan d'aya ya dunga d'agasu,sannan ya rungume Abiey,

Naanah ta turo baki gama cikin shagwa6a tace"ni kad'aice ba ad'aga ba wllh bazan yarda ba,da saurin ya saukar da Abiey yace"sorry princess,zuwa yayi ya rungumeta ya had'a da yaran ya rungume yace"Alhamdulillahi Allah ya rayamin zuriyata,duka suka amsa da amin,


Nima anan nake cewa ALHAMDULILLAHI

Allah na godemaka da kabani ikon sauke wannan littafin me suna CIKIN WAYE?Alkhairan dake cikinsa Allah yasa damu dasu akasin kuma Allah ya karamu dashi,

Ina godiya da goyan bayan da kuka bani tundaga farko har zuwa k'arshen littafin,

Godiya ga Anty Hauwa shugabar kungiyar arewa Allah ya arbarkaci zuri'arki,

Jinjina ga Hussaini 80k,nagode Allah yabarzuminci ya baka mata tagari,muzo musha biki loll🤪😂

Fatan alkhairi ga duk wata member ta kungiyar arewa writers

Masoyana kuma na gode muku sosai ana together🤝🤝ina sonku fiye da tunaninku sai mun had'e a sabon Novel d'ina🤝😂

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including  your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "CIKIN WAYE page 91 to 100 end"

Post a comment