Results

DAJIN DUHU 21

dajin duhu 27
haka akacigaba da yaki hargari yasakewayewa amma barde haimas baigaxaba al'amarin daya kara jefani cikin mamaki kenan nakuma tabbatr lallai akwai wani sirri dabansaniba danganeda barde haimas ba'a gusheba anayaki har dare yayi a wannan rana visa mamaki sai dakarun taron dangi suka ja da baya 

suka bar yakin suka koma cikin sansaninsu suka zazzauna suna hutawa yayinda nikuma da barde haimas muka shiga cikin gidana shigarmu keda wuya barde haimas yafadi kasa yana nishi sama sama narigada nasan tsananin tsabar gajiyace tadamesa Dan haka cikin sauri naje nahada ruwan xafi nakai masa bayi nadawo nafada masa yakai jarumin jarumai kadaure kaje ka watsa ruwa koka samu karfin jikinka barde haimas yayi murmushi yamike yaje yayi wanka yadawo sannan yagbatar da Ibadunsa ga ubangijin Mosulunci bayan yakare duk abinda zaiyi sainamatso kusadashi nace yakai wannan jarumi 

mekake tunani danganeda wannan janyewa da dakarun taron dangi sukayi tabbas akwai alamar tambaya ? yaya kwana 3 muna gabxa yaki dasu basu janyeba yaukuma rana daya sujanye lallai akwai wani tuggu dasuka shirya mana Wanda mu bamusanshiba koda jin haka sai barde haimas yace nima tabbas nayi tunanin haka amma koma miye suka shirya ubangijin musulunci yana kallo kuma tabbas baxasuyi nasaraba akanmu kota wanne hali koda naji haka sainace yakai wannan jarumi miye karfin 

gwiwarka da tabbacinka akan ubangijin musulunci xai agaza mana koda Barde haimas yaji wannan tambaya tawa saiya dubeni cikin tsananin mamaki yace tabbas Wanda yabace yabace yanxu kaibaka. tunani da abinda yafaru tsakanina da dakarun taron dangi nayi yaki natsawon kwana uku baci basha baixama hujja agrekaba nayi yaki da dakaru fiyeda dubu ashirin basuyi galabar kasheniba shima 

baizama hujja agarekaba miyesa idan tsafinka gaskiyane baikarekaba dafa yunwa da kishirwa har saida kagudu kaje kaci abinci kahuta kadawo dukda kasancewar kana yakine visa lamarin tsafi bawai dakarfin damtsenkaba kona jarumta kodanaji haka sai nayi shiru inamai sunkuyardakaina Dan duo abinda barde haimas yafada gaskiyane banida ja daga nan naga yatashi yaje yawanke fuskarza hannunsa xuwa 

kafafunsa yayi shimfida yacigaba da bautarsa harxuwa gabannin asuba sannan yadan kwanta yayi baccinda baifa sa'a dayaba gari yafara haske nan da nan yamike yashiga dammarun yaki yadauki garkuwarsa da takobinsa mai taken gayawa jini nawuce yayi gagarumar shigar yaki mai ban tsoro yafito nima na shiga shiri nadauki jakar tsafina da sandar tsafina nafito al'amari. dakarun taron dangi kuwa
..
.
bayan wannn janyewa dasukayi sai suka koma cikin sansani nanfa yarima kaimar da sarkin yaki suka kama dura musu ashariya. suna tsine musu suna kaiconku taron banxa ace duk yawanku mutum daya yagagareku yaxamemuku alkakaki saikasheku yakeyi tsawon kwana uku baihutaba amma kunkasa koda lakutar jikinsa lallai wuta xatayi fushidaku xaku kasanece cikin tabewa gafalalu Dan haka gobe idan xamu taresu yaxama dole mukoma cikin lamarin tsafi INA shugaban dakarun bakar runduna nan take wani barde kato mai katon kai da mummnar suffa duk jikinsa amumurde yake yazo yatsugunna gaban yarima

 kaimar yace gabe idan xamuyaki subarde haimas inabukatar kaida rundunarka kuhadu guri daya kuxama mikiyar tsafi kutunkari barde haimas kudinfa kaimasa harita sama yace angama yashugabana daga nan yatashi yatafi yarima kaimar yasake kiran wani shugaba nawata runduna yace inashugaban rundunar kare dangi nan ma wani barde yafito yatsugunna gaban yarima kaimar shima yacemasa agobe inason kaida rundunarka Ku koma cikin lamarin tsafi kudawo suffar gwaggon biri kudinfa yakar barde haimas 

takasa yace angama yashugaba yakira sugaban rundunar azzaluma shima yaxo yaduka agabansa yace kukuma agobe inason kota wanne hali kukamamin wannan bokan take shima yakarbi umurni koda gari ya waye muka fito filin daga muka tsaya nida barde haimas saimukaga runduna takasu kashi uku kashina farko suka rikide sukaxama wata katuwar mikiya wadda girmanta da muninta makadai ya isa yasaka karamin jarumi fitsari a wandonsa mikiyar tanada dogayen farata masu tsananin kaifida tsini sannan tanada jajayen idanu kamar rana xata fadi kai hatta gashi. dake jikin fuka fukanta kaifine kamar 

takobi nan fa mikiyar tayiwata kuruwa wacce dukkanin birnin saida ya amsa sannan runduna tabiyu tarikide taxama wani katon gwaggon biri mai tsananin girma da muni ahannunsa nahagu yanarikeda wata Katuwar majaujawa wacce kodaru arba'inbasu isa sundagataba ahannunsa nahagu kuma wata katuwar takobice mai tsananin girma da kaifi tabaiyana shima nan take yayi wata kururuwa mai tsananin firgitarwa lokaci daya kamar hadinn vaki shida mikiyar nan sukayo kan barde haimas nikuma rundunar mutanen nan tayo kaina mukayi mugun gamo

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "DAJIN DUHU 21"

Post a comment