Results

DAJIN DUHU 22

DAJIN DUHU 28

koda muka hadu saimuka kacame da axababben yaki nida runduna ta uku inajifarsu da kofofin bala'i natsafi yayinda suma naga suna maido minda martanin nan da nan guri ya hargitse atabangaren barde haimas ma haka takasance tsakaninshida wadannan mikiya dakuma gwaggon biri na sihiri yaxama

sun kuntata mishi suna kaimishi hari ta sama da kasa nan da nan suka fara Neman kuntata mishi duk sanda wannan birin yakawo masa Sara da gudumar dake hannunsa idan yayi tsalle yakaucewa harin duk abinda gudumar tasamu walau dutse bishiya ko kuma dirkar gini take abin xaiyi raga raga yaxama gari itakuwa wannan mikiyar duk sandata kawo masa wafta da yatsunta idan yakauce

komaye tasamu take take ketasa gida biyu idanko takawo masa yanka da fuka fukanta masu tsananin kaifi da tsini duk abinda tasamu saita rabashi gida biyu koda kuwa katon dutsen ko bishiya komadai miye haka akayita gumurxu tsawon sa'a daya a wannan lokacinne fa wannan birin yayi nasarar sarar

barde haimas agadon bayansa take gurinya dare jini yayi feshi barde haimas baisan sanda ya kwala ihuba saboda tsabar tsananin xafi da xogi kafinya rufe bakinsa tuni wannan mikiya itama takafa masa kumbunanta akirjinsa suka nutse take jini yayi tsartuwa daga kirjin NASA nan fa yakara yin wata

kururuwa wacce tasa gaba daya yakinya jagule domin dawakai suka cigaba dayin haniniya suna kayarda mahayansu saboda tsorata kanan jarumai suka fara cika wandunansu da iska duk wannan kururuwar dayakeyi yana adukene batareda yadagoba yana mai dafe kirjinsa hatta ita kanta wannan

mikiya dakuma wannan birin na tsafi saida suka tsorata suka Jada baya sukai cirko cirko bayan kamar dakika sittin barde haimas yamike yana maitangadi a wannan lokacin Dana dubi idanunsa narantse dagirman tsafi nadauka wutace keci acikinsu saboda tsananin ja dasukayi saboda tsabar fushida fusata

 koda yagama mikewa tsaye saiya dubi bangarena yaga nima yakin namu yatsaya wato wannan runduna tadena yakata duk kowa yashiga taitayinsa saboda ganin wannan

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "DAJIN DUHU 22"

Post a comment