Results

KAINE SANADI page 11 to 20


   KAINE!SANADIï¼?

💘💘💘💘💘💘💘💘

 

 

Story and written by

Fateemah Sunusi Rabee'u

Ummu Affan

 

Wannan littafi na kud'i ne duk meso sai ya nemeni ta WhatsApp numberta 08104335144 don Allah ku da kuka saya karku fitarmin dashi na rok'eku,tamkar amana yake agare ku.

 

Bisillahir rahmanir rahim

 

🅿�11-12

 

Bayan sun gaisa dame gadi ta kutsa kanta ciki,kai tsaye 6angaran JB ta wuce don taga alamar kamar nan ne part d'insa,koda taje bakin k'ofar sai tayi siranda ta kasa koda motsi a zuciyarta tc"idan kinshiga me zaki ce masa?wai kinyi tunani kuwa Nutailah kefa macece me zakiyi wajen d'ana namiji?wata zuciyar ta bata amsa da "hkr zan basa domin ya fita daga rayuwata,halan yabata k'warin gwiyar fara buga k'ofar,

 

Sbd bugun da k'yirjinta yake ji take kamar zai fasa gida biyu,bud'e k'ofar taji anyi,zubawa juna ido sukayi da sauri tayi k'asa cike da kame kame,

 

Juyawa yayi ya koma ciki amma a zuciyarsa yana tunanin me ya kawo yarinyarnan gidansa,shugowa tayi,k'amshin turarensa ya bugi hancinta gabanta be dena fad'uwa,gabansa ta zube tace"don Allah kayi hkr akan abunda ya faru naji nikeda laifi amma in Allah ya yarda hakan bazai sake faruwa,

 

Zaunawa yayi bisa luntsumemiyar kujerar dake farloursa,zuba mata manyan idanuwansa yayi yace"meyasa kike bani hkr byn kince nid'in banxa kud'ina na bansa,dariya yai snn ya d'aure"ai tinda kika gayamin bak'ar mgn dole nayi maganinki bazan barki ba dole na rama abinda kikamin saina zame miki SANADIN da saikinyi da nasanin abinda kikamin,

 

Tuni zuciyar Nutailah tayi zafi ba komai yasa taxo bashi hkr saidon bata son Innarta taji cewa har yanzu bata kiyayesa ba,mik'ewa tayi wani kallo ta wurga masa tace"me kake da suna Jb ko me?to koma menene kai kasani Allah ya gani nabaka hkr tunda bazaka hak'ura ba to muzuba mugani,

 

Wata irin funcikota da yayi sai gata gabansa har suna shak'ar numfashin juna da sauri tayi baya,

 

"Yace"k'aryar banza kike ke k'aramar 'yar bariki ce,zan nuna miki kin ta6o wanda zai gyara miki zama,murmushin takaici tayi tace "saidai mugyarawa juna zama,

 

Juyawa tayi tafice da sauri,dunk'ule hannunsa yai ya bugi iska yace"cheef d'iyar matsiyata ta shugo har gidan ubana ta gayamin mgn zan nuna mata kuskuranta,

 

Tana fitowa sukayi kichimis da Beenafah,kallon kallo suka farawa juna,Beenafah ta k'araso tana kallon Nutailah cike da tuhuma tace"me yakaiki part d'in Jb�,inda inda ta fara"a'....wai...da.....wai..da...man,"wai daman me?ki natsu ki sanar dani,

 

Kasa mgn tayi sai kawai ta juya tabar gurin da sauri gate ta fita tayi gidansu,Beenafah tabi bayanta da kallo kafin ta girgiza kai ta wuce,

 

****************�

 

Sosai yau suke murna Sbd Dad yaune zai dawo an tarbesa da abinci danasha kala-kala,Mum da Beenafah suna ckn murna da frn ciki haka Jb,ranar hk nan ya daure bai fita ba don shegen yawo ne dashi baison zama gida sai yawan bi club,

 

Direba ya d'aukosa daga Air port,Yana shugowa Beenafah ta ruga ta k'amk'amesa tana masa oyoyo,shima ya rungumeta cike da k'aunarta,

 

Turo baki gaba Jb yayi yana harararta akanme zata rigasa zuwa gurin Dad dinsa sai kace nata ya fad'a aransa,sakinta Dad yayi ya rungume Jb yana bugun bynsa alamar rarrashi don yasansa da kishi,

 

Bayan anci ansha Dad ya wuce ciki don watsa ruwa Mum tabi bynsa,sai Jb da Beenafah,kallonsa tayi tace"yah Jb daman don Allah yau inaso kakaini Super Market zanyi sayayya,

 

Wani kallon banza ya mata kafin yace"waye direbanki?ko babu direba gidan ne?ko kuwa ke baki iya tuk'in bane?mtsuuuww yaja tsaki yacigaba dacewa"ke ba 'yar gida ba sai shegen iyayi da felek'e,mik'ewa yayi yabarta agurin,binsa tayi da kallo har yabar gurin ajiyar zcy taja kafin ta furta"yah Jb kaine kawai za6in zcyt inasonka yayanah da sannu zan gyara maka rayuwa......

 

 

'ANYA KUWA BEENAFAH ZAKI IYA😂😂

 

Ummu Affan,don Allah karku turawa kowa na kud'i ne littafin duk meso ya nemeni👏

4/10/20, 12:44 PM - +234 902 070 1465: 💖💖💖💖💖💖💖💖

  KAINE!SANADIï¼?

💘💘💘💘💘💘💘💘

 

Story and written by

Fateemah Sunusi Rabee'u

Ummu Affan

 

Wannan littafin na kud'i ne duk meso ya nemeni ta WhatsApp numberta 08104335144 don Allah ku dakuka saya karku fitarmin dashi na rok'eku,tamkar amana yake a gareku

 

Bismillahir rahmanir rahim

 

🅿�19-20

 

Yace"Na nemarwa d'anki aure ne,ai daga Mum har Jb lokaci guda suka mik'e,mum tace"aure kuma Alhj,yace"eh aure domin aure ne kawai zai dawo da Jabeer hayyacinsa ckn wnn mummunar rayuwar da ya jefa kansa ciki,

 

Jiki a sa6ule Mum ta zauna,shi kuwa Jb ya kasa zama,Dad yace"sami guri ka zauna,ahankali ya wani zauna ja6as,Dad yace"Jabeer kasan bazan ta6a maka za6en tumun dare ba ka kwantar da hankalinka ni nasan nan gaba zakayi alfahari da xa6in dana maka,

 

Ai sbd tsabar takaici ma,kasa mgn JB yayi kwatakwata ma bai gane inda mgnr Dad ta nufa,shi za'awa aure"to dawa?amma fa an cucesa ba kad'an ba yanzu wai ace shiza'awa aure bayan xa tsarin aure anan kusa a gurinsa ji yake kamar zcyrsa zata buga,

 

Mum tace"wai wacece zaya aura ne,ta fad'i hakan cike da takaici amma idan xaka kalli fuskarta bazaka ta6a gane hakan ba,Dad yace"yarinyar wajen Malam Habu mak'otanmu naga

yarinyar tana da hnkl ga natsuwa,

 

Ai da sauri Mum ta sake mik'ewa domin yadda takejin ta tsani Nutailah tun farkon ganinta da ita,tace"yanzu Alhj ka rasa wacce zaka had'a da yaron nan sai wnn k'aramar yarinyar da ko secondry bata kammala ba yarinyar Habu wanda beda sana'aryi sai zaman kashe wando dayi da mutane,

 

Yace"don Allah Hjy ya isa hk ni naga dacewar hakan yasa nayi,zama tayi ji take kamar zcyrta zata fasa amma bazaka ta6a gane hakan a fuskarta ba,cikin sanyin murya tace"Allah ya huci zcyrka Alhj ni da wai Beenafah nake taso Jabeer ya aura sai nake ganin kamar zasu fi dacewa,

 

Yace"meyasa tun tuni baki fad'a ba sai yanzu tabbas Beenafah ma tana da tata natsuwar saidai mun riga mun gaba mgn da iyayen yrnyr nan da wata guda za'ayi biki,saidai ko nan gaba idan yana da ra'ayi sai ya had'a da Beenafar,jigun tayi sbd takaici amma tasa aranta dole ne fa sai Jb ya auri Beenafah idan yasan wata ai baisan wata ba,

 

 

Jb kuwa tunda yayi k'asa da kansa ko d'ago fuska ya kasa sbd tsabar rud'in da yashiga ji yayi kansa ya masa wani nauyi kamar wanda aka d'aurawa k'atun dutse akansa sbd nauyin da kan ya masa idanuwan nan nasa sun kad'a sunyi jawul sbd 6acin rai,

 

Bayajin zai iya sa6a mgnr mahaifinsa tabbas Dad yana kaunarsa da kaunar farin cikisa amma a wnn karon yazo masa da babban abu,da yaji abin da mum tace gami da a had'ashi da Beenafah aransa yace"so suke kawai suga bayansa idan suka aura masa mata biyu ai sun kashesa,

 

Dad ne ya katse masa tunani da cewa "cikin satin nan inaso kashirya domin zuwa kaga yarinyar,da kyar ya iya d'ago kai ya amsa da "to Dad,snn ya mik'e yace"bari naje na kwanta Dad,yace"shikenan ka kwantar da hnklinka nasan idan kaga yrinyr zaka sota,gyad'a kansa kawai yayi ya wuce,

 

Kan bed ya fad'a rik'e da kansa da ke barazanar tarwatsewa,aransa yace ko wacece yarinyar nan sai ya gana mata axabar da sai tayi tunanin dama batazo duniyar ba wllh saitayi da nasanin batasan sa ba kuma bata amince da auransa ba wnn kenan,

 

 

Malam Habu ya kalli Innar Nutailah ya sanar da ita duk yadda sukayi da Alhj Mukhtar,da sauri ta rik'e k'irji tace"aure kuma malam duka yrnyr nan nawa take yanzu kai sbd abin duniya zaka bayar da 'yarka wnn ai siyar da ita ma zakayi,

 

Harara ya banka mata yace"daman nasan saikinyi mgnr banxa data wofi to koma mai zakice saidai kice 'yata dai tawa ce kuma na bawa d'an Alhj Mukhtar auranta,wnn mgnr daidai a kunnan Nutailah da k'arfi k'irjinta ya buga dammmm!nan take ruwan hawaye ya tsinkewa fuskarta,

 

Muryar Innah taji na cewa"Malam yrnyr nan fa nasan batason yaron nan domin ita Sayyeed ta keso yaron Malam Saminu,wani dogon tsaki yaja yace"wanne Saminu wanda yake kasa kaya a kasuwa na hatsi kayan da basu wuce buhu biyu ba idan aka had'asu d'ansa zan bawa auran 'yata,

 

Rik'e baki tayi tace"to ai ya fika tunda shi da sana'arsa kai me kake siyarwa,yace"duk abinda zakice saidai kice amma aure babu fashi nan da kwana ashirin da biyar domin wata guda mukasa kuma anci kwanaki biyar,

 

Nutailah najin haka tafita waje da gudu tana kuka,sosai take gudu ta nufi.......

 

Tofa ina kuma Nutailah ta nufa sai kun biyoni

 

Don Allah kar ku turawa kowa wnn book na kud'i ne meso ya nemeni,

 

 

 

Ummu Affan


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "KAINE SANADI page 11 to 20"

Post a comment