Results

KAINE SANADI page 21 to 30


Ummu Affan

4/10/20, 12:44 PM - +234 902 070 1465: 💖💖💖💖💖💖💖💖

  KAINE!SANADIï¼?

💘💘💘💘💘💘💘💘

 

Story and written by

Fateemah Sunusi Rabee'u

Ummu Affan

 

Wannan littafin na kud'i ne duk meso ya nemeni ta WhatsApp numberta 08104335144 don Allah ku dakuka saya karku fitarmin dashi na rok'eku,tamkar amana yake a gareku

 

Bismillahir rahmanir rahim

 

🅿�21-22

 

 

Sosai take gudu bata sauka ko ina ba sai gidansu Sayyeed,zaune ta iskesu Mmn Sayyeed dashi da harda Babansa da alama wata mgnr suke tattaunawa,

 

Jikin Mama ta fad'a tana kuka sosai,nan take duka hnklinsu ya tashi tambayarta suke lfy,cikin kuka take sanar dasu abinda taji Babanta yace"da sauri Sayyeed ya mik'e cike da tashin hnkl yanacewa"Jb kuma Baba yasan halin Jb kuwa yake son had'aku,nace"Wllh yasani son abin duniya ne kawai yakeson kai rayuwata inda bata daceba,

 

Mama ta rufemin baki tace"kull nasake jin kin fad'i haka ga mahaifinki,idan haka Allah ya k'addara miki baki da yadda zakiyi addu'a ita zaki rik'a Nutailah Allah ya tabbatar miki da abinda yafi alkhairi agareki,

 

Sosai Nutailah ke kuka tace"bana sonsa Mama wayyo nashiga tara,ta kurma ihu,Dukansu suka Rud'e musamman yah Sayyeed wanda yakejin zcyrsa kamar zata fashe,

 

Baba yace"hkr zaki Nutailah kibi za6in iyayenki shine mafi alkhairi agareki,nan suka dunga mata nasiha da wa'azi har tadena kukan domin Nutailah Allah ya d'aura mata wani abu shine hkr da tawakkali,

 

Tare suka fito da Yah Sayyeed ta kallesa tana hwy shima idanuwansa jawul suke tace"yah Sayyeed naji bak'in ckn wnn abu,banso ba inama Babana za6i ya bani da banda miji da ya wuceka amma inaso kasani ina sonka,hwy a tsinke mata,

 

Shima dauriya yake donji yake kamar yayi kukan yace"ya zamuyi hk Allah ya rubuto mana da man ke ba matata bace kinsan matar mutum kabarinsa amma banajin har abada xan dena k'aunarki Nutailah,shima sai hawaye duka suka had'u suna kuka zuciyoyinsu sukayi rauni,

 

Dole shine yayi shuru ya dawo yana rarrashinta hartayi shuru snn ya rakata k'ofar gidansu tashiga tana waiwayarsa tana hawaye,shima bayan shigarta duk'ewa yai a gurin yn kuka daga baya yatashi yana addu'ar Allah yasa hkn shinee mafi alkhairi

 

(Gaskiya na jinjinawa Sayyeed damon samun kamarsa a cikin samarin zamanin nan da kamar wuya idan da wani ne sai yabata shawarar da bata daceba ko kuma yace su gudu Allah Ya k'ara shirya mana matasanmu abin ya Allah),

 

Tana shiga a farlour taci karo da Babanta zai fito yana ganinta yace"Yauwa Nutailah kije uwarki zata sanar miki da komai ko kiso ko kik'i dole ne sai anyi,ya fita yana faman banbamin fad'a,

 

Bin bayansa tayi da kallo hawaye masu zafi nabin kuncinta,Allah bai bata mahaifi na gari ba,da sauri tace"Allah na tuba Allah ka shiryamin mahaifina,Innah ta kalleta zatayi mgn Nutailah ta rigata dacewa"naji komai Innah kuma na amince tunda bani da yarda zanyi Allah yasa SANADIN hanyar Alkhairina kenan Allah yasa SANADIN shiryuwar mahaifina kenan zan masa biyayya Innah,na fad'a tare da wucewa d'akina ina kuka sosai,bina tayi da kallo cike da tausayina ita kanta hawayen take,

 

 

 

"Mum me kikeson sanar dani JB zaiyi aure kuma Nutailah zai aura yarinyar da uwarta ke mana wankau,Beenafah ta fad'a cike da rud'u da tashin hnkl,Mum tace"ki natsu ki kwantar da hnklnki kiji me zance,Beenafah tace"Mum taya hnklna zai kwanta byn JB zai auri wata bani ba,ada ina k'aunar yyarinyar nan Nutailah amma a yau Natseneta mum natsaneta wllh bana k'aunarta tunda kuma ta shugo gonata sai na zame mata SANADIN dasai tayi da nasanin sanin JB bama auransa datayi ba,

 

Murmushi Mum ta saki tace"sai yanzu na tabbatar kin tsotsi nono na ne da danake ganinki sanyi sanyi sai nake tunanin ko cenji akamin dana haifeki,tabbas sai mun zamewa Nutailah k'adangaran bakin tulu,barni da kwad'ayayyon wllh sainayi mgninsu,

 

Beenafah tace"daga yau nima na zama mara mutumci wllh zan iysyin komai akan JB da dukiyarsa,gaba d'aya suka saka dry mum tace"ko wata biyu baza'ayi da auranba zai aureki ita kanta yarinyar dole muga bayanta,Beenafah tace"wnn hk yake,nan suka dunga shirya makircinsu,

 

Kimanin makonni Uku kenan da saka ranar Nutailah da Jb har zuwa lokacin baije ba shifa har lokacin baisan ma wacece zai aura ba,ba wanda ya sanarwa a ckn abokansa don yasan dry zasu masa musamman Kb da yasan komai gami dashi akan rashin son aure yanxu,shi dayace nan da shekaru goma masu xuwa baijin zai iya aure sai gashi kwatsam au za'a masa aure tsaki yaja a karo naba adadi,wayarsa ce yaji tana k'ara yana dubawa yaga My Dad,d'auka yayi yana turo baki kamar wani k'aramin yaro"Hallo Dad,ya fad'a cikin kasalalliyar murya,

 

Dad yace"kana inane,"ehna gida Dad,to ganinan a hanya kashirya kafin inzo zamuje wani guri kayi fa shiri sosai,zan tambayesa inda zasu ya kashe wayar,

 

Dole badon ransa na soba ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda milk,wow zo kuka kyau gsky Jb kyakkyawa ne samun kamarsa sai antona,ya gama shirinsa yana wani ciccijewa don shi bai cika saka manyan kaya ba kuma yanadasu bila adadin yasan idan yasa k'ananun kaya tunda tare zasu fita da Dad to zaice ya cenxa ne shiyasa yasaka manya,

 

Ko da yashigo farlour kallonsa kawai Beenafah keyi bakinta ya kasa shuru saida tace"wow yayanah kayi kyau don Allah tsaya na maka pic,wata jrin harara ya banka mata tare dajan tsaki ya fice,ji take kamar ta jawosa jikinta ga wani had'ad'd'an k'amshi dake tashi jikinsa,har lok'ensa take ta window,

 

Dad ne ya iso,murmushi yayi ganin yadda tilon d'an nasa yayi kyau aransa yace"tabalakallah masha Allah,

 

Snn yace"kayi kyau d'ana,d'an murmushin yak'e yayi domin tunda akace za'a masa auran nan ko mrmshn baiso yayi,Dad yace"daman tunda naga bakason zuwa gurin surukar tawa nace yau kashirya saina rakaka,da sauri JB ya kalli Dad tabbas Dad yanason yrnyr nan sosai yace"no Dad kamin kwatance sai naje,kama hannunsa kawai yayi suka nufi gate,suka fita,ganin sun nufi gidan dake kusa da nasu yace"Dad yanaga zamu shiga nan byn ba kowa aciki,murmushi Dad yayi yace"ban sanar da kai komaiba don naga hnklinka baya jikinka tunda kaji batun nan,nan ne gidan surukanka kuma kyauta na mallakawa iyayen matar dazaka aura nan da sati guda,

 

Da sauri ya kallesa lallai ya karya Dad na kaunar mutanan,a bakin gate yabarsa yace"JB don Allah kashiga kar kabani kunya nasanar da iyayen yrnyr yau zakazo,Dad na gama fad'a ya juya gida shi kuma Jb ya tura kansa ckn gidan cike da gadara,

 

 

 

Tofa idan JB ya shiga yaga wacece zai aura ya zata kasance🤣🤣,

 

Sai kunbiyoni,banyarda aturawa kowa ba wnn littafin na kud'i ne duk meso yanemeni ni Ummu Affan domin amana ne a gurinku

 

 

 

Ummu Affan

4/10/20, 12:44 PM - +234 902 070 1465: 💖💖💖💖💖💖💖💖

  *KAINE!SANADII*

💘💘💘💘💘💘💘💘*

 

 

*Story and written by*

*Fateemah Sunusi* *Rabee'u*

*Ummu Affan*

 

________________________________

 

 

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*

_________________________________

*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*

_________________________________

https://www.facebook.com/104534761033461/posts

arewawritersassociation@gmail.com

 

 

Litafin nan na kud'i ne banyarda atura min shiba meso ya nemeni 08104335144

 

 

Bismillahir rahmanir rahim

 

🅿�23-24

 

Cike da gadara yake k'ara kutsa kansa cikin gidan A harabar gidan sukayi kici6is da Baba nan fa ya fara washe baki"Jabeer ka iso sannu da zuwa zo muje na maka jagora,Baba yayi gaba cike da mamaki JB ke bin bayansa tunani yake ina yasan mutumin nan amma ya kasa tunowa,farlourn bak'i na musamman ya kaisa ya washe baki kamar gonar auduga,"zauna yaron albarka,bai zauna ba kallonsa kawai yake aransa yace "ma kwad'aici zanyi maganinka ne,

 

Ganin baida niyyar zama yace"to bari na kira maka ita,ya fita da sauri,kallon farlour kawai yake ko ina fes,snn ya mayar da kallonsa ga k'ofa wacce zata shugo kawai yake jira,

 

Acen ciki kuwa Baba ya isje Nutailah wacce ke ta faman kuka tunda aka sanar mata yau JB zaizo hnklinta yatashi kuka kawai take da k'yar Innah tasatayi wanka,tunda ta zira doguwar rigarta ta jube kan gadonta tana kuka,

 

Shugowar Babanta yasa ta mik'e da sauri tana kallonsa,harara ya zuba mata"to a sararriya wllh idan kikace kuka zakiyi tayi hawayenki ya k'are a hakan ki tashi muje yazo,

 

Da sauri ta dafe girjinta tana zazzare idanuwa harga Allah ita tsoronma had'uwarta dashi take,yace"kin zubamin ido ki wuce muje nace,hijabinta ta jawo tayi gaba yana binta a baya,Innah tace"ki d'au ruwa da lemu a tire gasucen na had'a miki,hannu tasa ta d'auka,Innah tabi d'iyar tata da kallon tausayi,

 

Saida sukaje k'ofar farlour snn Baban ya wuce,kasa shiga tayi hawaye nabin kuncinta,saida tayi kusan minti 20 snn tayi kundun balar shiga,

 

Har lokacin yana nan tsaye hannayensa zube ckn aljihun wandonsa yana kallon k'ofar,kanta k'asa ta shugo,bai gane ko wacece ba saida ta ajiye tiren dake hannunta ta d'ago"ina wuni,da sauri kuwa ya juyo jin muryar yarinyar da bazai ta6a mancewa ba,domin har zuwa yanxu maganganunta na masa yawo akai

 

 _K'ud'inka na banza to meye amfaninsu tunda ba'abidasu ta hanyarda ta daceba ni udinka basa gabana_

 

Zuba mata ido yayi kafin ya mik'e yana sakar mata wani shu'umin murmushi yace"daman kece?ya d'an soya gefen sajensa yace"uhmmm lallai kuwa nayi frn ck da wnn had'in kodon innuna miki kud'in nawa sun isa ga alama nan tun farko da k'ud'in aka saye ubanki ya bani keee�,

 

A cikin tsananin fusata ta mik'e ckn hawaye tace"ko mai zakamin ya tsaya kaina kawai,karka saka iyayena,Kauuu kauuuu fasss fassss kakeji ya kwasa mata mari har biyu saida ta juya ta jufe a gurin sbd tsabar rikicewa ga wasu taurari da ta dunga gani ta fashe da kuka mai rikitarwa,ta kowa yayi gabanta cike da k'asaita ya duk'a saitinta yace"duk ranar da ina fad'a kina fad'a wllh sai namiki wanda yafi nayau k'azama kawai sakarya 'YAR TALLAH ke idan banda Dad ya had'amu ko a hanya kin isa ki ganni kimin mgn me zanyi da 'yar tallah mtsuuuuw yaja dogon tsaki ya mik'e yayi kutubar da tiren da takawo masa har yakai k'ofa ya tsaya bai juyo ba yace"ki tanaji irin zaman hkr da k'uncin da zaki tsinci kanki a gidan JB Tundaga yau kisa aranki kin fara shiga kunci da taskona,ya bud'e k'ofar ya fita ya wani bankota,

 

 

K'amk'ame jikinta tayi a gurin ta dungule guri guda tana wani irin kuka na bak'in ciki da 6acin rai addu'a take Allah ya mata sassauci,

 

A hankali ta tashi ta tattara kayan tayi cikin gida,Baba da Innah suna zaune a farlour tana shugowa ya mik'e "badai kimasa rashin kunyarnan taki ba ko?don wllh yace kin masa wani abu sai kin gane,kuka ta saki Innah kuwa cewa tayi"me yafaru naga fuskarki tayi ja haka harda shatin yatsu,kunsan abunku ga farar mace,

 

Da sauri ta tashi ta shige d'aki tana kuka bayan tasaka key kan gado ta fad'a tasaki kukan bakin ciki,wanne irin uba ne wnn,

 

Innah zugum tayi tare da tagumi tana hawaye,yace"kudai kuka sani aure kuma babu fashi nan da sati guda,yayi ficewarsa,

 

D'akin Nutailah ta nufa amma ta buga tak'i bud'ewa sai ta wuce nata dakin alwala tayi tazo tana nafilfilo tanawa d'iyar tata addu'a,

 

 

 

Yau sauran kwana biyu bikin JB da Nutailah sosai Gidan Alhj Mukhtar ake shagalin miki,Mum ta bar komai a ranta ta nuna kamar babu komai sai hidindumu ake ita ta shirya komai,da kanta taje Dubai ta shiryowa Nutailah kayan lefe a kud'in da ta amsa hannun Dad batayi sankaiba tasan komai yadda yadace don batason duniya tazargeta da komai ckn taku take abunta,

 

Da'akai lefen sai yabawa suke yayin da mutanan unguwa sai tsegumi suke a kan Malam Habu yasayar da 'yarsa,Mama kuwa wato mmn Sayyeed ita ta d'auki d'awainiyar gyaran Nutailah ciki da wajenta domin ita d'in shuwa ce 'yar Maiduguri tasan komai fannin k'amshi da sonran kayanmu na mata,

 

Gidan Alhj Mukhtar cike yake da 'yan uwa da abokan arziki sai murnar suke da hidindimunsu komai cikin girma da dattako ake kukuwa bikin tilon d'ansa ake

 

Yau Juma'a ya kama bikin JB da Nutailah a babban masallaci alka taru inda aka d'aura auran JABEER MUKHTAR JB da NUTAILAH ABUBAKAR Akan sadaki dubu d'ari biyar,

 

 

Kumuje zuwa wayyo NUTAILAH yaudai ta zama matar JB ya kuke tunanin zaman nasu zai kasance uhmm😭😭Har na fara tausayin Nutailah,KAINE SANADI me zai farune da har yazama sanadin da kyau sauran tafiya😂

4/10/20, 12:44 PM - +234 902 070 1465: 💖💖💖💖💖💖💖💖

  *KAINE!SANADII*

💘💘💘💘💘💘💘💘*

 

 

*Story and written by*

*Fateemah Sunusi* *Rabee'u*

*Ummu Affan*

 

________________________________

 

 

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*

_________________________________

*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*

_________________________________

https://www.facebook.com/104534761033461/posts

arewawritersassociation@gmail.com

 

Bismillahir rahmanir rahim

 

🅿�25-26

 

Gidan su Nutailah ma cike yake da 'yan uwa da abokan arziki sai shagalin biki ake,Nutailah daman na gidan Maman Sayyeed tanaji ance an d'aura auran ta dun k'ule guri guda tana wani rukitaccen kuka,shi kenan ta faru ta k'are an daura mata auran JB,Mama ce ke faman rarrashinta amma takasayin shuru,

 

Sayyeed ranar yayi kuka sosai yana dawowa masallacin wajen d'aurin aure,kayansa ya had'a a akwati ya nufi Katsina suna da dangi acen,yace ko sati guda ne gara yaje yayi ko zcyrsa tayi sanyi iyayensa basu matsa masa ba suka masa ftn alkhairi,

 

Da kyar Nutailah tayi wanka saida Mama tasata agaba snn tayi aka shiryata cikin wata had'ad'd'iyar shadda da tasha aikin surfani wow daman Nutaailah tana da kyau hk na fad'a lokacin dana ganta,

 

Sosai Innahrta ta matafad'a hk ma Mama sun nuna mata auran kud'i ubanta ya mata sai tabi a hankali snn tawa mijinta biyayya,mota guda aka aiko aka d'auki Nutailah har cikn gidansu JB inda aka sake mata shiri cikin wani d'anyen material me tsada snn aka gabatar da liyafa a wani babban holl da Mum ta kama,

 

Abokan JB ba babu abinda suke masa sai tsiya,ya shak'a iya shak'a hakan yasa yamusu banza,KB yace"wllh aboki ganewa ne bakayi ba ai irin 'yan 17 ko 18 sunfi dad'in sha'ani yadda katafiyar dasu hk zasu taso dashi  a gidanka ni nan 'yar 15 ma zan aura yasin,dukansu suka saka dariya Awwal yace"mgnrka hk take KB to daman yaushe zaka d'auko 'yar jami'a tazo tadunga ganin kai baka isa da itaba ko tafi k'arfinka ai mu daman a 'yan secondry muke,suka kumasa dariya,

 

Mik'ewa JB yayi yace"bari na baku guri sai kuyi hirarku da hujja,don kun fara samin ciwon kai,dariya suka shek'e Kb yace"eh dole ka fad'i hk mana amma wlh zaka sani ne,sosa k'eya yayi yace"kanku kuma akeji,wayarsa ya ciro yana kiran buduwarsa Sakeenat wacce har yanxu yake son d'ana taronsa akanta,tana d'auka tace"JB manya idan aka kirraka baka d'auka,zaman bed ya zauna tare da lumshe idanuwansa muryar Sakeenat tasashi nishad'i don badai tsak'in murya ba,

 

Yace"idan kikaga ban d'auka ina wani uzurin ne yakike ya gida ya Aiki,tace"duk lfy pls JB kazo in ganka yau,manyan idanuwansa ya sake lumshewa yace"Sakeenat bani da lokaci amma idan zaki iya zuwa inda nake sai na miki kwatance,tace"inason ganinka dole nazo JB amma sai gobe don yanzu yamma tayi sosai,murmushin cin nasara yai yace"ok to ai badamuwa,

 

Haka suka d'an ta6a hira kasancewar shi bameson hayaniya bane yasa basu wani dad'e ba sukayi sllm,murmushi yayi yace"gobe zaki shugo hannu yarinya,Kb da yashugo yanxun yace"kaida kake ango kuma kake batun wata zata shugo hannu,tsaki yaja mtsuww "amma ba d'an rainin wayau da hnkl sama da kai Kabir ni kakecewa ango to ango a gurinwa,Kb yace"agurin Nutailah wllh kasaki ranka karkayi girman kai ka cuci kanka ka murji amarcinka kawai aboki,

 

Wata irin harara JB ya masa na baka da hankali yace"da wnn k'wailar yarinyar kakecewa wai naci amarci lallai baka da hankali kai bari kaji ko yarinyar nan ta amsa sunanta na cikakkiyar mace bazan iya wani abu da itaba don bata kaiba ni na wuce tsaranta balle wnn 'yar ficikar yrnyr,,mtsuww yaja tsaki,

 

 

KB da kallo kawai yake binsa da ya tuno yadda yaga Nutailah d'azun yrny kyakkyawa ga cika komai ta had'a amma Jb ke cewa hk,murmushi yayi yace"uhmm JB ina jiye maka nan gaba kazo kanawa yarinyar da ka raina 'yar murya akan ta soka,fulo JB ya wulla masa yace"amma ka cuceni na rasa wacce zanso sai wnn d'iyar makwad'ancin humm ai wllh na tanaji abinda zan mata bani ta wulak'anta ba harda gayarmin mgnr banxa humm,

 

Shidai KB sharesa yayi domin yasan dole nan gaba JB yaso Nutailah ko don sbd wasu abubuwa da take dasu da yasan JB nasonsu a jikin mace,

 

 

Wajen Takwas na dare aka kai Nutailah gidan JB dake Malali GRA fad'ar had'uwar gidan 6ata baki komai yaji duk aikin Dad ne gsky yayi k'ok'ari duk kud'in da Malam Habu yaci amma ko chokali yakasa siyawa Nutailah garama Innarta ta siyamata kayan kitchin masu kyau da tsada haka Mama ma tayi k'ok'ari sosai komai na kichin d'inta Innah da danginta ne suka mata kuma kaya masu kyau domin Innar ba laifi danginta sun mata musamman Yayarta dake aure Abuja tabata kud'i masu auki dasu ta had'a tawa Nutailah duk don dai a d'an fita kunya duk da Dad yace kar tayi amma tace sai tayi don gudun karwataran dangin miji suwa Nutailah gorin da aka kawota ko chokali babu,Shidai Babanta saidai shiriyar Allah amma Malam Habu yayi nisa bayajin kira,

 

Sosai Nutailah ke kuka,mutane sai yaba gidanta suke,Mama tasake mata fad'a sosai snn suka fita suka barta,kuka taci gaba dayi nan fa zazza6i me zafi ya rufeta jawo bargo tayi ta rufe jikinta tana rawar sanyi amma duk da hk bata dena kukanba,

 

Kuzo muje rakiyar ango d'aki,cewar Awwal,harara JB ya banka masa yace''Wllh duk wanda zai kama gabansa ya tafi gara ya wuce don ba d'an iskan dazai bini,dariya suka saka Kb yace"haba ango daga rakiyar dazamuyi,ganin abin nasu iskanci ne tashi yayi yazari key yayi ficewarsa a mota ya barsu,suma ganin hk kowa ya kama kansa,

 

Tuk'i kawai yake Allah-Allah ya ke ya isa gida don ya fara shukawa yarinyarcen rashin mutumcin da yatada nadar mata,

 

Koda ya isa d'akinta yanufa,har lokacin kuka take idanuwan nan nata sunyi luhu luhu sbd kuka ga zazza6i me zafin da ya rufeta,yana zuwa kuwa da ya wani funcikota sai gata k'asa wanwar kanta ya bugu da garo nan take tasaka wani rikitaccen kuka,

 

 

Kallonta yayi a wulak'ance kafin ya tako inda take yace"........

 

 

 

Ummu Affan kar kumanta banda turawa kowa littafin nan na kud'i ne meso ya nemeni 08104335144

 

Fateemah S Rabee'u

UMMU AFFAN

4/10/20, 12:44 PM - +234 902 070 1465: 💖💖💖💖💖💖💖💖

  *KAINE!SANADII*

💘💘💘💘💘💘💘💘*

 

 

*Story and written by*

*Fateemah Sunusi* *Rabee'u*

*Ummu Affan*

 

________________________________

 

 

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*

_________________________________

*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*

_________________________________

https://www.facebook.com/104534761033461/posts

arewawritersassociation@gmail.com

 

Bismillahir rahmanir rahim

 

🅿�27-28

 

 

Yace"ina son na sanar miki bawai kinzo gidan nan dan ki huta bane a'a kinzo ne don ki k'untata saikinyi da nasanin shugowa rayuwa ni bazan ranki bane na wuce ajin insoki har na iya zaman aure da ke,

 

Kuka sosai Nutailah take domin ta bugu iya buguwa ga zazza6in da take fama dashi cikin da kushasshiyar furya tace"kayi hkrr,mtsuww yaja tsaki ya fita d'akin bedroom nasa ya wuce bathroom ya fad'a yayi wanka kafin ya fito d'aure da tawul gaban merro ya tsaya ya shafa turarukansa snn ya zura wata doguwar rigar barci,k'aramin furig d'insa ya nufa,ya d'auko kwalbar giyarsa domin idan baishaba sai yaji zcyrsa na azalzalarsa sai yaja yakejin sauk'i,

 

Bayan ya gama sha nan take wani dogon barci ya kwashesa a saman bed,

 

...................................................

 

"Beenafah ya kamata ki kwantar da hankalinki aure dai tsakaninki da JB babu fashi,cikin takaici tace"Mum ni kad'ai nasan yadda zcyta ke min yanxu shikenan JB yanacen tare da wata zai kwana baniba wllh ji nake kamar na kashe Nutailah sbd k'inta da nake na tsaneta Mum ban k'aunarta,ya fashe da kuka,Mum ta fara buga bayanta cikin sigar rarrashi tace"gobe ne zamuje gurin bokan nan kuma tare dake zamu,kije ki kwanta ki kuma kwantar da hankalinki kisa aranki tamkar kin auri Jabeer ne,

 

Da haka ta lalla6ata har ta kwanta,snn itama ta nufi bedroom d'in Alhj,

 

...........................

 

Innah ce zaune kan sallaya wajen k'arfe biyun dare addu'a takewa 'yarda Nutailah Allah ya bata zaman lfy da mijinta yasamusu k'aunar junansu ita da mijinta ya karesu daga sharrin duk wani abunk'i,tun d'ayan dare take nafilfilo saida takai wajen hud'u snn ta zauna ta addu'o'i sai da aka kira sallar asuba tayi snn ta kwanta,

 

Jb na dawowa masallaci da wajen shidda na safe da 'yan mintoci,bedroom nata ya nufa,yana tura k'ofar ta bud'e domin ko tashi ta kasa balle ta rufe tananan inda yabarta tun jiya ko barci ta kasa rawar sanyi kawai take jikinta na rawa sosai,

 

Tsawa ya daka mata amma ko k'wak'k'waran motsi ta kasa,ganin yadda jikinta ke rawa ya matsa kusa da ita "ke lfy ya tambayeta cikin tsawa,ko mgn ta kasa sai rawar baki da take,k'aramin tsaki yaja,kafin ya funcikota sai gashi ta fad'o jikinsa lagob,

 

Zai wuntsilata ta fad'i,amma yadda yaji jikinta zafi rau kamar garwashi yasashi tallanbarta ya kwantar da ita kan gado,

 

Fita yayi ya kira likitan gidansu awaya yashaida masa yazo gidanshi,wajen minti talatin sai gashi,har d'akinta ya rakashi,ganin yadda hak'oranta ke had'ewa suna wani kaf kaf,likitan yayi saurin k'arasawa ya fara aikinsa akanta,

 

Zuwa cen ya kalli JB yace"yarinyar nan tunani ya mata yawa da yawan kuka shi ya haifar mata da wnn zazza6i me zafin,yanzu dai kasamar mata abinda zataci ko tasha snn tasha magani insha Allahu zata sami sauk'i domin jininta ya hau sosai tana buk'atar barci da hutu,

 

Tare suka fita da likitan har yana masa tsiyar sayake ko an gurji amarci ne da yaji ya kirasa,sosa k'eya kawai yayi baice komai ba domin yana ganin girman likitan tun yana yaro shine likitansu,

 

Yana had'a mata ruwan tea yana jan tsaki da hk ya gama ya kai mata kasa sha tayi harara ya ban kamata yace"zakisha ko sai nashiga jikinki da bulala,sbd yadda take tsoran jb yasa tasha kusan rabin ganin zatayi amai yace tabarshi hk mgni ya mik'a mata hawaye ta fara don batason magani,tsaki yaja yace"kina 6atamin lokaci fa,

 

Haka ta sha maganin nan kuwa barci ya kawosheta,tsaki yaja yabar mata d'akin yana cewa haka kawai an had'aka da aiki daman farar mace me ta iya sai shegiyar kasala da saurin ciwo mtsuuuw yaja tsaki,

 

Lokacin da ta farko sasoi taji sauk'in jikinta don haka bathroom ta fad'a tayi wankanta tazo ta shirya ckn atamfa riga da siket tayi kyau sosai duk da fuskarta tayi fayau kuma babu kwalliya amma tayi kyau,

 

Farlour ta fito,yana zaune yana faman aiki a computer kallo daya ya mata ya kauda fuska k'asa ta duka ta gaishesa bai amsa ba sake gaishesa tayi,

 

Yace"kai yasa nifa ba k'aramin cutata akaiba wai dolena sai na amsa kina ganin aiki nake mtsuuw yaja tsaki,wayarsa ce tayi k'ara kallo wayar yayi kafin ya saki mrmsh,

 

D'auka yayi"Sakeenat 'yan mata,murmushi tayi tace"ganinan zuwa fa gidan naka,da sauri yace"da gaske,tace"yes da gaske mana yace"ok sai kin iso,ya katse kiran,kallon Nutailah yayi ckn daure fuska yace"ki shiga kitchin ki had'awa bakuwata abinci saurian kimin shirme kema kiga shirme,ya tashi ya tattara takardunsa yayi sama,binsa tayi da kallo kafin ta girgiza kai kawai ta nufi kichin,

 

 

Ummu Affan littafin nan na kud'i ne08104335144

4/10/20, 12:44 PM - +234 902 070 1465: 💖💖💖💖💖💖💖💖

  *KAINE!SANADII*

💘💘💘💘💘💘💘💘*

 

 

*Story and written by*

*Fateemah Sunusi* *Rabee'u*

*Ummu Affan*

 

________________________________

 

 

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*

_________________________________

*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*

_________________________________

https://www.facebook.com/104534761033461/posts

arewawritersassociation@gmail.com

 

Bismillahir rahmanir rahim

 

🅿�29-30

 

 

Komai na buk'ata a kwai hakan yasa ta fara aikinta Farar taliya tayi sai miyar stew da taji naman rago,snn ta had'a juice na cocnut da Zuma,tana ckn aikin bakuwar Jb ta iso kiransa a waya tayi yaje ya shugo da ita,

 

Daidai Nutailah ta fito zata jera kayan akan dinning suka shugo,kallonsa Sakeenat tayi ckn tuhuma,"wacece wnn,ta fad'a cikin kishi,

 

Harara ya wurgawa Nutailah yace"bazaki gaisheta bane,kallonta tayi"ina wuni,bata amsa ba taci gaba da harararta tace"JB wai wacece itaï¼?,kama hannunta yayi yace"yar aikina ce fa bakiga abinda take ba,

 

Cike da rashin yarda tace"yar aiki kuma jibirta fa tsaf wnn kyakkyawar yarinyarce 'yar aiki,janyo Sakeenat yayi jikinsa yace"pls baby mance da ita 'yar aiki ce,da haka suka wuce ciki bayan ya d'aya Sakeenat sama sukayi sama a haka,

 

Wasu hawaye ne suka gangaro kan fuskar Nutailah,byn ta gama jera komai ta d'ibi wanda zataci tayi bedroom nata,tasa abincin gaba tayi takasa ci sai kuka,yah Sayyeed ne ya fad'o mata tace"Allah sarki yayanah ko yanza yana ina nasan dakai na aura bazaka ta6a wulak'anta ni irin haka ba,

 

Da k'yar taci kad'an ta mayar kichin,har lokacin basu fito ba,ko motsinsu ma bakaji,kallon k'ofar room d'insa tayi tare da girgiza kai a fili ta furta Allah ya shiryaku,

 

************

 

Mum ce da Beenafah zaune gurin bokansu,shi kuwa bokon babu kyawun gani,yanayin shigarsa zuwa halittarsa gashinan dai wani iri sai k'atuwar murya da k'aton jiki cikinsa sai ka d'auka ckn mace me ckn wata tara ce,

 

6a66aka dariya yayi byn ya gama jin baya nansu snn ya kallesu da kwalakwalan idanuwansa yace"zata auresa amma sai tayi wani sharid'i guda d'aya,

 

Da sauri suka had'a baki wajen cewa meye wnn sharad'in,kallonsu yayi yana zazzaro idanuwa yace"zan baku wani magani,wanda zakiyi sarki dashi snn ki je Jabeer ya kusance ki wnn ne kad'ai zaisa ya aureki domin maganin zai shiga ta jikinsa,

 

Mum tace"ba wani kalan aikin sai wnn,yace"shi kad'ai ne zaisa ya aureta,ya mik'a musu maganin,godiya suka masa suka biyasa snn suka kama hanya,

 

Mum tace"gaskiya wnn aikin yayi tsauri da yawa banso ki lalata rayuwarki Beenafah tun kafin ayi aure zaice wani ya kusanceki,

 

Murmushi Beenafah tayi tace"mum karkiji komai indai zai aureni wnn badamuwa bace,ajiyar numfashi kawai mum tayi snn suka ci gaba da tafiya don ckn dajine saida sukaxo titi snn suka dau motarsu sukayo gida,

 

..............................

 

 

 

K'ishi Nutailah taji tanaji fitowa tayi domin ta d'au ruwa a furish,,bayan ta d'auka ta juyo hannunta d'auke da cup zata tsiyaya,abinda ta gani yasata sakin cup d'in da ruwan ji kake kwatsatsa kofin ya fashe daman gilash cup ne,

 

Su d'umma dake cikin wani hali tare suka juyo,harara JB ya zuba mata kafin ya sauke Sakeenat yazo gurin da take tsaye,wani wawan mari ya kifa mata a kid'ime ta kallesa tare da dafen gurin nata hawaye,

 

Kallon raini ya mata yace"gidan ubanki akwai kamarsa ne?to ki tsincesa da kyau kuma saikin biyasa dak'ik'iya jahila 'yar kauye meye kika gani da hankalinki zai tashi haka,

 

Sosai Nutailah ke kuka,Sakeent dariya tayi wacce daga ita sai bes jikinta tace"da kyau ai irin wad'an nan 'yan aikin sai ana musu haka,d'aukar Sakeenat yayi suka nufi ciki yace"kafin mu futo ki tabbatar babu komai a gurin nan,

 

 

Ummu Affan littafin nan na kud'i ne 08104335144

4/10/20, 12:44 PM - +234 902 070 1465: 💖💖💖💖💖💖💖💖

  *KAINE!SANADII*

💘💘💘💘💘💘💘💘*


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "KAINE SANADI page 21 to 30"

Post a comment