Results

KAINE SANADI page 41 to 50 End


*Ummu Affan*

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim
      
🅿�41-42

Hawaye kawai ke zubar masa yana tunanin me yasa ya aikata hakan me ma yasa ya mayar da rayuwarsa haka,

Abinda ya faru,Daman sabon bokanta yasanar da ita karta kashe Daddy ta bari sai an fara kawar da JB snn adawo kan Dad,tana dawowa gida k'awar ta kawo mata ziyara nan k'awar ta bata wnn mgni tace datasawa Alhj ko JB a abinsha yasha to shikenan saidai wasu basu ba,hakan yasa ta mance da mgnr bokan ai kuwa Alhj na rasuwa komai nakan JB ya sauka,turan aljanun da aka masa suka fita jikinsa SANADIYYAR sumansa kenan,tundaga lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa daman duk wani abu da yake to bashi bane aljanin nan ke komai da yakeyi,hakan yasa ya dawo shuru yaji mutuwar mahaifinsa da kuma rayuwarsa da yake jinta tamkar mafarki yayi,

Snn bayan fitar Beenafah ashe mai gadi yabi bayanta yana ganin abinda ta bunne ai kuwa tana fita ya bisu ya tone,,yana ta Allah wadai da wnn abin cuta da tayi niyyar wa mutanan gidan,

Kb ne ya dafa abokinsa JB yace"lallai kayi babban rashi Jabeer amma wnn shurun naka yayi yawa karka jawowa kanka wata cutar,kallon Kabir yayi yace"wai in tambayeka sai naga kamar Daddy yayimin aure koï¼?,

Cike da mamaki ya ke kallonsa yace"wnn wacce irin tambayar renin hnkl ce JB bayan da kanka ka d'auki d'iyar mutane kabawa su Munnir,da sauri ya mik'e a gigice yace"wai daman da gaske ne ba mafarki nake ba,

Abin na JB ya fara bawa KB mamaki yace"JB wai lfyrka kuwa,sai kawai yaga JB yasaka kuka yace"wllh Kabir bansan meke faruwa dani ba tun ranar da Dad ya rasu nakejina wani iri kamar sabo,ban san meyasa ba,

Kama hannunsa KB yayi yasashi a moto shima ya shiga bai kaishi ko inaba sai gidansu kasancewar mahaifin Kabir babban malamin addini ne d'an malam ne kafi halin malam,

Haka yawa Mahaifinsa bayanin abinDA Jabeer yace"snn ya d'aura da cewa"Baba na dad'e ina zargin kamar mum tana masa wani abu bazan mance ba kwanakin baya ta sameni akan tanaso mu had'a baki domin ganin bayan JB to nidai nak'i amincewa inda har wa'azi na mata tak'i snn ana kwana uku Daddy za rasu tasake min mgn akan tanaso mu had'a baki mu d'auke matar JB Nutailah nan ma nak'i yarda na dunga mata nasiha daga k'arshe zagina tayi tayi wai banason na k'aru sbd mak'udan kud'in da tace zata bani,nasan ta had'a baki ne dasu Munnir domin a d'auke maka mata,

Hawaye kawai Jb ke fitarwa anan ne KB ya sanar musu duk irin rayuwar da JB yayi shaye-shayensa zuwa neman matansa da yadda ya tsani aiki a office da kuma wulak'ancin da yawa Nutailah,

Sosai jikin JB yayi sanyi jin irin mummunar rayuwar da yayi wllh duk abinda ya faru bai saniba yace ckn hawaye"Baba duk wnn abinda ya farun wllh bansan ya akayi duk nayi suba shiyasa tun ranar da akayi mutuwar nan nake jina wani iri,


Malam Baba yace"tabbas a kwai wani babban sihiri da aka maka wanda yasa aka maka turen wani aljani duk ya gabatar da abinda ya faru,addu'a itace bakamin mumini idan harda sa hannun su mummyn taka to asiri na gab da tunowa domin tunda na jikinka ya karye,

Wasu manyan addu'o'i ya basa na karantawa yace yaje yayi tayi snn ya basa nasha da na kariya da tsari yace yasha,ya d'aura da cewa "karka nuna musu hankalinka ya dawo kabisu a yadda sukazo maka zaka gano komai yanxu abinda ya kamata ka fara ceto rayuwar matarka daga hannun wad'ancen 6ata garin,gdy sosai JB ya masa snn suka bar gidan,

.......................................

Munnir ne yasami shiga gurin Nutailah lokacin ta idar da sallah kenan sam ta mance bata rufe k'ofar ba kimanin kwanakinta uku kenan a gidan baci basha ta yi wani iri duk ta galabaita domin bata bud'e k'ofar balle ta amshi abincin da suke mata magiyar ta amsa,kullum ckn sallah take tana kai kukanta gurin me duka,

Ta tsorata da ganinsa baya ta farayi ckn hawaye shima yana binta yana dry da lasar baki yace"yaudai k'arshen alewa k'asa ta faru ta k'are wllh yau sai nayi duk wani abu danayi niyyaryi da ke,

Kuka take tana basa hkr domin duka k'arfinta ya k'are tana kaiwa jikin garo ya cimmata tare da fincikota jikinsa,ya fara k'ok'ari fatattaka kayan jikinta.......Littafin nan na kud'i ne banyarda kowa ya fitarmin da shiba na rok'eku,

08104335144Fateemah S Rabee'u
UMMU AFFAN CE
4/10/20, 12:44 PM - +234 902 070 1465: 💖💖💖💖💖💖💖💖
  *KAINE!SANADII*
💘💘💘💘💘💘💘💘*


*Story and written by*
*Fateemah Sunusi* *Rabee'u*
*Ummu Affan*

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

🅿�43-44Sosai ya faracin nasarar cire mata kaya cizo da yakushi kuwa yasha su,amma sbd tsabar k'arfi hali yak'i sakinta,daman kuma ance k'arfin mace da namiji ba d'aya ba,har ya kaita k'asa yana k'ok'arin haike mata,wayarsa ta fara k'ara tsaki yaja ba tare da yabi takan wayarba,kira har wajen biyar,wani dogon tsaki yaja ya saki Nutailah wacce tsabar kuka har ta kusan suk'ewa,


D'aga kiran yai zai fara masifa yaji muryar Awwal nacewa,"tun wuri kayi ta kanka ga JB da KB nan a hanyar zuwa gidanka,ai a furgice ya cilla wayar aljihu zuwa yayi ya d'aga Nutailah ya kinkimeta ya fita a guje,mota ya cillata shima ya shige ya figi motar a guje daidai fitarsa gate su JB suka iso yana ganinsu ya k'ara gudun motar cikin zafin nama JB yabi bayansa,


Abinda ya faru,Awwal suka gani,JB ya damk'e wuyansa don yasan tare suke da Munnir yace ko ya fad'a masa inda Munnir yakai masa mata ko ya kashesa shine yaji tsoro yasanar masa byn wutowarsu shi kuma ya kira Munnir ya sanar masa,

Sosai suke gudu a titin donma sunci sa'a babu motoci kasancewar titin ckn unguwa ne,haka suka dunga tsare a titi,koda suka iso babban titi Munnir bai saurara ba hk suka dunga gudu,shima JB ckn zafin nama yake binsa domin burinsa ya sha gaban Munnir amma da yake shima Munnir d'an duniya ne k'ara gudu yake yana kaucewa JB,


Tuni Kb ya fara tsorata yace "don Allah JB karka kashemu fa,cikin dakakkiyar murya yace"a yanxu bana tsoron mutuwa burina na kama munnir ya bani matata,


Haka suka dunga gudu duk inda suka wuce sai bakin mutane yayi mgn wasu suce anya lfy wasu suce duk yadda akayi na gabancen ne bashi da gaskiya wasu suyi ta zage zage wasu kuma suce Allah ya tsare kunsan dai bakin mutane,wasuma d'auka sukayi ko film ake to amma babu 'yan d'auka,


Wani ne da ya lura da abinda ke faruwa musamman da ya hango JB yasansa sosai tare sukayi karatu a England,juyawa yayi da motarsa yayi yanke sai gashi yasha gaban Munnir,wani wawan burki munnir yaja memakon ya tsaya a'a sai yayi rubas zai kwana tsautsai ya gifta aikuwa sukayi karo da wata mota nan take motar Munnir ta wuntsila gashi kan gada suke ai kuwa suka fad'a motar na wuntsila wuntsilah,


A matuk'ar furgici JB da KB suka fito kai da duk al-ummar dake gurin"NUTAILAHHHHHH!!!!!!!Abinda bakin JB ya furta kenan akaga ya doshi gurin shima zai fad'a nan fa mutane sukayi kansa kuka yake yana fuzge jikinsa amma da yake mutanan da yawa hk sukaci k'arfinsa,


A gurin ya zufe gwiwarsa a k'asa ya saka wani rikitaccen kuka,


Shi kansa kukan yake,daga baya aka d'agasa suka nufi k'asan tuni masu temakon gaggawa sun iso,inda aka kwashi Munnir da Nutailah sai asibiti,dukans basusan wanda ke kansu ba,inda Allah ya temakama da suka fad'o sunyi cen gefe yayin da motar tayi gefe ta kama da wuta,Asibitin su Jb suka wuce wanda yazamo kamar wani kurma ba uhm ba uhmm uhmmm,


Sakamakon fad'owar da sukayi hakan yayi SANADIYYAR........Fateemah S Rabee'u
Ummu Affan
4/10/20, 12:44 PM - +234 902 070 1465: 💖💖💖💖💖💖💖💖
  *KAINE!SANADII*
💘💘💘💘💘💘💘💘*


*Story and written by*
*Fateemah Sunusi* *Rabee'u*
*Ummu Affan*

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


Littafin nan na kud'i ne banyarda kowa ya turamin,tamkar amana yake a gurinku,ga me so 100 kachal,08104335144Bismillahir rahmanir rahim🅿�45-46


SANADIYYAR da k'awarta guda ta dagar gaje domin likitoci sun tabbatar da k'afar bazata iya gyaruwa ba saidai a yanke domin ba k'aramin dagargajewa tayi ba,ga buguwar da tayi da ake tunanin da wuya ta iya dawowa ckn hayyacinta sbd kanta ya bugu sosai,Allah dai yayi anyi nasarar ceto rayuwarta tana numfashi😭,


Munnir kuwa an tabbatar da bazai ta6a iya moruwa ba,gashi shima yana numfashi amma yayi mummunar buguwa inda shi da wuyama duka k'afafunsa su muro,gashi bazai ta6a iya kusantar mace ba domin gaba d'aya komai nasa ya kwance ya bugu iya buguwa,


Lokacin da aka sanar dasu xubewa a gurin JB yayi yana wani irin rikitaccen kuka cewa yake wllh NI NE SANADI me yasa na aikata hakan yanxu gashi yarinyar mutane zata rasa k'afa me yasa namata wnn mummunar SANADIN da bazata ta6a mancewa da SANADI na ba,


KB shima kukan yake yace"tabbas JB KAINE!SANADI!mummunar SANADI kuwa saidai ka kwantar da hnklinka tunda kaima lokacin da kabadata ba ckn hnklinka kake ba,


JB bai dena kukaba,shima kansa idan za'a bashi gado a asibitin ya dace donshi kansa majinyaci ne,ganin abun na JB bana k'are bane dole yasa aka kamasa aka danna masa allurar barci snn aka samu natsuwa,


KB ya nufi gidansu Nutailah domin ya sanar da mahaifanta,


Daidai lokacin,Innah kuka take wiwi,domin dawowarta daga gidansu JB kenan inda ta sami Mum da Beenafah a farlour suna sake shirya yadda zasu d'auki ran JB da kuma Nutailah karaf a kunnan Innah da sauri ta shiga tana salati tace"abinda kuke shiryawa kenan to in Allah ya yarda mummunar manufarku kanku zata dawo kuma ku fitomin da 'ya domin tambayarta nazo ai abun ya dad'e yana bani mamaki ganin Nutailah ace surukinta ya rasu amma batazo ba snn imaso in tambaya ganin kema kina ckn alhinin rashin Alhj yasa na miki uxuri ashe ke abinda kike shiryawa kenan ko kin zaci bandamu da 'yata bane?to wllh ki fitomin da 'ya ko kuwa hukuma ce zata rabamu,


Sosai Mum tasa dariya tace"uhmmm Mero kenan hukuma ko to maza kije ki kiraminsu,kuma inason ki sani wllh 'yarki Nutailah sai naga bayanta tunda ta shugo gonata,Innah tace"ta Allah ba takiba kuma in Allah ya yarda mugun kaba'inki akanki xai dawo,


Innah ta fita da saurin tabar gidan shine fa tashiga gida tana kuka,Baba zai fito sukaci karo ganin halin da take yasa yabi bynta,"mero lfy ya tambayeta,ckn kuka ta sanar masa duk abinda ya faru,nan take jikin Baba yayi sanyi hawaye suka fara zubo masa yace"son abin duniya ga halin da yakaini na bayar da 'yata inda bai dace da ita ba,wllh Mero tuntuni na fara da nasanin auran nan danawa Nutailah inda ne dace da rayuwarta ba,yasaka kuka yace"yana da kyau iyaye mu rage son abin duniya da kai 'ya'yayenmu inda bai daceba,nasan halin yaron nan sarai amma nabi son zcy dason kud'i naba masa auran 'yata banyi wani bincike ba gashi matar ubansa nason neman rayuwarta,don Allah iyaye murage son abin duniya da hangen kammu a sama idan muka aurawa yaranmu 'ya'yan masu kud'i,


Duka suka saka kuka daidai shugowar,Sayyeed da KB domin Sayyeed yasama yasanar masa,shima ckn kuka suka shugo gidan,a furgice suka kallesu,Innah tace"Nutailah ta mutu ko?nasan abinda zaku sanar dani kenan,girgixa kai Sayyeed yayi inda suka musu bayanin koma,


K'asa Innah tayi da kanta hawaye na zuba ta kasa mgn ma,Baba ya fashe da kuka yace"duk abinda ya faru NINE SANADI da ban aura mata wnn yaron ba da hk bai sameta ba Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,me yasa na kasance ni meson kaina nasan NINE SANADI Nutailah ki yafemin na kasance a gareki ba uba ba nagari na cutar dake na cutar da mahaifiyarku ga babban laifina na guji mahaufata iyayena 'yan uwana dangina ahlina kai da duk wani abu nawa Allah natuba ka yafemin,yasaka kuka kamar wani karamin yaro sai su Sayyeed ne ke basa hkr,da haka suka wuce asibitin,Lallai Nutailah tana shan wuya,Iyayenta da suka ganta sunyi kuka kamar me sun xubda hawaye addu'a kawai suke mata,


JB tunda ya farko ya d'aura daga inda ya tsaya,kowa ya kallesa sai abin ya baka tausayi ya zama tamkar wani zautacce,d'akin da aka kwantar da Nutailah ya koma,ya zauna ya xuba mata ido yana hawaye tun likitocin na hanasa ganin yafi k'arfinsu dole suka rabu da shi,Innahrta ke jinyarta ita da JB to itadashi zance mana tunda sallah kawai ke fitar dashi baya fita,saidai Innah taje gida ta kwana shike kwana d'akin,


Ciwon na Nutailah ba k'arami bane domin JB yanaso idan ancire k'afar asamata tak'arfe,hakan yasa ma ya musu biza su hud'u suka tafi k'asar India domin a mata magani sosai,Shi Innah Nutailah sai abokinsa KB,Alhamdulillahi an samu nasarar cire k'afar Nutailah har anyi mata dashen wata,babbar sa'ar da suka samu tana farkowa da tunaninta ta farko,don K'ara ta saki tana salati da kiran Innarmu,wayyo zanmutu Innarmu kixo,
Tana ganin Innarta ta fara k'ok'arin tashi tana cewa Innah ki tafi dani don Allah kar wnn mugun ya illatar dani kar kuma ki mayar dani gidan JB,


JB dake gefe hawaye ne suka zubo masa,Innah ta k,ara ta rik'e Nutailah ta na godewa ALLAH da yadawo mata da 'yarta cikin hankalinta,Nutailah da taji abinda ya faru da ita kuka tasaka tana salati,JB da KB ne suka shugo tana ganinsu tasaka kuka tace"bana son ganinka na tsaneka Allah ya isa tsakanina dakai mugu azzalumi sai Allah yasakamin KAINE!SANADIN duk wani abu da ya faru da rayuwata KAINE!SANADIN k'umtata rayuwata KAINE!SANADIN wargaza rayuwata yanxu gashi kayimin babban SANADIN mayar dani musaka na tsaneka JB ban k'aunar koda ganinka ne Allah sai yasakamin,KAINE!SANADI"KAINE!SANADI�"KAINE!SANADI!Wllh KAINE!sANADIN duk wani abu da yafaru da rayuwata ALLAH YA ISA!!😭😭😭😭😭😭😭😭😭ta saki wani gigitaccen kuka.......Fateemah S Rabee'u
UMMU AFFAN
4/10/20, 12:44 PM - +234 902 070 1465: 💖💖💖💖💖💖💖💖
  *KAINE!SANADII*
💘💘💘💘💘💘💘💘*


*Story and written by*
*Fateemah Sunusi* *Rabee'u*
*Ummu Affan*

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


Littafin nan na kud'i ne ban amince kowa ya turamin ba,tamkar amana yake a gurinku ga me buk'ata 100 kachal,08104335144


Bismillahir rahmanir rahim

🅿�47-48A hankali JB ya k'araso gabanta tare da zube duka k'afafuwansa a k'asa ckn hawaye yace"duk nayarda da maganarki Nutailah amma inason ki sani wllh bayin kaina bane NINE SANADI amma bansan yarda akayi na aikata hakan ba,Nutailah kiyi hkr ki yafemin wllh yanzun kece a cikin raina da zcyta karki duba da abinda ya sameki nayi alk'awarin mutuwa ce kawai zata iya rabani dake da da halima sai ince mutuwarma ta d'aukemu rana d'aya lokaci d'aya Nutailah inason kisan ni JABEER MUKHTAR GATA ina sonki ina k'aunarki wllh kice za6in zcyta kuma ZA6IN MAHAIFINA Idan baki rayuwata tana ckn garari kimin duk hukuncin da zakimin amma karfa kice zaki rabu dani wllh bazan jure ba,


Cike da mamaki take kallon JB dake zube gabanta yana kuka yana rok'arta ta soshi,tabbas SHINE SANADIN abinda ya sameta amma daga Allah ne don tun ran gini tun ranar zane hawaye ne ke xuba a fuskarta,


Innah tace"Nutailah na sanki da tsiwa amma fa kina da sanyin hali da hakuri,kar ki kuma cewa JABEER Ne SANADIN abinda ya sameki daman cen haka Allah ya tsara miki kuma daman Allah bai gama halittar bawansa har sai ranar da bawan naan ya koma garesa inaso ki sawa zcyrki salama kiyi hkr da yadda rayuwa tazo miki ki yarda da k'addara ta alkhairi ko ta sharri,


Hawaye ke zubo mata ta kasa mgn haka KB yasanar musu duk abinda ya faru da JB akan bada saninsa yake komai ba,da yadda abin ya faru,Innah ta sanar musu yadda taji Mum da Beenafah na mgnr kashe JB da Nutailah,ita ma Nutailah ta sanar musu ganin Mum da Beenafah da tayi da abinda sukace,JB kuka kawai yake bai ta6a tunanin Mum zata masa hk ba lallai da zarar ya koma zai d'auki mummunan mataki akanta,


Nutailah har cikin ranta ta yafewa JB domin tasa aranta haka Allah ya k'addaro mata,shi kansa kullum ckn sadaka da addu'o'i yake domin neman yafiyar Allah akan laifikansa na baya,


Watansu biyar a India Nutailah taji sauk'i sosai sai abinda ba'a rasa ba tana tafiya da komai kai idan basani ma kayi ba baza kace ba k'afarta bace,Alhamdulillah hakan yasa suka karkato gida Nigeria da shi KB tuni ya dawo,Gidansu suka sauka wato gdn iyayenta,Baba yai murna da samuwar lfyr 'yarsa ya natsu,kamar bashi ba yanxu kasuwa ma yake zuwa yana sana'a,ya rok'i UMMA da Nutailah yafiya kuma sun yafe masa hakan yasa suka shirya zuwa k'auye harda JB,Sosai iyayen Baba suka amshemu inda ya nemi yafiyarsu ckn kuka da danasani sun amshi rok'onshi inda sukace daman basu rik'eshi ba kullum ckn addu'a suke masa,


Ma'u 'yarsu yayar Nutailah daman tuni aka mata aure yaranta biyu,tayi murna da ganin iyayenta da 'yan uwanta,nan JB yayi ta musu kyauta taban girma Satinsu guda suka dawo,


Ranar da suka dawo JB ya shiga gidansu da niyyar matakin da zaiwa mum,saidai yana shiga ya iske mum na burgima tana yaga kayan jikinta tana ihu,Beenafah sai kuka take tana rik'eta amma ina tafi k'arfinta Tana ganin JB ta nufesa tana dariya sosai tana tona duk irin abinda ta masa harda sanar masa ita ta kashe Dad,sosai hnklinsa ya tashi,hk ma Beenafah don bata ta6a sanin itace ta kashe saba,


Waje ta ruga tana ihu da tonawa kanta asiri,zubewa gurin yayi yana kuka Beenafah ta bita tana kiranta,haka mutanan unguwa suka taru suna jin abinda take fad'a"yeee yeee nice nan nawa Jabeer asiri nasa aka turo masa aljani wanda yake sarrafasa yana aikata alfasha da shayeshaye yeeee yeeee nice nan na kashe Alhj da hannu na yeeee yeee nice...nice....kai haka dai ta dunga tonawa kanta asiri tana 6a66aka dariyar hauka don ta zare duk abinda tayi ne yadawo kanta,Beenafah sai rufe mata baki rake amma tak'i shuru haka mutane suka dunga tsine mata suna ai bata ta,Haka mutane ke tazuwa yiwa JB jaje beda bakin mgn sai gyad'a kai,


Lokaci k'ank'ani ya fara dawo da martabarsa da ta mahaifinsa ya duk'ufa wajen ganin duk abinda mahaifinsa keyi yayi koma fiye da nasa,


Nan campanynsu yasake suna yasake bud'e wasu ya ja matasa jikinsa marasu aikinyi ya basu,sosai yake aiki komai shike gudanarwa tare da tallafin amininsa na gari KB sai kuma Sayyeed wanda ya kammala karatunsa nan take JB ya basa babban muk'ami a campanynsa,Lokaci k'ank'ani shima Sayyeed ya goge yayi arziki ya ginawa iyayensa babban gida shima ya gina wanda idan yayi aure zai xauna,


Dukansu su ukun sun had'a kansu JABEER KABIR SAYYEED sun zamo abokai sosai duk kansu da abu guda suke aiki,


JABEER ya bud'ewa Baban Nutailah babbar super market inda ya zuba masa abubuwan sayarwa snn yasamar masa masu aikin wajen,ya kuma gyara musu gida sunyi kyau kamar basuba ya mayar da Nutailah da Sadeeq makaranta me tsada,


Shekaru biyu kenan Nutailah ta kammala secondry nan take yane mar mata addimision a Kaduna University da yake abin na manya ne lokaci k'ank'ani ta fara d'aukar luctures a KASU,


Ta k'ara kyau komai nata yayi yadda akeso,kai bazaka ta6a kallonta kace bada k'afarta take aiki ba,Anyi bikin Kabir da wata k'anwarsa da akeson had'asa sai yanxu ya bada kai bori yahau sunsha bikin Kabir da matarsa Salma,Ganin karatun Nutailah ya fara nisa sosai yacewa su Baba yanason ta dawo gidansa,basu musaba inda INNARTA ta sake mata sabon shiri,haka Mama wacce zumincinsu yasake k'ullewa bayan sati guda da mgnr JABEER yazo ya d'auki matarsa suka wuce tambatsetssen gidansu.......
Wayyo Allah na gaji yasin typing akwai wahala loll😜,
ku biyoni Anjima insha Allahu domin jin k'arshen labarin,


Karku manta na kud'i ne ga kar a fitarmin dashi
08104335144Fateemah S Rabee'u
Ummu Affan
4/10/20, 12:44 PM - +234 902 070 1465: 💖💖💖💖💖💖💖💖
  *KAINE!SANADII*
💘💘💘💘💘💘💘💘*


*Story and written by*
*Fateemah Sunusi* *Rabee'u*
*Ummu Affan*

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


Littafin nan na kud'i ne ban amince kowa ya turamin shiba,tamkar amana yake a gurinku,ka duk meso sai yane meni,08104335144


🔚🔚🔚🔚🔚


Bismillahir rahmanir rahim

🅿�49-50


 Bayan sun koma gidansu,Nutailah taci gaba da karatunta shima aiyukansa sunsha masa kai ko wanne lokaci yana office dare nayi kuma da ya dawo a gajiye ne sai barci,Babu wani abu da ya ta6a shiga tsakaninsu baine metaba duk da yana buk'atarta haka ya rabuda ita sbd aiyukansa shi kansa yasan abin ya masa yawa duk da Kabir da Sayyeed suna temaka masa sosai,amma yanaso ne ya jajarce da aiyuka irin na Daddynsa,Alhamdulillah abubuwa na tafiya yadda ya dace,yana zaune office yake tunanin rayuwa hawaye ne kebin fuskarsa yana sake jaddada tubansa ga Allah,sakatariyarsa ce ta shugo take sanar dashi yana da bak'uwa yabata izinin tace ta shugo,ta fita zuwa cen akayi sallamamuryar wacce yaji yasashi saurin d'agowa tare da mik'ewa a furgice yana kollonta itama shi take kallo,kafin tasami guri ta xauna cikin hawaye tace"Jabeer baka ganeni ba ko,


Zaunawa yayi jikinsa a sanyaye yace"Sakeenat na ganeki mana,kuka take sosai tace"Jabeer naga rayuwa na cuci kaina da na biyewa son zcy na dunga aikata alfasha yanxu gashi,naga k'arshena likita ya tabbatarmin ina da cutar nan me karya garkuwar jiki HIV,Da sauri ya zaro ido shi kansa hawayen yake yace"Sakeenat ki yafemin nima hardani da na k'ara d'auraki a hanya,tace"Jabeer baka da laifi domin tun kafin masanka nake aikata xina daman kawai nazo ne katemakin da kud'in da zanyi mgni domin duniya ta juyamin baya bani da komai su kansu iyayena yanxu k'yarata suke,Kud'i sosai ya bata yace tayi magani yana k'ara bata hkr itama tana basa snn tace ya rok'ar mata Nutailah,byn tafiyarta jikin Jabeer ya kuma sanyi da duniyar nan addu'arsa kullum Allah ya yafe masa,Tunda ya dawo a farlour ya xufe yana mayar da numfashi Nutailah ce ta fito ckn doguwar riga bak'a jallabiya tayi kyau sosai k'arasowa tayi ganin yanayin da yake ruwa me sanyi ta kawo masa ya amsa yasha sosai zama tayi daga gefensa tana mrmsh tace"Don Allah Jabeer ka rage yawan aiyukan nan karka jazawa kamka wata cutar aiyukan da kake yayi yawa,numfashi yaja yace"nagode da kulawarki insha Allahu zan rage,nan yake bata labarin Sakeenat saida tayi hawaye tace na yafe mata,Beenafah ce ta shugo da gudu tana kuka sosai zubewa tayi jikin Nutailah a rud'e suke tambayarta me ya faru,ckn kuka tace"Mum ta rasu wayyo nashiga uku Mum ta mutu tayi mummunar mutuwa abin babu kyau ku temaka ku yafewa Mum ko taji dad'in kwanciyar kabari wllh da kyar aka sallaci sallarta sbd yadda take wari da d'oyi,


Dukansu saida sukayi hawaye tabbas hakkin rai babba ne mutum ya kashe mutum uhmmm Allah ya kyauta yasa masu hali irin na mum su cenxa,


Haka sukayi zaman makokin Mum babu wasu jama'a,


Bayan rasuwar mum da wata biyu,Beenafah ta samin Jabeer da Nutailah tace"Jabeer ka temakamin ka aureni kaga yanxu banda kowa daman mahaifina ya dad'e da rasuwa Nutailah ki tausayawa maraicina kisa Jabeer ya aureni,da sauri ya kalleta kafin ya gyara murya yace"Beenafah tabba ina tausaya miki amma kiyi hkr da wnn mgnr nayi alkawarin dai zan rik'eki a hannuna har Allah ya fito miki da miji na miki aure a yanxu Nitailah ce kawai a zcyta banajin xan iya mata kishiya,Kuka Beenafah ta saka tana bashi hkr,Nutailah ta tausayawa Beenafah har cikin ranta tace"don Allah Jabeer ka aureta idan tani ce karka damu wllh na amince kuma zan xauna da Beenafah tsakani da Allah,girgixa kai yai bazan iya ba,snn ya tashi,


Beenafah ttasaka kuka ta fad'a jikin Nutailah rarrashinta tayi tace tayi hkr zata shawo mata kansa,


Da daren ranar taje har d'akinsa ta sami guri gefensa ta zauna tace"don Allah kayi hkr ka aureta kaga yanxu tayi hnkl ta natsu ka tausaya mata don Allah,kollonta yayi yace"Nutailah baki sona ko nasan baki sona nine kawai nake haukana tunda gashi har zakice na iya auran wata,numfashi taja tace"ina sonka Jabeer wllh ina kaunarka saidai kaduba mgnta don Allah ka tausaya mata,"bazan iya auranya ba yace,hawaye ta fara tare da juya masa baya da sauri ya rungumeta ta baya yace"don Allah karkiyi kuka tayi alkhawarin bazakiyi kuka ta sila na ba,tace"to ka amince da auranta,yace"hakan xai saki frn ck,gyad'a kanta tayi yace"to na amince,da karfi gabanta ya buga akace kishi kumallon mata dole ne ko wacce mace tada dashi saidai wata tafi wata dannewa tayi tare dayin murmushi tace "nagode,Daga haka kuma hirar ta cenxa salo,inda suka lura duniyarsu ta ma'aurata,


Nutailah tasha wahala don wnn shine karon farko,Jabeer kuwa addu'a kawai yake saka mata ganin ta kawo masa budurcinta snn ya k'ara gode Allah da ya azurtashi da kimtsattsiyar mata,haka yadunga tarairayarta da dad'ad'an kalamai masu dad'i da kwantar da hankali tare sukayi wankansu,


Tun daga wnn rana komai ya cenxa salo inda sukaci gaba da kwan kwad'ar soyayyarsu,Jabeer yana son Nutailah sosai Allah ya mata wata baiwa dashi kad'ai yasan kayansa,Rana d'aya aka saka bikin Jabeer da Beenafah da kuma na Sayyeed wanda zai auri wata yarinya nan k'asan layinsu take Mariya tana da hnkl ga natsuwa sosai ta kammala secondry sbd iyayenta bamasu k'arfi bane bataci gaba ba,


Innah Da Baba sunyi murna dasukaji Jabeer zai auri Beenafah daman sunso suyi masa mgnr,inda suka had'esu duka ukun suka musu addu'a


Anyi bikin ckn kwanciyar hnkl da lumana inda duka amare suka tare gidajensu,sosai suke zaman lfy Beenafah da Nutailah inda suke kyautatawa junansu snn suke kyautatawa mijinsu kowa burinta taga tawa mijinta abinda yake so,tabbas dukansu yana jinsu aransa amma a ckn zcyrsa yafi son Nutailah domin ita d'in 'yar baiwa ce,amma bai nuna musu domin baison had'a hatsaniya a ckn matansa daman kuma dole ne daman idan kana da mata biyu ko sama da haka kaji wata ciki tafi kwanta maka,

......................................................


BAYAN SHEKARA GOMA
Zuwa lokacin had'in kai sosai ya shiga tsakanin familyn Nutailah wacce ta dad'e da kammala karatunta yanxu cikakkiyar lawyer ce yaranta hud'u,mai sunan Dad Mukhtar kenan wanda ake kira Daddy sai me sunan Babanta Abubakar wanda ake kira Sadeeq snn me sunan Kabir abokin Jabeer da ake kira Kb boy,sai autarta Me sunan Innarta Maryam da ake kira Ikhram,


Beenafah kuwa yaranta uku Hafsat ce babba sai me sunan Mmn Jabeer Halimatu ana kiranta Mamee sai autarta Ihsan duk mata ne nata,Alhamdulillah yaran sun had'a kansu suna k'aunar junansu bazakace ga yaran wacce ma sbd had'in kai kowa mahaifiyarsu suka d'auketa,

Kabir ma yaransa uku shi kuma Sayyeed nasa yaran biyu  ne mace da namiji,Sosai rayuwa ta musu dad'i komai na tafiya yadda yadace cike da nasarori Jabeer ya zama babban mutum arxik'insa d'ana bunk'asa yake su kansu matansa ya gina musu babbar masana'anta inda aka kina shagunguna banya aka xuba kayan sayarwa dangin atamfofo saddoji yaduka leshuka dogayen riguna takalma kai harda 'yan kunnaye ko wanne shago akwai abinda ake sayarwa,sun xuba ma'aika Sadeeq k'anin Nutailah ma ya kammala karatunsa da yake Doctor ne aiki bai masa wahalar samuba tunda yana da Yayansa Jabeer,

Su Innahh saidai muce masha Allah yanxu suna ckn jin dad'i komai ya wuce daman ance dukkan wani tsanani yana tare da sauki tabbas gashinan komai ya wuce kamar ba'ayi ba,suna yawan xuwa k'auyansu sosai,


BAYAN SHEKARA wata GOMAN

Daddy babban yaron Jabeer daka gansa kaga ubansa komai halinsu iri d'aya ne kamar yadda Jabeer yake kafin amasa asiri yaro ne me natsuwwa sosai yake kula da k'annansa baya son raini snn baya da wulak'anci shiyasa uban kesonsa sosai ko Office wani lokacin tare suke zuwa idan ba skul,


Suna hutu hakan yasa sukaje office tare da Abban nasu da yamma sun dawo daidai k'ofar farlourn bak'i suke jin nishi sama-sama,a hnkl suka k'arasa k'ofar a bud'e take hkn yasa suka shiga me zasu ganiï¼?,


Hafsat ce babbar d'iyar Beenafah tare da wani saurayinta suna alfasharsu hankalinsu kwance,cikin wani irin halin da keda wuyar fassara a gurin Jabeer ya zube cike da tashin hnkl nan take ya sume,


JIn fad'uwar mutum yadawo dasu daga duniyar da suke,Daddy yayi kansu dukan saurayin yake da kyar ya gudu,snn ya koma kan Hafsat saida ya mata dukan tsiya da gudu tayi cikin gida iyayen hankali tashe suka fito ckn kid'ima ganin Hafsat tsirara haihuwar uwarta,


Ruwa aka nema me sanyi aka samasa nan ya farfad'o yana kuka,kowa jikinsa yayi sanyi Beenafah kukan take Nutailah sai hkr take basu,Jabeer yave"ashe hk iyaye keji idan yaransu suka lalace tabbas Allah ya nunamin ishara ne domin nima naji yadda akeji da na lalata yaran mutane,D'aga hannu yake yana k'ara jaddada neman yafiya ga Allah da gode masa da ya nuna masa laifinsa tun a duniya,


Tundaga ranar Hafsat ta zamo ckn kuka da danasani daman bata ta6ayi ba sai ranar ta rok'i yafiyar iyayenta ta tuba,Shima Jabeer ya sake tuba snn yadunga sadaka domin a tayashi addu'a,Munnir kuwa bai mitu ba amma rayuwarsa tana cikin garari to koda ya warke baida kata6ussssssï¼?


Iyalan Alhj Jabeer kuwa da abokansa Kabir da Sayyed,
Sosai suke xamansu lfy da fahimtar juna,Alhamdulillah

ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN Allah na gode maka da kasa na kammala littafin nan lfy

Alkhairan dake cknsa Allah yasadamu dasu akansin dake ciki Allah ya yafemin,


Nagode gareku wad'anda suka sayi littafin nan musamman masu min sharri ina godiya


Bazan manta da ku ba

Yusuf Nuhu
Sa'a Preety
Asmy Jafar
Maryam
Kai dukanku ina godiya kar kuce ban kira sunanku ba don Allah kuyi hkr wllh na rigasu na kama sunandu ne,dukanku ina gdy Allah yabar zuminci,

Sai mun had'e a book d,ina me suna NAYI GUDUN GARA,

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "KAINE SANADI page 41 to 50 End"

Post a comment