Results

NAMIJIN GASKE littafi na biyu 2 part A


NAMIJIN GASKE
Littafina biyu 2
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
Part A
.
Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa
wannan labari ta
ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan
za'a kiyaye
Copyright
Shuraih Usman
.
.
Al'amarin muhaisin kuwa tun ranar da mahaifiyarsa ta sanar dashi labarin mahaifinsa ,sai yaji babu abin daya ke so ya aikata face ya je birnin tehran ya yaki sarki humaiz don ya dauki fansar abin da yayiwa mahaifinsa
.
Akullum baya aikin komai face tunani, da yadda zai bi yaje ya kashe sarki humaiz, amma daya tuna da mahaifiyarsa sai yaji sam ba zai iya yin tafiya mai nisa ya rabu da ita acikin wannan kungurmin daji ba'
.
Wata rana muhaisin na zaune yana ta tunani ransa sai harzuka yake,
Ji yayi hannu ya dafa kafadarsa koda ya juyo don yaga waye mai wannan hannun, sai yayi arba da mahaifiyarsa hamasiya,
.
Hamasiya tayi murmushi tace "yakai dana shin menene ke damunka , naga kwana biyu sam baka samun kwanciyar hankali tunda na sanar dakai labarin mahaifinka,"
Koda jin haka sai muhaisin ya yi wata murmushi na karfin hali yace" babu abin da ke damuna yake mahaifiyata,"
.
Hamasiya tai murmushi akaro na biyu sannan tace "muhaisin nasan abun da ke damunka ,kasani bana son ganinka acikin damuwa ko kadan bisa haka ne, lallai na baka umarni daka shirya katafi izuwa birnin tehran don ka dauko fansar abin da akai wa mahaifinka, sannan ka gaji sarautar mahaifinka, muddin hakan zai sanyaka farin ciki."
Muhaisin ya dubi mahaifiyarsa alokacin da kwalla ya zubo daga idanuwansa yace" tabbas ina muradin tafiya birnin tehran amma ya ummina kiyi sani cewa sam banason na barki acikin wannan jejin cikin maraici, bana son rabuwata dake, "
.
"Babu komai muhaisin lokacin da nake cikin bakin cikin rasuwar mahaifinka ma, na yi rayuwa a cikin wannan jeji balle kuma yanzu danake farinciki bisa ganin zaka je ka kashe makashin mahaifinka, lallai na yarda da jarumtarka, da kuma sadaukantakarka, zan kasance mai yimaka fatan alhairi, har lokacin da zaka dawo,"
.
Muhaisin najin haka yafada kan cinyar mahaifiyarsa ya fashe da kuka, sai kace wani karamin yaro
.
A washe garin ranar ne muhaisin yai sallama da mahaifiyarsa ,nan suka rabu tana hawaye shima yana hawaye nan kama hanya izuwa birnin tehran
.
Sai da ya shafe kwanaki biyu yana tafiya batare da ya yada zango ba , indai yaji yunwa sai ya fiddo da jakar guzurinsa ya dauko naman wannan damisar ya dan ci kadan,
,
A rana ta uku ne yana kan tafiya sai ya shigo wata Daji wacce ta kasance bishiyoyinta duk guntayene sannan kuma busassu,
A gaba daya kasan wannan jeji busassun ganyayyakin bishiyar nan ce mamaye da wajen
.
Hakan yasa duk inda muhaisin ya taka sai kaji wata irin kara ta fito,
Yana cikin tafiyar ne ransa a sake babu ko alamun damuwa,
Kawai sai ya jiyo muryoyin mutane na tashi Nisa da shi, nan yayi sauri don yaga su waye ke rayuwa acikin wannan kungurmin jejin,
,
Koda ya kariso gindin wata bishiya sai ya labe a bayanta sannan ya bude ganyayyakin bishiyar da hannunsa nan idanuwansa suka c karo da wasu ,
Manya manyan mutane, sun daure wani tsoho ajikin wata bishiya , sai gana masa azaba suke
Shiko wannan tsoho ko ma yasan sunayi ,
Abinda yabaiwa muhaisin mamaki da wannan tsohon kuwa shine a tsaye akansa akwai wani murgujejen kato shi wannan katon ya sanya wata karfe a cikin wuta , a duk sa'in da karfen tayi zafi tay ja, sai ya fidda karfen daga cikin wutannan sannan ya dorata bisa kirjin wannan tsohon ,maimakon wannan tsohon ya tsandara ihu sai dai kaga yana motsi da bakinsa,
Su wayannan mutanen a dadinsu sunkai Dari,
Sun zagaye wannan bishiya wasu a zazzaune wasu kuwa a tsastsaye .
Koda muhaisin yaga suna neman su hallaka wannan tsohon sai ya fito daga bayan bishiyar nan sannan ya tunkari wayannan samudawan mutanen masu kiran mutanen farko.
.
Koda suka hango muhaisin yana durfafosu, sai dukkaninsu suka mike tsaye , nan take kowannensu ya fiddo da makamansa nan suka tsaya suna jiran isowar muhaisin,
.
Muhaisin na karisowa wajen sai ya tsaya , tsakaninsa da wayannan samudawan baifi taku Goma ba ,
Koda ya kare musu kallo da kyau sai ya gane ko suwaye
.
Su wayannan kartin sun dade suna tarkon muhaisin bisa hanasu zalinci daya keyi, amma da sun hadu sai kaga sun ruga sunyi daji,
.
Kimanin dakiku biyar babu wanda yace kala tsakanin muhaisin da wayannan samudawan mutanen,
.
Wani gabjeje daga cikin samudawan wanda duk ya fisu girman jiki da kuma fadin kirji, ya matso gaban wayannan samudawan sannan ya bushe da dariya ,
Sai da yayi mai isarsa sannan ya tsuke baki ya kuma bata rai tamkar an aikomai da sakon mutuwarsa.
Wannan gabjejen katon ya dubi muhaisin duba na tsanaki sannan yace"yakai wannan bakon jarumi wanda ya addabi rayuwarmu, kayisani ako wani lokaci tarkonka muke, ta yadda zamu samu mu kamaka mui maka kisan gilla, sai gashi yau cikin sauki ka fado cikin komar mu ,"
.
Koda jin haka sai muhaisin ya turbune fuska sannan yace" yaku wayannan azzaluman kuyi sani cewa tun ba yau ba munsha haduwa da ku amma da zarar kun yi arba dani sai ku ruga izuwa cikin daji, amma wai sai gashi yau an wayi gari kuna furtawa cewa zaku tunkareni, shin me yasa tun abaya ba kwa tsayawa mu fafata aduk sa'adda muka gamu"
.
Koda jin wannan tambaya sai gaba dayan samudawan mutanen nan suka bushe da dariya suna masu kyakyatawa,
Can sai wannan gabjejen ya daga hannu sama alamar a dakata haka
.
Ai take kuwa wajen yai tsit tamkar wani abu mai rai bai kasance a wajen ba,
.
Gabjejen yace " Ba komai bane yasa kaga a duk lokacin da muka hadu , bama taba tsayawa muyi fada shine shugabanmu boka Abulzulmu, shine ya sanar damu cewa lokacin gamuwarmu da kai baiyi ba ko, amma da tuni mun dade da shafeka daga doron kasa, kuma kar kayi zaton wai ko gudunka da muke tsoronka mukeji, jada baya ba tsoro bane, gyaran taku ne."
.
Muhaisin yayi murmushi sannan ya dubi gabjejen katon yace " koma dai menene wannan ku tarage mawa,
Kuyi sani wannan fitowar danayi na fito ne don na kawar da zalunci da kuma Azzalumai, lallai ina mai sanar daku daku gaggauta kwance wannan tsoho da kuke gana mai azaba, tun kafin raina ya hassala"
.
Shugaban samudawan najin haka sai yadaga hannunsa yayi wa mutanensa alaman su afkawa muhaisin,
Nan take dukkan samudawannan wayanda adadinsu yakai dari suka falfalo da azababben gudu suna masu kurma ihu,
.
Muhaisin na ganin haka shima sai yayi wani irin kuwwa sannan ya falfala da masifaffen gudu don ya cimma wayannan samudawan,
,
Koda y rage baifi saura taku biyu ba tsakanin muhaisin da wayannan samudawan sai muhaisin ya daka wata salle yai sama take yaje tamkar an cillashi daga cikin baka ,
A saman ne ya gabje wani basamude da kafarsa akai take wannan basamuden ya fadi shirim,
Shiko muhaisin bai yarda ya kafafunsa sun taba kasa ba hak ya ringa yawo a sama ta hanyar gab gabje wayannan samudawan da kafafunsa a kayukansu,
Cikin kankanin lokaci ya bazar da mutane akalla ashirin, sannan yakai karkensu,
Koda yazo karken wayannan samudawan sai yayi wata irin alkafura sannan ya fadi bisa guiwowinsa,
,
Yana faduwarne wani ba samude ya kaimai sara da nufin ya cizge mai kai da takobin sa cikin zafin nama da salon iya yaki ya kauce wa saran take takobin ta sari iska, kafin basamuden ya kara kaimai wani saran ne ya kama hannunsa ya murde take hannun takarye, wukar dake jikin hannun basamuden ta fadi a kasa, kafin takobin ta taba kasa tuni har muhaisin ya cafe takobin, cikin wata irin salo
.
Nan fa muhaisin ya hau wayannan kartin da sara da suka ,
Nan fa salon fadan ta canja, duk da yake muhaisin bai taba rike takobi ba bare ma yayi fada da ita, amma in kaga yadda yake sarrafa takobinnan ai ko wannda yayi shekaru yana koyan yakin takobi bazai nuna masa wani abin ba.
.
Cikin yan dakiku ya kashe samada karti tamanin kwata kwata wayanda suka rage basufi su ashirin ba,
Koda yan tsirarun kartin nan suka ga muddin aka cigaba da wannnan gumurzun toh zasu iya rasa rayukansu , nan suka ruga izuwa cikin daji,
,
Nan fa filin ya rage babu kowa face muhaisin da shugaban kartinnan wanda tunda aka fara wannan gumurzu ko gezau bai yiba daga inda yake
.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "NAMIJIN GASKE littafi na biyu 2 part A"

Post a comment