Results

NAMIJIN GASKE littafi na biyu 2 part B


NAMIJIN GASKE
Littafina biyu 2
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
Part B
.
.
Koda shugaban kartinnan yayi duba gaba da bayansa ,babu abin da yake gani face mutanensa ,birjik bisa kasa wasu a sume wasu ko sai murkususu suke,
.
Nan da nan hankalinsa ya dugunzuma ,ransa ya baci nan ya kwarara uban ihu , wanda ya amsa a cikin dajin gaba dayansa , take dabbobi suka ringi gudu, suko tsuntsaye sai suka ringa canja sheka
,
Nan take wannan katon ya zare wata makami na bakin karfe a mararsa
Ita wannan makami ta kasance marikinta na bakin karfene wanda tsawonsa yakai kamu daya
Akan wannan marikin kuwa wani mulmulallen karfene mai fadi wanda girmansa yayi na giginya uku, a zagaye da mulmulallen karfen kuwa wasu irin allurai ne masu tsananin tsini da kuma kauri a kakkafe ajikin mulmulallen karfen
Daidai tsakanin mulmulallen karfen da marikinta kuwa wani sarka ne mai tsayi wanda tsawonsa ze kai kamu uku zuwa hudu
Shi wannan sarkar yana jikin marikin makamin ne, kuma baya fitowa fili face an dannan wani waje ajikin makamin
.
Nan take wannan katon ya nufo muhaisin rike a hannnunsa wannan makaminne, koda ya kariso gaban muhaisin sai ya kaimai duka da wannan makami, da nufin yaiwa kan muhaisin fashin kwakwa,
Cikin zafin nama muhaisin ya sanya takobinsa ya kare wannan duka,
Take takobinsa ta karye sannan alluran jikin makaminnan suka cakeshi a damtsensa
,
Cikin matukar galabaita muhaisin ya sanya kafafuwansa ya daki wannan katon da su a fuska
Duk da girma irin na wannan katon amma sai gashi saboda karfin dukan da muhaisin yamai sai da yayi sama sannan yayi baya tamkar an janyeshi da majaujawa,
Katon ya fadi akasa yana aman jini
.
Tsakanin muhaisin da katon kuwa taku dari ne
Muhaisin ya falfalo da gudu a yayin da babu komai ahannunsa
Koda wannan katon ya ga muhaisin ya durfafoshi, sai ya mike tsaye sannan shima ya falfala da azababben gudu don ya tarbi muhaisin
Koda ya rage baifi taku goma ba tsakaninsu sai wannan katon ya matsa wannan madanni na jikin makaminshi take wannan mulmulalleen karfen dake makamin ya rabu da makamin sannan ya nufo muhaisin
.
Koda muhaisin yai arba da wannan mulmulallen dutsen kuma yaga tana nufoshine da nufin ta hallakashi
Sai yayi sufa izuwa kasa take wannan mulmulallen karfen ta wuce ta samansa shiko sai yaje da guiwa yabi ta tsakiyar kafafuwan wannan katon, sannan ya bulla ta bayansa tun kafin katon ya juyo sai muhaisin ya sake daka tsalle akaro na biyu
Ya dirga a gaban wannan katon nan cikin zafin nama ya kirba ma katon naushi a fuska take katon ya kwala ihu sabida radadin wannan naushi daya ji
.
Kafin katon ya warwarene muhaisin ya kama hannunsa mai rike da wannan makami ya karya take katon ya sake kwala wata ihun wacce tafi na farko Amo da kuma sauti
.
Nan take makamin da ke rike a hannun ta fadi akasa
Cikin bakin zafin nama muhaisin ya dauki makamin sannan ya damfara wa wannan katon aka
Take kan katon ya dagargaje,
Nan take ganganjikin ta fadi kasa, dungulmin kan kuwa sai malalar da jini yake
.
Koda muhaisin yaga ya samu nasarar hallaka wayannan kattin sai yayi murmushi sannan ya dubi makamin shugaban kartin wanda take hannunsa , ya daga makamin sama sannan yace
"Daga yau wannan makami ta zama mallakina kuma da ita zan isa birnin tehran sannan na dagargaza kan sarkinsu da ita"
Nan muhaisin ya nufi gindin wannan itaciya wajenda wannan tsoho mai fararen kaya yake a daddaure
.
Wannan tsohon kuwa duk wannan gumurzu ada ya faru tsakanin jarumi muhaisin da wayannan karti duk akan idanuwansa ne,
Lallai rabon dayaga irin wannan jarumi tun zamanin wani sarkinsu wanda yake mulki a kasarsu
.
Muhaisin na zuwa gaban tsohon sai ya sanya wata takobi ya sare dukkan igiyoyin da suka daddaure tsohon
Tsohon kuwa koda yaji sassauci a bisa yanayin dayake sai ya budi baki yafadi wata kalma
"Alhamdulillah" wacce muhaisin bai taba jinta ba,
Tsohon ya budi baki da kyar akaro na biyu yace ruwa ruwa ,
Muhaisin na jin haka sai ya juya da nufin ya isa wajen da jakar guzurinsa take,
.
Kwatsam sai gani suka yi gari tayi duhu, dukkan wani haske ya rikida izuwa duhu
.
Babban abin mamakin kuwa shine a wannan lokacin tsakar ranace
.
Sai da dukkan dajin duhu ya mamayeta sannan wani dan haske ya bayyana take wannan hasken ya dan haskaka duhun nan kadan ta cikin hasken kuwa sai wani bakin hayaki ya fara fitowa
.
Wannan hayaki yai ta fitowa yana taruwa a waje daya ,sai da bakin hayakinnan ya gama taruwa sannan ya rikide ya koma suffar wani TSOHOn mutum
.
Shi wannan tsohon babu komai ajikinsa face wata guntuwar wando
Gashin kan tsohon nan hade da gashin gemunsa
Sune suka sauko suka rufe ilahirin jikinsa ,
.
Daure a damatsansa kuwa wasu layoyine da gurunan tsafi
.
Duk wannan abin daya afku akan idon muhaisin da wannan tsoho ya afku
.
Tsohon nan kuwa ma'abocin yawan gashi sai ya tunkari wajenda su muhaisin suke zazzaune,
,
Babu abin da zai kara baka mamaki da wannan tsohon shine sam baya tafiya da kafafuwansa ,
Iska ce ke daukansa ta kaishi duk inda yake so,
.
Koda wannan tsoho ya iso gaban su muhaisin sai ya bushe da dariya , koda ya tsuke bakinsa ga barin yin dariyar sai ya dubi muhaisin yace
"Yakai wannan jarumin saurayi kayisani yau babu mai kareka daga sharrina ,lallai yau ka hadu da babbar masifan da ta wuce zaton tunaninka"
.
Muhaisin najin haka sai ya dubi wannan tsoho yace da shi"yakai wannan bakon tsohon shin me na aikata agareka da har kakeson ganin bayana"
.
Tsohon najin haka sai ya tuntsire da dariya akaro na biyu sannan ya tsuke bakinsa yace
"Ka aikata manyan laifuka a gareni yakai wannan jarumin, kayisani cewa Sunana Abulzulmu Boka uban bokaye
Akwai wata damisa daka kashe da kuma wasu arnan daji wayanda kayi wa kisan gilla
.
Su wayannan arnan daji daka kashe dakaruna ne,kuma ni na turosu don sui maka kisan wulakanci a bisa kashe wannan damisar da kayi
Amma sai aka samu rashin sa'a duk ka hallakasu
Wannan yasa nazo da kaina don na gama da kai"
.
Koda gama fadin hakan sai boka abulzulmu yai nuni da hannunsa izuwa ga jarumi muhaisin, hade da fadin wasu dalasimai na tsafi
.
Take sai jikin muhaisin ta fara sandarewa , kafin wani lokaci gaba daya jikin muhaisin ta gama sandarewa,
In kadubi muhaisin yadda ya kame ya sandare ya koma GUnKI
.
Boka abulzulmu na ganin haka sai ya fashe da dariyan mugunta sannan yace" Na rantse da girman tsafi babu wani mahaluki walau mutum ko aljan daya isa ya maidoka izuwa siffarka ta asali face Ni, Ahaka zakai ta zama har duniya ta tashi wannan shine hukuncinka"
.
Nan dai ya cigaba da kyakyata dariya har ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba.
.
Wannan shine Al'amarin daya faru ga jarumi muhaisin a hanyarsa ta tafiya Birnin tehran don dauko fansar kashe mahaifinsa da sarki humaiz yayi.
.

Marubuci:- Shuraih Usman
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "NAMIJIN GASKE littafi na biyu 2 part B"

Post a comment