Results

NAMIJIN GASKE littafi na biyu 2 part C


NAMIJIN GASKE
Littafina biyu 2
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
Part 2C
.
Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa
wannan labari ta
ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan
za'a kiyaye
Copyright
Shuraih Usman

Al'amarin sarki humaiz kuwa washe gari da aka fito fada sai yasa sarkin yaki zabbagu ya shirya masa dakaru milyan daya wayanda zasui mai rakiya shima boka kamsusullajani
.
Koda wayannan dakaru suka hallara a fada , sai sarki humaiz ya fito daga cikin gidan sarauta, cikin wata gagarumar shigar yaki.
.
Nan sarki humaiz ya hau kan wata farar doki wacce aka yima ta Ado na gani na fada
.
A loacinne wani badakare ya busa wata kaho
Take aka fara tafiya
.
Tawagar sarki humaiz wadda ta kasance babbar tawaga wadda duk wani jarumi ko sadauki muddin yayi arba da su sai yaji hantarsa ta kada
.
Bayan sun shafe kwanaki goma suna tafiya batare da sun yada zango ba , bisa jagorancin boka kamsusullajani.
.
A kwana na goman ne suka yada zango acikin wani daji mai yawan sarkakiya, kai da gani kasan baza'a rasa muggan dabbobi ba acikinsa ba
.
Bayan dakaru sun gama kafa tantuna sai hadimai suka fara shirin dafa abinci
.
A cikin tantin sarki humaiz kuwa shine a zaune bisa wata kujera ta sarakai sannan ga wasu dakaru majiya karfi agefen hagunsa da damansa .
Agaban sarki humaiz kuwa kayan lambu ne kala kala acikin wata babbar faranti ta zinare
.
Kwatsam sai gani akayi boka kamsusullajani ya bayyana a cikin turakar koda bayyanarshi sai ya durkusa agaban sarki humaiz yace
"Yakai sarkin sarakai , hakika nayi bincike a cikin halwar tsafina bisa ga yanayin wannan daji da muka yada zango, kuma bincikena ya nunamin wata babbban masifa dake tunkaro mu"
.
Koda jin haka sai sarki humaiz ya turbune fuska yace"shin me ne tsafin naka ya nuna maka , sannan wata masiface take tunkaro mu"
.
Boka kamsusullajani yayi gyaran murya sannan yace "kayisani ya sarkin sarakai wannan dajin yana da mugun hadari domin kuwa
A cikin wannan dajin akwai wasu irin dabbobi wayanda adadinsu yafi dubu dari uku,
Su wayannan dabbobi sun kasance duk wata halitta da sukayi arba da ita take suke rufar masa su farke tumbinsa sannan su kwashe kayan cikinsa
Dabbobin sun dade suna rayuwa awannan daji sukan tare ayarin fatake ko rundunar mayaka wayanda tsautsayi ya shigo dasu cikin wannan daji"
.
Koda sarki humaiz ya gama sauraran wannan zance daga bakin boka kamsusullajani sai ya bushe da dariyan farinciki al'amarin daya baiwa boka mamaki kenan, cikin nuna alamun mamaki yace"ya shugabana shin ina dalilin wannan dariyar taka "
.
Sarki humaiz yayi shiru ga barin dariyar sannan yace " kasani yakai wannan boka cewa ba komai ya sanyani wannan dariyar ba face ji danai cewa zamu fafata yaki da wayannan dabbobin,kasani na kagu ainun damu isa dajin burkum don mu fafata da wayannan yanfashin daka labarta mani su,
Asabili da marmarin yaki dana keji , sai gashi yanzu yaki tazo ta taddani hargida"
.
Sarki humaiz na gama fadin hakan ya mike tsaye sannan ya fice daga cikin tantin
Fitarsa keda wuya sai ya kira sarkin yaki zabbagu sannan ya umarceshi daya hada masa rundunar dubu dari biyar zai fita farauta
.
Nan take zabbagu ya zabo zakwakuran dakarunsa har dubu dari biyar
Sannan sarki humaiz ya zo garesu ,
Ya dubesu yace dasu "yaku jarumai kuma gwaraza na birnin tehran kuyi sani cewa zmu fita farauta yanzu tare daku ,
Wannan farauta bata komai bane face ta wasu muggan dabbobi masu yawan gaske .
.
Lallai duk wanda yayi wani jarumta na musamman a cikin wannan farauta sama da ni ,
To yana da babban kyauta daga wajena "
.
Koda jin haka sai dakarun sukai shewa sannan suka kwala ihu iya karfinsu har saida sauttin muryoyinsu ya cika gaba daya ilahirin dajin
.
A sannan ne suka fice daga sansaninsu, sarki humaiz ne agaba sannan sarkin yaki zabbagu a gefensa .
.
Koda suka yi tafiya na sa'o'i biyu sai suka iso wani bangare acikin dajin
.
Shi wannan waje yakasance bishiyoyinsa jibga jibga ne
.
Su wayannan bishiyoyi ganyayyakinsu ya rufe gaba daya ilahirin jikinsu
.
Koda su sarki humaiz suka kariso wannan waje sai sarki humaiz ya bada umarnin a dakata take kowa yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak.
.
Sarki humaiz ya sauko daga kan dokinsa ya tsugunna ya debi kasan wannan waje ya sunsuna,
Sannan ya watsar ya haye kan dokinsa
Ya juyo yace wa dakarunsa "kuyi shiri domin kuwa wayannan dabbobi anan wajen suke da zama...."
Ai bai gama rufe bakinsa ba sai wani badakare ya kwala ihu.
.
Koda dakaru suka juyo don ganin wanda yayi ihun sai sukai arba da wata mummunar halitta.
Ita dai wannan halitta tana kama da damisa amma kuma sabanin damisa ita halittar bakace kirin.
.
Sannan ga wasu kaho guda biyu a tsakiyar kanta.
.
Take wannan halittar ta suri badakaren tai sama dashi isuwa daya daga cikin bishiyoyi masu duhuwa da sukai wa dajin kawanya.
.
Bayan dakiku kadan sai gani akayi wannan badakaren da dabbarnan ta janyeshi sama ya fado kasa .
.
Babu abin daya dugunzuma hankalin dakarun face ganin irin kisan da akaiwa wannan badakare , fafe tumbinsa akayi sannan aka kwashe kayan cikinsa

Take dakarun suka tsorata ainun da ganin irin wannan kisa take suka zazzare makamansu daga cikin kufe

Koda dakarun suka zazzare makamansu sai suka tsaya acikin shiri ,jira kawai suke suga ta inda wayannan dabbobi zasu kara bullo masu

Saida aka shafe dakiku ashirin amma wayannan dabbobi basu kara fitowa ba
Dakaru kuwa sai zazzare idanuwa suke tamkar zaSu ci babu

Koda dakiku ashirin da biyar suka shude sai sarki humaiz ya bada umarni da a sassare wayannan bishiyoyi

Take wasu dakaru suka nufi gindin bishiyoyin suka fara saransu cikin tsoro , tamkar ace kyat su ruga

Koda dakarun suka fara saran bishiyoyin kwatsam sai akaji dirgowan wasu abubuwa bisa kasa
Koda su sarki humaiz sukayi duba izuwa wajenda sukaji sautin dirgowan wayannan abubuwa sai hankulansu ya. Dugunzuma ainun,

Take ido ya raina fata ,wasu daga cikin dakarun kuwa marasa karfin zuciya sai tsoro ya darsu a zukatansu

A mamaye agaban su sarki humaiz wayannan dabbobi ne makil wayannda adadinsu yakai Dubu dari ukuRelated Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "NAMIJIN GASKE littafi na biyu 2 part C"

Post a comment