Results

NAMIJIN GASKE littafi na biyu 2 part D


Shuraih Usman
NAMIJIN GASKE
Littafina biyu 2
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
Part 2D
.
Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa
wannan labari ta
ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan
za'a kiyaye
Copyright
Shuraih Usman
.
.
Take dabbobin suka yi karaji sannan suka afka ma su sarki humaiz
Nan aka rincabe da masifaffen gumurzu tsakanin dakarun sarki humaiz da kuma wayannan dabbobi
.
Koda aka fara wannan gumurzu sai dakarun sarki humaiz suka raina kansu domin kuwa wayannan dabbobi sai karkashesu suke tamkar kiyasai,
,
Saide kaga dabbobin sun yi daka wata irin tsalle sun dira ajikin badakare take zasu sanya hakwaransu su farke mai ciki saide kaga kayan cikin bil'adama na kwarara biisa kasa
.
Abin daya dugunzuma hankalin dakarun shine sam dabbobin basa jin sara bare suka don kuwa muddin takobinsu ya hadu da jikin dabbobin saide kaji wata kara ta tashi tartsatsin wuta ya baiyana tamkar takobin ta sari dutse
.
Cikin kankanin lokaci dabbobin nan suka kashe kaso daya daga cikin dakarun sarki humaiz
.
Alokacin da sarki humaiz ya lura da irin barnan da dabbobin sukai masu
Sannan yaga ko dabba daya basu samu nasarar kashewa ba
..
Sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ransa yayi matukar baci take jikinsa ta kama bari nan ya kwarara wani uban ihu wanda ya firgita dukkan wata halitta dake cikin dajin
.
Kai hatta dabbobin nan sai da suka razana da jin wannan ihu
.
Dakarun sarki humaiz kuwa sun zata wata babbar masiface wadda tafi wadda suke ciki a yanzu
Hakan ce tasa suka firgita sannan suka yanki daji batare da sun san inda suka nufa ba
.
Sarkin yaki zabbagu ne kadai bai firgita sosai ba da wannan ihu da sarki humaiz yayi
.
Koda sarki humaiz ya gama kwarara wannan uban ihu kawai sai ya hau wayannan dabbobin da sara baji ba gani,
Duk da ya kasance wannan saran baya illatasu amma su kansu dabbobin sai da suka tsorata da al'amarin sarki humaiz
.
Sarki humaiz na cikin saran dabbobin ne kawai cikin sa'a sai ya soka ma wata dabba takobinsa a baki
.
Bisa mamaki sai yaga wannan dabbar tayi kururuwa sannan ta fadi kasa matacciya
.
Koda ganin haka sai sarki humaiz ya fahimci lagon dabbobin nan
.
Nan ya cigaba da tsalle tsalle yana dirgowa a gaban dabbobin yana soka takobinsa a cikin bakunansu
.
Koda zabbagu yaga haka shima sai yayi koyi da sarki humaiz shima ya ringa daka tsalle yana soke bakunan dabbobin nan
.
Cikin kankanin lokaci sarki humaiz da sarkin yaki zabbagu sukai ma dabbobin nan mugun barna don kuwa sun kashe sama da dubu dari biyu
.
Kwata kwata wayanda suka rage basufi dubu dari ba
.
Nan dai su sarki humaiz suka zage damtse sai ragargazar dabbobin suke bayan dakiku dari uku da sittin ne suka gama karkashe wayannan dabbobi
.
Sarkin yaki zabbagu ya dubi sarki humaiz a zuciyansa yace "lallai sarki humaiz ba karamin sadauki bane ,wai shin ma ta yaya aka yi har ya gano lagon dabbobin nan"
.
Sarki humaiz kuwa koda yaga sun karar da dabbobin nan sai ya daga kai sama sannan ya kwarara wata uban ihu wadda tafi ta farko firgitarwa da kuma amo,
Shi kansa sarkin yaki zabbagu baisan lokacin daya durkusa bisa guiwowinsa ba ya sanya yan yatsunta ya toshe kunnuwansa
.
Tsuke bakin sarki humaiz keda wuya sai wannan karar ta lafa
Koda sarki humaiz yayi duba izuwa gabashin wannan daji sai yaga wata kura ta toshe gabashin dajin.
.
Koda ya lura da kyau sai yaga ashe wasu rundunar mayaka ne ke tahowa wajenda suke
Ai yana ganin haka sai ya gyara rikon takobinsa sannan ya gyara tsayuwa
.
Alokacinne sarkin yaki zabbagu bin sharmil ya mike daga tsugunon dayake
.
Rundunar nan na karisowa sai sarki humaiz yaga ashe ma dakarunsa ne wayanda suka gudu sukaje inda suka kafa sansaninsu suka debo gaba dayan. Rundunar
.
Agaban wannan runduna kuwa boka kamsusullajani ne ke jagorantarsu
.
Rundunar na karisowa sarki humaiz ya basu umarnin da a cigaba da tafiya
Take yakama dokinsa ya hau sannan aka cigaba da tafiya

Wannan shine abin daya faru ga sarki humaiz tare da rundunarsa a lokacin daya baro birninsa don zuwa zuwa kogin bahar jallus ya dauko kambun tsafi
¤¤¤. ¤¤¤
Al'amarin muhaisin kuwa sa'adda boka abulzulmu ya maida shi gunki
.
Babban kuskuren da boka abulzulmu yayi shine barin wannan tsoho mai sanye da fararen kaya da yayi araye
.
Abin dayasa boka abulzulmu baiga wannan tsoho ba kuwa shine A lokacin da tsohon. Yaga boka abulzulmu ya bayyana kawai sai ya fara fadin wasu kalmomi
Take Allah ya makantar da Abulzulmu ga ganin wannan tsoho
.
Alokacin da wannan tsoho yaga duk abin daya faru tsakanin boka abulzulmu da kuma sadauki muhaisin
.
Koda bacewar boka Abulzulmu sai tsohon nan ya mike tsaye ya nufi wajen da jakan guzurin sadayki muhaisin yake Ajjiye
.
Da isar tsohon wajen sai ya bude jakar ya dauko wani batta wadda take cike da ruwa
.
Nan ya zuba ruwan a tafin hannunsa sannan sai yayi motsi da bakinsa da halamu wasu kalmomi yake furtawa.
.
Koda gama furta kalmomin sai tsohon ya tofa a hannusa ,sannan ya murmurza hannunsa ,
Yana gama murza ruwan a hannunsa ne sai ya iso gaban sadauki muhaisin nan ya shafe gaba dayan ilahirin jikin muhaisin da wannan ruwan.
.
Koda gama shafe muhaisin da ruwan nan sai gaba daya ilahirin jikinsa tayi haske,cikin kankanin lokaci gaba daya jikinsa ta juye izuwa siffarsa ta asali
.
Koda muhaisin ya komo izuwa siffarsa ta asali sai yayi tari har sau uku sannan ya dubi wannan tsoho dake gefensa yace "yakai wannan dattijo kayisani cewa ina da labarin boka abulzulmu Akan muddin yayi sihiri toh ko duk duniya zasu taru akan su karya wannan sihiri ,to bazasu iya ba saboda karfin sihirinsa da kuma hatsabibancinsa.
.
Amma sai gashi kai ka karya alkadarinsa, cikin kankanin lokaci
,
To waishinma kana da wannan karfin sihirin amma katsaya kana gani kartin can suka ringa azabtar da kai"
.
Koda jin haka sai tsohon yayi murmushi sannan yace da farko dai sunana Kuzaifa bin Usman
Sannan kuma ni ba boka bane kuma bana tsafi bare sihiri"
Muhaisin najin haka sai yace "to in kai ba matsafi bane taya har ka iya yin wannan sihiri mai matukar ban mamaki"
.
Tsoho kuzaifa yace"duk wannan abu dakaga nayi ba tsafi bane...."
"To in ba tsafi ba me nene" muhaisin ya katse shi
.
Tsoho kuzaifa bin Usman yaci gaba "bakomai bane ba face taimako daga Allah madaukakin sarki,kayi sani yakai wannan sadauki cewa babu abin daya gagari Allah(SWT) acikin wannan duniyar"
.
.

Marubuci:- Shuraih Usman
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "NAMIJIN GASKE littafi na biyu 2 part D"

Post a comment