Results

NAMIJIN GASKE littafi na biyu 2 part E


Namijin gaske
Littafi na biyu 2
Marubuci Shuraih Usman
© Shuraih 99% 2017
Part E

Tsoho huzaifa ibn Usman ya cigaba da fadin " ubangiji madaukakin sarki shine wanda bai haifa ba kuma ba'a haife shi ba shine Ubangijin daya halicci dukkan mutane da dabbobi da duwatsu da duk wani abun daka tsinkaya a cikin wannan duniya dama ita kanta duniyar baki dayanta,
Allah (S W T) shi ne ya halicci sammai bakwai da kassai bakwai a cikin kwanaki shida sannan ya dorasu akan al'arshi, shine ubangijin da ido ya faku daga ganinsa kunne ya gaza ga saurarensa, ubangijin annabi ibrahima A.S ubangijin fiyayyen halitta Annabi Muhammadu S.A.W

Tun sa'in da tsoho huzaifa ya fara bayaninsa jikin muhaisin ya mutu ya ji zuciyarsa ta karkata ga wannan addinin musulunci nan da nan ya dubi tsoho huzaifa yace "yakai wannan tsoho hakika naji zuciyata ta karkata ga wannan addini naka duk da kuwa na kasance da ni da mahaifiyata bama da wani addini bama bautar komai kawai dai munsan muna rayuwa, maza ka sanar dani yadda zanyi na shiga cikin addinin islama.
Farin ciki ya kama Tsoho huzaifa sa'adda yaji hakan a take ya biyawa muhaisin kammar shahada ya maimaita sa'annan suka cigaba da tafiya
Bayan sun dau kimanin kwanaki biyu suna tafiya a tare tsoho huzaifa na koyar da muhaisin abubuwan da suka danganci addinin musulunci a rana ta biyu ne bayan sun idar da sallar isha'i suka hura huta domin jin dumi
Suna zazzaune a gaban wutar tsoho huzaifa ya dubi muhaisin yace "kai ko yaro na sha'afa ban tambayeka tarihinka ba da garin da ka nufa"
Koda jin wannan tambayar sai muhaisin ya dan gyara zama sannan ya kwashe dukka labarinsa ya gayawa tsoho huzaifa ya kare da cewa "kaji wannan shine labarina da dalilin fitowata daga gida kuma na dau alƙawarin bazan taba komawa ga mahaifiyata ba face da kan makashin mahaifina sarki humaiz, amma kaiko menene labarinka da labarin birninku, muhaisin ya karisa maganar tasa da tambayar tsoho huzaifa
Tsoho huzaifa ya dubi muhaisin yace kamar yadda na sanar dakai a baya sunana Huzaifa ibni Usman ni dan birnin Nurul Islam ne kasar mu na gaba kadan tafiyar kwanaki shida zamuyi mu isa , ba komai bane ya fito dani daga gida ba face yaɗa addinin Muslunci a duniya to ina cikin wannan tafarki ne na iske waƴancan kartin daga ceci rayuwata daga hannunsu koda na iso garesu sai nayi musu sallama babbansu ya dago kai ya dubeni ya daka mani tsawa yace "waye kai da har zaka biyo ta wannan daji sannan ka ratso izuwa sansaninmu

Na dube shi a natse nace "sunana Huzaifa ibni Usman nazo gareku ne da addinin tsira addinin musulunci yaku wayannan mutane ina kira a gareku da ku yi watsi da duk ababen bautar ku ku riki ubangijin nan da ido baya iya ganinsa kunne baya iya jin zancensa, wannan ubangijin da ya halicce ku don ku bauta masa sannan ya ni'imta ku da ni'imominsa..." Ai tun kafinma na karisa maganata shugaban dakarun ya sake daka min tsawa a karo na biyu sannan ya dubeni yace "wato kai kana nufin mu hanu ga bautar gumakanmu da wuta lallai ka tabbata tababbe kuma dole muyi maka hukunci akan hakan "
Yana gama fadin hakan yai dubi ga yaransa ya daka wa wasu tsawa yace " ku kamo min malalacin tsohonnan ku daureshi jikin bishiyar nan,
Aiko bai gama rufe bakinsa ba wasu tika tikan samari su uku sukai kaina suka kamani suka daure jikin bishiya
Wannan shugaban nasu daka kashe ya zo gareni fuskarsa na yatsine nan ya umarci yaransa dasu hura wuta, nan da nan ko suka hura, ya sanya karfe cikin wutar yacigaba da azabtar da ni har lokacin da Allah madaukakin sarki ya amsa addu'ata ya turo ka gareni ka tseratar dani daga wurinsu."
Tsoho huzaifa yace "a cikib labarin daka sanar mani naji ka ambaci sunan sarki humaiz na birnin Tehran to ka sani shi wannan sarki watanni uku baya yayi hawa yazo har birninmu ta nurul islam da nufin ya yakemu ya kona birninmu sannan ya kashe kowa da kowa dake cikinsa amma Allah bai bashi iko ba Al'amarin kuwa duk ya farune sanadiyar labarin gimbiyar mj zaharatu daya samu labarinta
Sarkinmu sunansa Ubayyu ibn hubairu sarki ubayyu na da matar aure guda daya mai suna fatimatu kuma yana da ƴa guda ɗaya mai suna gimbiya zaharatu

Gimbiya zaharatu ta kasance kyakkyawa na gaban kwatance do minko randa aka haifeta matan da suka amshi haihuwarta sai da suka tsorata da tsananin kyawunta suka ruga ga sarki suna cikin tashin hankali suka sanar dashi matarsa fadimatu ta haifi aljana

Sarki ya cika da mamaki gaya ya tafi ga matarsa da kansa ya dau jaririyar yana dubanta shima kansa sai da ya tsorata da kyawun jaririyar amma sam bai kawo cewa aljana bace sarki yayi farin ciki matuka da samun ƴa da ranan suna ya zagayo aka sanyawa yarinyar suna zaharatu saboda tsananin kyawunta

Tun yarinya zaharatu na ƴar shekara biyar manyan sarakunan duniya ke tururuwa wurin neman wa ƴaƴansu aurenta har Allah ya nufa ta girma ta cika shekaru ashirin a duniya inda asalin kyawunta ya bayyana sarakuna tajirai da manyan ƴan kasuwa kuwa sukai ta tururuwa a fadar sarki ubayyu don neman auren gimbiya zaharatu.

Duk sarki ko tajirin da yazo wurin sarki neman aure. Zaharatu sai sarki yace dashi "yakai wannan dan sarki kaje ka nemi amincewar gimbiya muddin ta yadda ta aminta dakai a matsayin wanda zata aura to ba makawa zan aurata gareka muddin kuma tace a'a sai kai hakuri don ni bazan aurar da ƴata ga mutumin dabata kauna ba"
Suko tajirab a duk sa'in da sarki ubayyu ya fada masu haka sai su tafi wurin gimbiya zaharatu don neman amincewarta itako ko kallonsu ma batayi ballantana ta kula su
To a irin hakane labarin gimbiya zaharatu ya riski Sarki humaiz na birnin tehran ....

Zan cigaba

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "NAMIJIN GASKE littafi na biyu 2 part E"

Post a comment