Results

NAMIJIN GASKE littafi na biyu 2 part F


Namijin gaske
Littafi na biyu 2
Part F
Marubuci Shuraihu Usman


Ana hakan ne Sarki humaiz ya samu labarin gimbiya zaharatu nan take ya kirayi bokansa ya umarceshi daya bayyana masa hotonta yaga

Bokansa Kamsusullajani ya fiddo madubin tsafinsa ya shafeshi maimakon madubin ya bayyana hoton gimbiya zaharatu ai sai ya tarwatse wannan abu ba karamin tayarwa da boka Kamsusullajani hankali yayi ba ya dago ya dubi sarki humaiz yace
"Ya sarkin sarakai kayi sani cewa Su mutanen birnin nurul islam daka umarceni dana nuna maka hoton gimbiyarsu sun kasance suna bautawa wa ni ubangiji ne na daban wanda ya ke matukar kiyaye su daga dukkan tsafi, kai sani cewa su fa tsafi ko sihiri baya cika tasiri a jikinsu face an taki sa'a shiyasa kaga ma madubin tsafina ya tarwatse yayin dana ke kokarin binciko maka hoton gimbiya zaharatu, "

Sarki humaiz ya numfasa sannan yace "to ko ma dai menene ina bukatar daka bani shawarar ta yadda zan bullo masu domin kuwa na samu labarin ita wannan gimbiya zaharatun kyakkyawace ta gaban kwatance kai wasu ma sunce inda za'a zagaye duniya kaf da matukar wuya a samu wacce ta dareta kyawu wannan yasa najinina matukar kaunarta wutar begenta na ruruwa cikin zuciyata"

Koda boka Kamsusullajani yaji batun sarki sai ya mike daga durkuson dayayi yace "ya sarkin duk duniya yanzu dai ina mai baka shawara daka aika dan sako ga mahaifin gimbiya zaharatu tunda dai shine sarkin kasar kana mai nuna bukatuwarka nason auren yarsa, in ya amince to ya shafawa kansa da kasarsa lafiya in kuwa ya bijire sai kayi hawa da dakaru kaje ka rushe kasar tasa sannan ka dau ita gimbiya zaharatun ka aureta "

Sarki humaiz yayi na'am da shawarar da boka Kamsusullajani ya bashi nan da nan ya tashi manzo da takarda zuwa ga sarki ubayyu

Sarki ubayyu na zaune bisa karagarsa ta mulki a fada a na tsaka da fadanci manzon sarki humaiz ya shigo fadar kai tsaye ya mika wasikar dake hannunsa ga magatakarda

Magatakarda ya bude ya fara karantawa kamar haka
Daga Sarkin sarakuna sarki humaiz na birnin tehran zuwa ga sarki Ubayyu kai sani cewa na rubuto wannan takarda ne gareka ina mai neman auren ƴarka gimbiya zaharatu, nasan cewa kana da labarina da duk irin zaluncina, in ka amince da ka aurar da ƴarka gareni ka shafa wa kanka da mutanenka gamida birninka lafiya muddin kuwa ka bijirewa bukatata zanyi hawa nida dakaruna muzo har birninka mu yakeka mu kashe samari,yara da tsofaffin birninka sannan mu kama matayenku a matsayin bayi mu kuma kone birnin naka sannan na auri yartaka, kaima kuma nai maka kisan gilla.."

Aikoda magatakarda ya zo nan a karatunsa sai sarki ubayyu ya daka masa tsawa cikin harzuka hayaki na fitowa daga bakinsa ya dubi dan sakon sarki humaiz yace masa maza kaje ka sanar da wulakantacce kuma kafirin sarkinku cewa bazamu Aurar da gimbiya zaharatu ga kafiri azzalumi ba in yaki yake ji to ya fito da gabadayan rundunarsa mu gwabza

Sarki ubayyu na gama fadin hakan yayi wucewarsa cikin gida zuciyarsa na tafarfasa bisa ga kalaman sarki humaiz

Koda manzon sarki humaiz ya dawo gareshi ya kwashe duk abunda ya faru ya gayamasa nan take sarki humaiz ya dubi sarkin yaki zabbagu ya daka masa tsawa yace afara shirin yaki don kuwa nan da kwanaki uku zamu isa ga birnin nurul islam
Washe gari kuwa sarki humaiz yai hawa da dakarunsa suka nausa birnin nurul islam,
Acan birnin nurul islam kuwa tuni labari ya riski sarki Ubayyu game da futowar sarki humaiz Nan da nan ya kira sarkin yakinsa mai suna faruk ya sanar da shi da afara shirin yaki,

Kafin su sarki humaiz su riski birnin nurul islam tuni sarki Ubayyu shima yayi gagarumar hawa da dakaru masu matukar yawa ya fita bayan birninsa ya tsaya suna tsumayen su sarki humaiz su karaso

Koda isowar su sarki humaiz suka riski rundunar sarki ubayyu sai suka ja linzamin dawakansu suka tsaya,
Nan fa aka cigaba da kallon kallo tsakanin rundunar sarki humaiz da rundunar sarki ubayyu,
Rundunar sarki ubayyu basu kai ko rabin rundunar sarki humaiz ba amma hakan bai sanya sunji ko dar a cikin zukatan su ba illa wani irin ƙwarin guiwa dake shigarsu
Su kuwa dakarun rundunar sarki humaiz mamaki suke gamida farin ciki na ganin sun fi abokan hamayyarsu yawa ko shakka basayi zasu yi nasara a wannan yaki

Sarki humaiz ya fito gaban rundunarsa yana bisa kan ingarman doki yai kira da sauti mai girma yace "yakai sarkin birnin nurul islam kayi sani cewa ka janyowa kanka da kasar ka masifar da bazaku iya riketa ba, ina mai tabbatar maka da a wannan rana zan shafe birnin ku daga doron kasa a bisa bijirewa bukata da kayi,"

Sarki humaiz na gama fadin hakan sarki ubayyu dake gaban rundunarsa ya daka wa sarki humaiz tsawa yace " kai mushriki wanda ya riki wanin Allah a matsayin abin bauta, kada yawan rundunarka ya rudeka lallai ina mai tabbatar maka da baku isa ku yake mu ba face da yardan ubangijin musulunci shi kuwa ubangijin musulunci baya goyon bayan azzalumai "

Koda sarki humaiz yaji abunda sarki ubayyu ya fadi sai ya harzuka matukar harzuka yai dubi ga rundunar sa ya daka masu tsawa yai masu umarni da su afkawa su sarki ubayyu

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "NAMIJIN GASKE littafi na biyu 2 part F"

Post a comment