Results

NAMIJIN GASKE littafi na daya 1 part F

Namijin gaske 1
Part 1F
(c) Shuraih Usman
@shuraih 99%
NAMIJIN GASKE
Littafina daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
Part F
.
Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa
wannan labari ta
ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan
za'a kiyaye
Copyright
Shuraih Usman
.
Acan birnin tehran kuwa tun lokacin da sarki hinzur ya mutu, sai aka rada waziri humaiz, a
matsayin sarki.
.
Nan fa waziri humaiz ya dawo izuwa sarki humaiz,
Nan ya fiddo da asalin siffarsa ta mulkin zalunci,
Mutanen birnin tehran sun koka sosai akan wannan mulki nasa,
Ya kara yawan haraji, bisa na da, kuma bai dauke wa kowa ba, yaro,jinjiri,babba,tsoho, dole su
biya,
Laifi kadan talaka zaiyi yanzu zaisa ayanke masa hukuncin kisa
Su ko attajirai na matukar jin dadin mulkin nasa ,
Rabon da a shimfida irin wannan mulkin zaluncin tun zamanin wani gawurtacce kuma sadaukin
Azzalumin sarki mai suna Lu'umanu
(A duba kundin tsatsuba)
.
Wata rana sarki humaiz na barci sai yayi mafarkin wai ga sarki hinzur ya dawo izuwa birnin tehran
Yana zuwa ya nufi gidan sarauta
Da zuwansa gidan ya shiga dakaru suka taso masa amma koda sukayi arba da tsohon sarkinsu
Sai suka zubda makamansu,

Nan sarki hinzur ya dakumo wuyan sarki Humaiz,
Bayan ya hada masa jini da majina ya luguigita shi,
Sai ya sanya masa igiya a kafa sannan ya daure igiyar a jikin doki, nan ya hau kan dokin sannan ya
zabureshi,
Wannan dokin yai ta tsala gudu, bai tsaya ako inaba sai da ya kariso tsakiyan gari,
Koda mutane sukai arba da sarki hinzur sai suka kamu da matukar farinciki ,
Nan take sarki hinzur ya dubi jama'an garin yace da su"Ya ku al'umman birnin tehran shin kuna son
wannan sarki naku kuna jin dadin mulkinsa ,koko a'a na kashe shi"
.
Gaba daya jama'an garin sai cewa suke akashe shi, la'ananne,azzalumi,akashe shi kawai
Nan take sarki hinzur ya sauko daga kan dokin daya ke kai sannan ya amshi takobi a hannun wani
badakare, ya daga sama da nufin ya fille ma sarki humaiz kai.
Humaiz na bada hakuri amma ina
Nan take sarki hinzur ya sauke mai takobin....
.
A daidai wannan lokaci ne sarki humaiz ya farka a firgice, wata kyakkyawar mace dake kwance
agefensa ta mike , cikin kissa tace
"Ya masoyina shin meke damunka ,da har ka farka haka a firgice"
.
Murmushi yayi yace"Wani mugun mafarki nayi "
Yana gama fadin hakan sai ya sauko bisa kan luntsumemiyar katifan da suke kwance akai,
.
Cikin kankanin lokaci ya sanya kayansa, sannan yayi tafi da hannu,
Gama tafinsa keda wuya sai ga wasu dakaru su biyu sun shigo cikin turakar, dakarun suka russuna a
gabansa nan ya umarcesu dasu tafi su kira masa boka kamsusulajani,
Nan suka fice.
.
Cikin kankanin lokaci sai ga boka kamsusulajani ya bayyana acikin turakar ,
Yace "ya shugabana shin me nene dalilin daya sanya kace ayi kirana,"
Sarki humaiz yace" yakai boka kamsusulajani kayi sani yau nayi mugun mafarki wanda ya tsorata
ni ainun,dalilin kiranka kuwa so nake ka fassara mani wannan mafarki tawa,
.
Take ya kwashe labarin abinda yagani acikin mafarkinsa ya sanar da shi,
Koda boka kamsusulajani yaji haka sai yace ya shugabana, ina bukatan lokaci don nayi bincike bisa
halwar tsafina "
Sarki humaiz yace" na baka daga yau zuwa gobe da safe lallai ina son jin fassarar wannan mafarki,"
Koda gama fadin haka sai boka kamsusulajani ya bace bat.
Washe gari a fada ana fadanci ayayin da kowa ya lura da hankalin sarki humaiz ya dugunzuma
ainun,sabanin da dazakaga sai annashwa yake yana keta dariya .
Kwatsam sai gani akayi boka kamsusulajani ya bayyana tsulum acikin fadan,
Wasu fadawa har sun tattara rigunansu da niyyar su ruga amma koda suka ga boka kamsusulajani ne
sai hankalinsu ya kwanta
.
Nan ya kwashi gaisuwa a wajen sarki
Srki humaiz ya sallami kowa a fadan fada ta rage su su biyu,
Sarki humaiz yace "gareka boka kamsusulajani shin me ka ganpo abinciken dakayi,"
Nan take boka kamsusulajani yafara bayani kamar haka" hakika mafarkinka sai ya tabbata..."
Sarki humaiz ya daka masa tsawa yace"ashe kai wani sakarai ne ban sani ba tayaya mutumin dana
kasheshi da hannuna zai dawo ya kasheni, ko ka taba ganin anmutu an dawo ne"
Boka yai murmushi yace "eh ba'ataba mutuwa an dawo ba , amma kasani alokacin daka kashe sarki
hinzur ai baka kashe matarsa hamasiya ba,babban kuskuren daka aikata kenan,

Kayisani koda hamasiya ta tsira daga hannunku, tana dauke da ciki wata takwas, kuma ta haife
wannan da nata yanzu haka ya girma ya zama gawurtaccen jarumi, kuma gagarabadau, lallai ina
sanar da kai cewa yana nan zuwa birnin ka nan da yan wasu lokuta kuma ya kasheka sannan ya
amshe mulkin mulkin mahaifinsa .
Koda sarki humaiz yaji haka sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ,nan ya dubi boka kamsusulajani
yace dashi"toh shin yanzu ina mafita,
.
Boka kamsusuljani yace" mafita dayace "
Cikin kaguwa sarki humaiz yace "yakai dirkan birnin tehran gaggauta sanar dani mafitar da ka samo
mana"
.
Boka yace "bakomai bane wannan mafita face ka mallaki Wata KAMBUN TSAFI wacce aka
killace ta a tsibirin bahar jallus"
.
Boka kamsusulajani ya dubi sarki Humaiz bin Humas yafara bashi labari kamar haka
.
Kimanin Shekaru aru aru da suka shude A Cikin wannan birnin Na Tehran anyi wani gawurtaccen
Azzalumin sarki mai suna LU'UMANU na birnin Tehran a duba KUNDIN TSATSUBA
.
Shi wannan sarki mai suna Lu'umanu yana da wata kambu na tsafi wacce take daure a hannun
hagunsa,
Da wannan kambune yayi amfani inda yai ta shimfida mulkin zalunci ,
Har lokacin da wani ma'abocin bakon Addini ya hallakashi
.
Yanzu kambun tsafin na ajiye a tsakiyar tsibirin bahar jallus,
Muddin ka mallaki wannan kambu toh duk duniya babu wani jarumin da bazaka taka ba,
Sai ka zama guguwar Annoba mai shafe birane,
Akwai wasu Manya manyan sarakunan aljanu na duniya baki daya guda goma sha bakwai da ke ma
wannan kambu bauta,
Muddin ka mallaki wannan kambun toh duk zasu da wo karkashin ikonka,
.
Ita wannan kambu tana tattare da alkaluman sihirin tsafi guda dubu
Kasani muddin ka mallaki wannan kambu toh tamkar ka mallaki wayan can sihirin tsafin ne,
,
A baya jarumai, sadaukai, da Mazan kwarai, duk sun rasa rayukansu bisa mallakar wannan kambu
ta tsafi,
.
Kayisani yakai wannan sarki
Kafin ka isa tsibirin bahar jallus kuwa sai ka bita cikin wasu mugayen dazuka guda biyu,
.
Dajin farko ana kiransa da suna Burkum
Babu komai acikin wannan daji face dandazon yan fashi wayanda adadinsu yafi milyan
Su wayannan yanfashi sun kasance mugayene sam basu da imani ko kadan don ko bera sukai arba
da ita toh take suke gutsutstsure namanta su rabata ga junansu yadda kowa sai ya samu
.
Komai suka samu raba daidai suke da ita yadda kowa zai samu duk kankantashi kuwa,
.
Atarihin wannan daji babu wani mahaluki walau mutum ko aljan wanda ya taba ratsawa ta cikin
wannan daji a raye,
Kai muddin mutum ya shiga wannan daji toh tamkar ya shiga lahira ne don kuwa baza a sake jin
duriyarsa ba
.

,
Daji na gaba kuwa ana kiransa Da suna Darul marid babu komai acikin wannan daji face wasu irin
zabga zabgan maridai wayanda adadinsu yakai dubu
.
Su wayannan maridai kaifi ko tsini baya tasiri ajikinsu face zagwaron karfin damtse, don sun
kasance suna masu baiwa jikinsu horo ta hanyar shan wani tsumi wanda muddin suka sha toh ko
kwana zakayi kana saransu ,
Ba za su san kanayi ba
.
A tarihin duniya baki daya
ba'ataba samun wanda ya ratsa ta cikin wayannan dazuka guda biyu sannan ya fito a raye ba walau
mutum ko aljan,
.
Shi kuwa tsibirin bahar jallus, duk yafisu masifa da bala'I
Don kuwa wasu irin Aljanu ne a wajen
Su wayannan aljanun suna da katon kai kaman randa sannan sai sililin kafafuwa wanda ke
barazanar karyewa a ko wani lokaci,
,
Aljanun gaba daya jikkunansu launin ja ne,
Da sun hadu da mutum ko aljan nan take zasu zuke jinin jikinsa, ta hanyar taba sassan jikinsa
.
Su wayannan aljanu suke tsaron wannan Kambu ta tsafi
.
Lallai tafiya neman wannan kambun tsafi bakaramin masifa da bala'I bane
Don kuwa NAMIJIN GASKE ne kadai zai iya tunkarar wayannan masifu batare da yaji tsoro ko
shakka acikin zuciyarsa ba
."
Koda boka kamsusuljani yazo nan azancensa sai yaga sarki humaiz ya bushe da dariya al'amarin
daya bashi mamaki kenan
Sarki humaiz ya dubi boka kamsusuljani cikin yarda da kai yace
"Lallai ko zan rasa rayuwata sai na mallaki wannan kambun tsafin kuma ina sanar dakai cewa ka
shirya don kuwa da kai za'ayi wannan tafiyan
.
SHIN SARKI HUMAIZ ZAI SAMU NASARAR MALLAKAR KAMBUN TSAFI KUWA
.
WANI IRIN MASIFU DA BALA'IEU ZAI HADA DASU
.
SHIN BOKA KAMSUSULLAJANI ZAI AMINTA YAYI WANNAN TAFIYA MAI MUGUN
HADARIN KUWA
.
INA LABARIN JARUMI MUHAISIN DA MAHAiFIYARSA
.
SHIN ZAI SHIRYA YAZO BIRNIN TEHRAN DAUKAN FANSA
.
WANI KARAN BATTA ZA'AI TSAKANINSA DA SARKI, HUMAIZ,
.
Domin jin wayannan amsoshin sai ku tsumaye ni a littafi na biyu
.
NAMIJIN GASKE
Littafina daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman

Tel. 08133209890
.
Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa
wannan labari ta
ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan
za'a kiyaye
Copyright
Shuraih Usman
.
SHEKARAR RUBUTAWA:- 2017
Addreshi:- tshon/kasuwa gidan malam Usman ,nasarawa state Keffi
.
Akwatin waya:- 0908626148,08133209890
.
Kagaggen labari daga shuraih Usman
SADAUKARWANE GA
M.malam Usman
M.hajiya Maryam
Mujahid hamza(mijin biza) best friend forever
Sis.Zainab Usman
Bro.abdulaziz Usman
Sis.Amina Usman
BAN MANTA DA KUBA
Dahiru Usman Diffusion(D.U.D)
Anas aliyu katuka (bin malik)
Suleiman ishaq(Big army)
Abdullahi Isa (B.O.C)
Dafatan kuna cikin koshin lafiya
Alhamdulillah

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "NAMIJIN GASKE littafi na daya 1 part F"

Post a comment