Results

NI DA YAYA LAMEER page 1 to 10

❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
         
         **NI DA YAYA  LAMEER**

                              ❤❤❤❤
                               🧡🧡🧡💓
   *Gajeran labari*

*Story and written*

*By*

*Fateemah Sununi Rabee'u*
*(Ummu Affan)*

         

________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


*MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽*
*UWANIN QAUYE*
*CIKIN WAYE?*
*And now👇*

 *NI DA YAYA  LAMEER!*

*WhatsAPP no 08104335144*


_*SHINFIƊA*_
*Godiya ta tabbata ga Allah (S W T)da yasake bani dama na rubuta muku wannan littafin,Tsira da aminci suk'ara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad (S A W)da alayensa da sahabbansa da wad'anda sukabi ta farkinsa har zuwa ranar sakamako.*


_*GIRGIƊI*_

_*Wannan labarin k'irk'irar ran labari ne banyisa don chin zarafin wani ko wata ba duk wanda yaji yayi kama danashi to arashi ne da fatan za'a guji zargi banyisa don wani ko wata ba ko cin zarafin kowa ba,banyarda a juyaminshi to ko wacce suffah ba da fatan za'a kiyaye.*_


*DIDECATED TO ATK*

*SPECIAL GIFT TO*
*ANTY HAUWA*


_GAISUWA TARE DA FATAN AL'AMARIN ƳAN UWANA NA AREWA WRITER'S ALLAH YA ƘARA HAƊA KANMU AMEN_


BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM


🅿1↪2"Ni aradun Allah ba inda zani haba Kakar nan wai me ke damunki ne ko duk rud'un tsufan ne,

Muryar wata 'yar matashiyar budurwar yarinya kenan wacce bazata wuce shekaru goma sha hud'u da haihuwa ba,

Kakar tata wacce ashekaru zatayi sittin da biyar tace"haba 'yar jikallena zenabubuwata 'yar abullena don Allah kije mana kinga yanata jiranki kar yajiki shuru,

Turo baki gaba tayi cikin tsabar shagwa6a irin ta goyan kaka tace"Aradun Allah mutumin nan d'an renin wayau ne Kaka jiya fa har mazge min baki yayi sbd tsabar mugunta irin tasa nifa nagaji da zuwa gurinsa,

Kaka ta fara turata"don Allah Abulle ki wuce banson shak'iyanci irin naki,d'an murmushi tayi aranta tace"uhmmm wllh nasan mgninsa yau,

Da gudu ta ruga ko mayafi babu,ita dai Kaka cewa tayi "sai kin dawo Abulle na,ko juyowa batayi ba,bata dire a ko ina ba sai k'ofar gida,daidai inda yayi parking motarsa,

Sai lokacin na k'are mata kallo ba laifi kyakkyawace 'yar dubaduba,Choculate colour ga idanuwa da dogon hanci d'an bakinta me kyau,bata cika tsayi ba kuma ba gajera bace daidai daidai misali

Jikinta kuwa atamfa ce,riga da zani sai kallabi da ta d'aura fuskarta ba kwalliya don ba kwalliyar take ba,

Tsaye yake jingine a bakin motarsa kyakkyawan saurayi fari dogo,ai ina kallonsa nace masha Allah don guy d'in ya had'u ba makusa ko ta ina yayi,d'an boko wayayye daga ganinsa kasan nera ta zauna ajikinsa,

Tana zuwa taci burki gabansa,da sauri ya matsa,"subuhanallahi ya fad'a duk a zatonsa dokine ya antayo a guje,"Lah YAYA LAMEER gsky yau ka had'u d'an bani wannan k'atuwar wayar taka na d'auke ka photo,

Nan ta zura hannu aljihunsa tana k'ok'arin cirowa,

Rik'e hannun yayi gam yana kallonta,d'aure fuska yayi"wai ke Zainab sai yaushe zakiyi hankali ne,harara ta banka masa,

Sai kuma ta k'wa6e fuska"uhmm don Allah ka kawo na d'aukeka photo yaufa ka had'u sosai,

Mik'a mata wayar yayi,ta kasa danno inda ya kamata don ba iyawa tayi ba,jikinsa ta dawo,yauwa nama fasa d'aukarka kunnamin game na fad'an nan,

Wanda ake haka,nan ta fara nuna masa da hannu da k'afar ta kama hannunta yayi yace"to naji yau bazan kunna miki ba sai kin amince zaki koma gurin Ammi,

Mak'e kafad'a tayi"uhhhm uhmmm Wllh bazai yarda ba,ba kai bane chaf ni bazan yarda ba,

Juyawa yayi zai shiga mota alamar yayi fushi "da sauri tasha gabansa tare da rungumesa ta mak'alk'ale ajikinsa,turo baki tayi cikin shagwa6a tace"Am Sorry Yayah Lameer zan koma amma saidai na dunga kwana d'akin Ammi,ka amince?murmushi yayi tare da gyad'a kai bayan ya lumshe ido alamar ya amince,

Tace"yauwa to kunna min game,yace"mushiga ciki zan kunna miki a d'akin KAKAH,


Ya kukaji littafin muci gaba ko mu tsaya,

Yawan comments yawon tyiping,baida yawa labarin idan kuka bani had'in kai da comments kuma shirhi masu dad'i to nima zakusha mamakin typing✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
         
            **NI DA YAYA  LAMEER**

                              ❤❤❤❤
                               🧡🧡🧡💓
*GAJERAN LABARI*


*Story and written*

*By*

*Fateemah Sununi Rabee'u*
*(Ummu Affan)*

         

________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽*
*UWANIN QAUYE*
*CIKIN WAYE?*
*And now👇*

 NI DA YAYA LAMEER!


_Rawa da girgiza zanyi gabanku in jujjuya💃💃Ina muku albishir kunyi dace da mai tarbiya,Comments d'inku na jiya yasa na jujjuya💃💃💃Idan kukaci gaba da haka zakusha mamaki_,

_Wow Aradun Allah jiya kunsani farinciki na yarda littafin nan ya samu kar6uwa,tom acigaba da gashi,_
_NI DA YAYA LAMEER Fans ina godiya,kuma 'yan Facebook ba'a barku abaya ba gsky inayinku over ana tare🤝_


*WhatsAPP no 08104335144**Diditated to ATK*

*Special gift to Anty Hauwa*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

🅿️3↪️4

Suna shiga suka iske Kaka har ta baje kan kujera tana gengad'i,sallama sukayi ta bud'e ido nan ta fara washe baki,

Tace"d'an tselan uwa LAMEERU kaine yaune kayi niyyar shugowa da ba kiranta awaya kake ku zauna amoto ba yau kuma me yashugo da kai,

Yace"Allah ya baki hak'uri Kaka yauma abinda ya shugo dani had'a kayan Zainab zanyi mu wuce gida ai bakisan fushi nake dake ba tunda kika rik'emin mata,

Zaro ido Zainab tayi😯tace"Chaf chafd'i jan aradun Allah bazai yarda ba wace mata ni ce mata,saitasa kuka tana nuna kanta"cikin kukan tace"ni YAYA LAMEER nace kadena cemin mata,ai sai araina ni ace ni mata ce,haik'an take kuka,

Da sauri yazo kusa da ita ya zawota jikinsa yarungume yana buga bayanta alamar rarrashi yace"Sorry My Wife bazan sake ba,sai kawai ta tun tsuro da dariya tasake hawa jikinsa tace"yauwa YAYA LAMEER haka nake so amma da zakace min mata

🤣🤣🤣(Kunji Ummu Inteesar to meye ma'anar Wife d'in na zaci duk d'aya ne,😜)

Kaka tace"shashashar banza kawai ai daman ko LAMEERU baizo ba nayi niyyar yau saikin bar gidan nan baki da aiki sai shashanci,gwalo tawa Kaka tace"kedai rud'un tsufa ne ke damunki,

Sallama muka juyo duka muka juya,Abbu ne sai Ammi da Baba sai Umma,

Ai da sauri na sauka jikin YAYA LAMEER naje na d'ane Abbu nace"sannu da zuwa Abbuna,rik'eni yayi cikin murmushi yace"yauwa Ummina,murmushi mukayi muka zauna bisa kujerun dake farlour,

Baba yace"Gwoggo sai mukaji Ummi ta dawo gidan nan,da yake haka suke kiran Zainab,kasantuwar sunan Gwoggonsu gareta wato Kaka,

Tun kafin Kaka tayi magana Zainab tace"Wllh Baba Yaya Lameer ne ya ke.....Umma ce ta buge mata baki sanadiyyar shurunta,Ammi tace"haba meye hakan ne kike bugemata baki ki bari ta fad'a kika sani ko wani abun yake mata,

Umma tace"haba gida d'aya fa kuke ya za'ayi ya mata wani abu na ba daidai ba,Ammi tace"amma kinsan part d'insu daban ko?,

Umma tace"duk da haka,Zainab ce ta fara cewa"kuma wllh nan....Baba ya daka mata tsawa "Ummi meye kikeyi haka,Kaka tace"wllh ni duk tabi ta isheni LAMEERU d'auketa ku tafi,kamar yana jira ya kafa hannunta sukayi waje,su Abbu da Baba dry suka saka,Kaka kuwa sai mita take,

Cikin mota ya sakata ya zagaya yaja motar,bai mata magana ba har suka isa gida,Wow masha Allah gidan ya had'u over,

Yana parking ya fice baibi takanta ba,da sauri ta fito tabi bayansa,daidai shigarsa farlour ta cimmasa,"wai Yaya Lameer meke faruwa ne,banza ya mata ya zauna a kujera jikinsa ta fad'a tana tumurmusarsa,

Ta turo baki"me nayi maka ne,Jan kunnenta yayi ta saki k'ara ya matse mata baki,6oye fuskarta tayi a k'irjinsa,tace"don Allah na tuba,daman duk lokacin da yayi mata hakan tasan laifi tayi,

Yace"meyasa kunnen nan naki bayaji Zainab saunawa zan ce miki duk abinda ya faru tsakaninmu karki sanar da kowa,

Kwantawa tayi jikinsa cikin shagwa6a tace"mancewa nayi fa bazan k'ara ba ai kaga ban fad'a ba ko,cike da yarinta tayi maganar,jan hancinta yayi"to ai nasan badon Umma ta gobjemin bakin Babyna ba yau da tayi 6aran 6arama,dariya tasaka"ai bazan sake ba amma fa naji zafi,hura mata bakin yayi "tom sorry my luv,

Gyara kwanciya tayi jikinsa Yaya Lameer barci nakeji,yace"kinyi sallah ko,tace"nayi tare ma da Kaka mukayi kafin kazo,yace"tom asha barci lfy,ya gyara mata kwanciya jikinsa,shi kuma ya d'auki romote ya kunna TV tare da rage k'ara lokaci k'ank'ani barci ya kwasheta daman ita bata da wahalar barci,

Bedroom ya kaita ya shimfid'eta kan gado,tare da ja mata barko ya koma farlour

Muje zuwa yawan comment yawan typing


Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
         
          _**NI DA YAYA  LAMEER**_

                              ❤❤❤❤
                               🧡🧡🧡💓
*GAJERAN LABARI*


*Story and written*

*By*

*Fateemah Sununi Rabee'u*
*(Ummu Affan)*

         

________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇

 NI DA YAYA  LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144Diditated to my fans

Special gift to Anty Hauwa

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

🅿️5↪️6

Jin kiran la'asar yasa ya mik'e bedroom ya shiga,domin tada Ummi(Wato Zainab)ganin ankira sallah kuma koba haka bama barcin yamma ba ya da kyau,

Tafin k'afarta ya fara shafa mata a hankali,bud'e idanuwanta tayi tana ganinsa ta turo baki cike da shagwa6a,tace"nifa barcin nan bai isheni ba Yaya Lameer,kwa6e fuska yayi kamar yadda itama tayin yace"My Wife an kira sallah fa,mik'ewa tayi tana dire dare,

Kamota yayi yace"meye hakan Babyna,tace"ba kai bane kawai ina barcina,yace"tom sorry anjima zakiyi barci,muje kiyi sallah,

Haka suka shiga bathroom ya mata alwala yayi sannan ya kinkimota sai kan dadduma ya mik'a mata hijab,yace"to ayi sallah bari naje masallaci luv u so much,

MUrmushi tayi"luv u too Yayanah,kiss ya manna mata a goshi ya fice,

Bayan ta idar,cire hijab tayi ta nufi part d'in su Ammi tasan yanzu sun daw
o,

Taci sa'a kuwa a kitchin ta isketa tana had'a abinci,domin Ammi da kanta take girki bata yarda da sai 'yan aiki sun girka mata ba,saidai suyi wanke wanke da shara da sauran abinda ba'a rasa ba,

Tace"yauwa Ammina kamar kinsan yunwa nakeji,murmushi Ammin tayi,kasa uwar barci kin tashi kenan ai na lek'a Lameer yace kina barci,murmushi ita ma tayi,tace"na tashi Ammi,

Kallonta Ammi tayi,saikizo ki tayani girkin kema don nan gaba ki k'ware sosai,turo baki tayi gaba,ta fara kunkunai,tasan abinda Zainab bata so kenan aiki musamman girki,tace"kai Ammi banfa iya ba,

Tace da hakan ai zaki kowa,ba don son ranta ba ta fara tayata saidai duk shirme ne,daga k'arshe Ammi tace ta bari kawai,cike da murna ta koma farlour bayan ta had'a tea ta koma tanasha kafin agama girkin,

Da dare bayan anyi sallar isha'i wajen takwas da rabi gaba d'aya suke zaune kan dinning table suna cin abinci,

Zainab tace"Ammi fa kin iya girki,dariya sukasa tace"ai shiyasa nakeso kema ki koya don wataran ki yi da kanki,Lameer yace"haba dai Ammi duka nawa take da zata fara koyan girki tun yanzu,

"Kai rufe mana baki duk kai ke k'arasawa Ummi bata son koyan abu,yanzu idan bata koya tun yanzu ba sai yaushe ko so kake nan gaba kazo kana mana kukan bata iya girki ba,

Abbu girgiza kai kawai yayi yana murmushi yace"rabu da d'an tselan d'an nan naki nan gaba idan yazo yace haka ni nasan amsar da zan basa,cikin shagwa6a yace"kai Abbu yau harda kai,yace"eh hardani,

Tashi yayi ya sungumi Zainab ya sa6a yace"mu,mun wuce saida safenku,yayi gaba,bayan fitarsa suka saka dariya,Ammi tace"yau naga yaro,Alh kaga yaran zamani ko?,murmushi yayi"wannan ai ba sabon abu bane a gurinmu tunda,tunda cen yasaba tunkan ya aureta bashiyasa muka musu auran ba kar azo a wuce gona da iri d'an yau baka shaidarsa,tace"haka ne kam Allah dai ya shirya mana zuria,ya amsa da amin,

Bai ajeta ako inaba sai kan bed,turo baki tayi wanda na lura kamar hakan ya zamemata jiki tace"kai Yaya Lameer yanzun saboda tsabar mugunta don kar inci abincin Ammi in k'oshi ka d'akkoni,yace"duk uban abincin da kikaci nagafa har k'ari kikayi idan kuma kinason k'atun ciki sai in mayar dake kiyi tumbi,6ata rai tayi don bata son tumbi tace"a'a wllh na k'oshi,dariya yasa mata yace"da sai na dunga miki wak'ar me k'aton ciki,

Acikin haushi takai masa duka,nan fa yaruga sai suka dunga zagaye d'akin yana mata dariya,ta fa shak'a sosai sai ta duk'e tana kukan shagwa6a,"ni wllh bazan yarda ba,

Zuwa yayi ya duk'a,da sauri ta d'ane bayansa ta mak'alk'alesa tana dry,yace"yanzun kin rama ko,tace"a'a sai kayi juya-juya dani,nan fa ya fara juya juyar da ita saida tace ta gaji sannan tace"wanka zanyi Yaya Lameer,

"To muje namiki,tace"wllh bana so,chaf wllh bazan yarda ba kama fita idan nayi sai ka dawo,yace"shikenan nima bari naje nayi nawa,

Haka ya fita,tashiga bathroom tayi wankanta,sannan tazo ta jura doguwar rigar barci,wacce bata wuce gwiwarta ba,

Zata kwanta kenan ya shugo shima cikin shigar doguwar rigar barci ta maza,hannunsa faranti ne da ya yanko musu kankana daman kullum kafin su kwanta sai sunsha,

Haka tana zaune jikinsa sunasha suna hira,har barci ya kwasheta,tashi yayi,ya bayar da farantin kitchin ya kashe wutar farlour da kayan kallo,ya dawo,nan yaza mudu bargo,Asuba ta gari


Insha Allahu zaku jini anji,Ina sonku masoyana a duk inda kuke,sai mun had'e anjima😂💃Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
         
                *NI DA YAYA  LAMEER*

                              ❤❤❤❤
                               🧡🧡🧡💓
GAJERAN LABARI


Story and written

By

Fateemah Sununi Rabee'u
(Ummu Affan)

         

________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇

 NI DA YAYA  LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144Diditated to ATK

Special gift to Anty Hauwa

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

🅿️7↪️8


Wajen bakwai na safe tuni suka gama shirinsu,Wow zo kuga Yaya Lameer ya had'u sosai cikin shigarsu ta likitoci,

K'ananun kaya ne jikinsa ya d'aura rigar likitoci a sama,Zainab ko sanye take da kayan boko,wando Ash colour farar riga da tazo mata har gwiwa sai hura ash da tasaka hijabinta wanda iyakarsa k'irji,jan hannunta yayi zuwa farlour,turjewa tayi,tana turo baki gama,

Murmushi yayi yace"menene kuma?,hawaye ta fara tace"Yaya Lameer nifa baganewa nake ba mkrntar nan kawai karabu dani banson zuwa,

6ata rai yayi yace"Wai Zainab meke damunki ne sam bakisan karatu duk k'ok'arin da nake akanki gami da karatu kyanyarnan taki haka take kamar dussa,

Hawaye ta fara,ta koma kan kujera ta zauna tc"tunda haka kace ba inda zani,nan fa tafara kuka wiwi,numfashi yaja,yadawo kusa da ita yazauna tare da jawo hannayenta ya murja,d'agowa tayi ta kallesa,shima ita yake kallo,

Yace"Zainab bazaki fahimta bane kingani nan mutum ne meson ilmi amma ke nalura ba abinda kika tsana irin karatu tanan fannin bazamu shirya ba,Kaka ce tun farko taja miki da idan kince bazaki ba tace"abarki ni bazan laminci hakanba gara tun wuri ki bayar da hnkl akan karatunki JSStwo kike amma ace bakisan komai ba,

Zuba masa ido tayi ganin yadda yake ta masifa aranta tace"daman ka iya masifa haka,a fili kuwa kwa6e fuska tayi tana niyyar sakin kuka,

Jawota jikinsa yayi yana shafa bayanta,d'ago fuskarta yayi suna kallon juna yace"Zainab ina so kiyi karatu mai zurfi hakan bazai samu ba harsai kin tsayar da hankali gurin fahimtar me ake koya miki,

Tace"ai zanyi naga sai fad'a kakemin,yace"to Sorry na dena kice ai,gaba d'aya suka saka dariya,ya kama hannunta "zo muje muyi breakfast gurin Ammi mu wuce ko,

Tace"nidai ka goyani,duk'a yayi ta d'are bayansa,sai dariya suke,

Ak'ofar part d'in su Ammi ya direta suka k'ara,akan dinning suka iske Ammin da Abbu yana karyawa shima zai wuce office,

Bayan sun gaishesu suka zauna,suka karya,sannan suka musu sallama,Ammi tace"Ummi a mayar da hnkl a karatu kinji 'yata,tace"to Ammi,Abbu yace"to adawo lfy,tace"Allah yasa,

LAMEER duk'awa yayi gaban iyayensa yace"to Ammina nima asamin albarka,murmushi tayi kamar yadda suke kullum tasa hannu akansa ta masa addu'a,yace"yauwa Ammina nagode,ya manna mata kiss,yace"Abbu sai mun dawo,sannan ya kama hannunta suka wuce,

Murmishi sukayi gaba d'aya sukabi tilon d'an nasu da kallo cike da k'auna,

Sun fara tafiya ya juyo ya kalleta,ganin yadda tayi shuru,yasan duk sbd zata skul ne ita kuma ta tsani mkrnt,

Har cikin gate d'in mkrntar ya shiga kamar kullum bayan yayi parking,ya kalleta bayan ya ruk'o hannayenta yace"My Wife kiyi karatu sosai ko bakison zama likitar kamar ni,murmushi tayi,"inaso mana,yace"to dole saikinyi karatu sosai kin mayarda hankali,tace"to zanyi,kiss ya manna mata a d'an garamin bakinta yace"oya to sai nazo d'aukarki,fita tayi tana d'aga masa hannu ganin ta wuce ya juya,bayan yawa me gadin mkrntar alheri,

Wani kyakkyawan asibity naga yayi hune da sauri me gadin ya bud'e masa yana masa sannu,gurin da yake parking yakai motarsa sannan ya fito,cikin takun isarsa naga ya nufi ciki,da na d'aga kaina naga anrubuta

LAMZAH speacial hosbital,ganin yadda ya d'aure fuska kamar bashi ba yasa na fara mmk,sai sannu ma'aikatan asibitin ke masa mgn ma ta gagara sai d'aga hannu,wani kyakkyawan Office naga ya shiga,masha Allah kawai nace ganin yadda aka tsara office d'in,zama yayi ya fara dudduba fayil d'in da ke gaban teburin,

Daga bisani ya fara duba marasa lfy,

Waye LAMEER wacece Zainab sai a page nagaba zakuji.


Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
         
                *NI DA YAYA  LAMEER*

                              ❤❤❤❤
                               🧡🧡🧡💓
GAJERAN LABARI


Story and written

By

Fateemah Sununi Rabee'u
(Ummu Affan)

         

________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇

 NI DA YAYA  LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144Wannan page sadaukarwa ne ga Hussen Abu Sameer da Nuradden Shu'aib Light,Ina godiya sosai🙏


Masoyana ako da yaushe kuna raina ina yinku irin sosai d'in nan,Masu kirana nagode da soyayyar da kuke min masumin magana da pc kuma nagode sosai,NI DA YAYA LAMEER Fans ina godiya sosai da soyayyar da kuke nunamin nagode🙏

My bestyna Ummu Inteesar marubuciyar 'YAR GANTALI,Inayinki keda Maman khaleel marubuciyar KISHIYAR ZAMANI,i luv u wujiga-wujiga.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

🅿️9↪️10

Malam Halilu,wanda aka fi sani da Malam babba babban malamin addini ne,wanda ke zaune a garin Kaduna,tare da matarsa Gwoggo Abu,asalinsu 'yan jahar katsina ne a wani k'auye me suna,Dukke"dake k'aramar hukumar funtua,

Malam babba karatun addini ne ya kawoshi kaduna inda yazama babban malamin addini na ahlussunna,matarsa Gwoggo Abu duk 'yan gari d'aya ne,

Yara biyu suka haifa duk maza,Ibrahim ne babba sannan Ahmad,sunyi karatun addini sosai haka harna boko,don ba laifi mahaifinsu na k'ok'ari akansu,

Ibrahim babban d'an kasuwa ne wanda yanzun yayi kud'i sunansa ya shahara shi kuwa Ahmad Babban malami ne dake koyarwa a jami'ar kaduna,

Rana d'aya sukayi aure domin Allah ya d'aura musu k'aunar junansu,Hassana da Husaina suka aura,Ibrahim keda Hassana shi kuma Ahmad Husaina,

Babban gida suka gina nakece raini anan suka saka matansu,kuma suna tare da iyayensu,

Shekara guda da auran matar Ibrahim ta hauhu wato Hassana,ta sami d'a namiji zo kuga murna,gsky sunyi farin ciki da samun k'aruwar nan,nan akayi ta murna da farin ciki ranar suna yaro ya amsa _LAMEER_ Yaro kenan d'an gata gurin iyayensa da kakaninsa haka Ahmad da Hussaina suna k'aunar Lameer part d'insu yake wuni,

Tunda aka haifesa ba ak'ara haihuwa a gidanba,ita dai Hussaina ba lbr da yake suna da ilmin addini sai suka mik'a al amuransu gurin sarki Allah suka dage addu'a,

Shekarun Lameer goma amma ba wani lbr shima iyayensa basu kuma haihuwa ba tundaga kanshi,

Makaranta me tsada yake zuwa,tun yana yaro shi d'in mai hazak'a ne baison wasa da karatu,kyakkyawa dashi ga miskilanci da jan aji kamar wata mace ko a class bai cika mgn ba wasu suna masa kallon mai girman kai shidai haka Allah yayisa baison surutu,

Bayan kammala primary yaje secondry,yana SS3 aka haifi Zainab,wato Ummarsa Hussaina ta haihu kamar yarda yake kiranta,Anyi farin ciki da haihuwar nan bama kamar Lameer,tunda aka haifeta yana tare da ita,haka nan yaji Allah ya d'aura masa k'aunar yarinyar,

Ranar suna taci Zainab,sunan Gwoggo sai iyayen ke kiranta Ummi,Lameer yace Zainab Kaka da Malam babba suce Abulle,

Zainab kenan yarinya mai k'iriniya kamar ba haihuwar gari ba,haka Allah ya halicceta sakaryace ta k'arshe,gaba d'aya halayenta irin na k'auyawa ne kuma ita d'in haihuwar gari ce,

Kaka wato Gwoggo tana tsantsar k'aunar jikar tata musamman da taci sunanta,bayan kammala secondry d'in Yaya Lameer yaci gaba da karatunsa a Kaduna university,mahaifinsa a waje yaso yayi karatu amma yace bazai jeba sbd Zainab,

Wacce sukayi sabo sosai,be bari Umma tawa Zainab komai shi ke mata tundaga kan wanka shafa sa kaya tsifar kai komaidai shi ke bata,

Lokacin da Ta isa shiga makaranta akasata,sai tayi ta kuka ita bazata ba,Kaka tace tayi zamanta,sai ta had'u da yaran unguwa ayi ta shirme,

Lameer duk baisan da hakanba kasantuwar karatunsa da yayi masa zafi kunsan karatun likitoci akwai wahala,

Akwai wata budurwa da suke karatu tare,tana mugun sonsa duk wata hanya da tasan zatabi saida tabi har Lameer ya fara kulata,KHAIRAT tana matuk'ar k'aunar Lameer kaiba ma itaba 'yan mata da yawa na kai masa hali Amma shi,baya kulasu,

Haka suke binsa kamarme,duk mkrntr Khairat kawai yake kulawa itama don tazomai a mutuniyar arziki ne da sunan karatu kawai zata dunga koya gurinsa,

Zainab bata son karatu sai yawo gidajen k'awaye abin na damun Babanta yasami yayansa sukai mgnr gurin Gwoggo sukaje suka sanar mata nan ta fara bala'in abar yarinya ta sakata ta wala,

Haka sukaci gaba da hakuri da halin Zainab yau taje gobe bata je ba,

Lkcn da Lameer ya gano abinda ke faruwa nan ya fara takurata,suyi fad'a wataran su shirya,

Yadawo da kansa yake kaita skul ganin hakan sai sam bata mayar da hankali tayi abinda ya dace,

Lameer yana matuk'ar k'aunar Zainab da kansa yasanar da Kakansu Malam babba nan take yace ko bayan ransa abawa Lameer auran Zainab,duk abinda Zainab zatayi Lameer baya ganin laifinta ta fannin mkrnt ne kawai suke samun matsala,

Dukkan mai rai mamaci ne Allah ya amshi rayuwar malam babba sunyi kukan rashi sosai,haka mutane domin malam babba mutumin arziki ne yasami yabo saidai fatan Allah ya kyautata makwanci,Gwoggo tayi kukan rashin miji adali,da haka akayi zaman makoki,

Lameer bayan kammala karatunsa,Abbu ya gina masa babban asibiti aka zuba ma'aikata,shi dakansa yasawa asibitinsa suna LAMZAH wato Lameer da Zainab,

Muje zuwa

Karfa kudamu nasan kun k'osa kuji taya akayi wnn auran nasu karda ku damu zakuji😉😂
Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
         
                *NI DA YAYA  LAMEER*

                              ❤❤❤❤
                               🧡🧡🧡💓
GAJERAN LABARI


Story and written

By

Fateemah Sununi Rabee'u
(Ummu Affan)

         

________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "NI DA YAYA LAMEER page 1 to 10"

Post a comment