Results

NI DA YAYA LAMEER page 21 to 30

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇

 NI DA YAYA  LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144Diditated to ATK

Special gift to Anty Hauwa

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

🅿️21↪️22

Gudu kawai suke shararawa akan babban titin gaba d'ayama fita sukayi daga cikin garin kaduna,

Wani k'auye suka kaita me suna Fanbeguwa,acen suke da wani gida babba cike suka kaita har zuwa lokacin Zainab batasan meke faruwa ba,

Boss suka kira a waya ya fito daga cikin gidan,kallon yaran nasa yai yasaka dariya hhhhhh ban ta6a baku aiki ba aka sami matsala ina alfahari daku,

Sara masa sukai suka had'a baki,"muma muna alfahari dakai megida,

Murfin bayan motar suka bud'e masa inda Zainab ke kwance kamar meyin barci,murmushi yayi ya d'auketa sak sai cikin gidan,

D'akin dake gidan ya kaita kan wata katuwar katima ya shimfed'eta,murmushi yai yace afili"Zainab bazan kasheki ba kamar yadda Khairat ta buk'ata domin tun ranar da ta nunamin ke naji ina k'aunarki shiyasa na za6i in kawoki nan domin inyi yarda nakeso dake,ke tawa ce har abada ba wanda zai sae jin d'uriyarki,yasaki dariya hhhhhhhhhh sannan ya koma farlour,

Kud'i yabawa yaransa masu yawa sannan ya musu godiya,suka fita daman su Acen Kaduna suke,amma idan yasasu aiki ko inane suna xuwa,

Wajen k'arfi biyu na rana Zainab ta farko,ahankali ta fara bud'e idanuwanta saman d'akin ta kalli ta juya idanuwanta zuwa ko wanne sassa na d'akin,a furgice ta tashi zaune abinda ya faru ne ya fad'o mata,Yayaaaaa Lameerrrrrrrrrr,ta ambata da k'arfi,

Daidai lokacin kuma Lameer ya rik'e saitin zuciyarsa,a hankali ya furta Zainab,sai kuma yaji gabansa na fad'uwa,

Boss ne ya shugo d'akin da sauri,ya gigice ta mik'e tana zare idanu,yace"Zainab lafiya aii daga yau nine na koma Yayanki ki mance da wancen kinji ko kizo muji dad'inmu,gadagadan yayo kanta,

Da sauri taja baya tana hawaye tace"waye kai?don Allah kayi hakuri kamayar dani gurin Yayanah,dariya yasaka yace"ai kuma ke da yayanki kun rabu kenan,kasheki akasa fa nayi amma saboda ina sonki yasa ban kasheki ba,don haka kibani had'in kai,zan mayar dake 'yar lele muji dad'inmu ko?ya k'arashe maganarsa da tambaya,

Runtse idanuwanta tayi da k'arfi hawaye nabin kuncinta ita bamafa tasan inda mgnrsa ta dosa ba,tace"don Allah kayi hakuri kamar dani cikin ahlina,

"Duk irn son da nake miki bazan yarda nayi gangancin nan ba kinsan ma wacece Khairat waye ubanta?,girgiza kai take tace"ni wad'an tambayoyin naka sun girmi kwanyata a makaranta ni banacin jarabawa kaga tambayoyinka zasu iya kassara kwanyata don Allah kayi hakuri kamar dani gurin Yayanah,

Funcikota yayi saigata jikinsa k'arata kwalla da k'arfi,bai damuba yace"wllh tunda nayi sha'awarki to sai na d'and'anaki,kuka sosai Zainab keyi nan fa suka fara danbe,

A 6angaran Lameer daidai lokacin yaga ya mik'e tsaye,a fili ya furta "Zainab duk yadda akayi ba lafiya meke damunki Zainabuna,komawa yayi ya zauna sai kuma yasake mik'ewa,ganin dai hankalinsa ya kasa kwanciya key ya zara ya nufi skul d'insu,

Me gadi na ganinsa gabansa ya buga,ckn fara'a Lameer ya gaishesa kamar kullum harda basa ihsani 'yar kyautar da yasaba masa,jiki a sanyaye ya amsa,sai yanzu yake da nasanin abinda yawa me kyautata masa a lokacin tunanin ya fad'awa shugabar mkrntr bai zo,masa ba,

Cikin harabar skul d'in Lameer yayi parking kamar yadda yasa ba,da kansa ya fito,don ganinta kawai yakeson yayi yawuce tunda lokacin tashi baiyi ba sai shidda,

Kamar daga sama saiga Hafsa k'awar Zainab tace"lah yaya lameer ina wuni,cikin fara'a ya amsa mata don duk abinda Zainab keso shima yanaso don ta ta6a fad'a masa duk cikin skull bata da kamar Hafsa,

Tace"tun da safe da aka mana break kazo gurin Zainab har yanzu baka dawo da itaba haran wani abunne ya faru,har aka koma class muna zuba ido bamu ganta ba,

Take gabansa ya buga da k'arfi annurin dake fuskarsa ya kau,yace"ni kuma ai duk yau banzo makarantar nan ba,cike da mamaki ta kallesa tace'aikuwa Baba me gadi ne yazo yace kai ke kiranta da sauri ta fita kuma har yanzu bata dawo ba,

A rikice ya juya gate ya nufa,baba me gadi na ganinsa gabansa yasake faduwa cikin yak'e yace"me gida har kafito,"Ina Zainab?abinda ya iya furtawa kenan,nan take jikin me gadi yahau rawa,ganin zai masa inda inda yashak'e wuyansa,Ina Zainab ya sake tambayarsa,

Nan take fa d'alibai da malamai suka fara taruwa,akaje aka sanarwa shugabar makarantar da kanta tafito,har lokacin me gadi ya kasa mgn,itama tambayarsa take abinda ya faru yak'i mgn,

Wata shak'a da Lameer ya masa ai ganin yana niyyar kaisa lahira da sauri ya fad'i abinda ya faru yad'aura dacewa"bindiga da wuk'ak'e suka nunamin shiyasa na tsorata,hawaye ne kawai ke futa fuskar Lameer yayin da kowa dake gurin yayi suranda.......

MUJE ZUWA💃💃

Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
         
                *NI DA YAYA  LAMEER*

                              ❤❤❤❤
                               🧡🧡🧡💓
GAJERAN LABARI


Story and written

By

Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

         

________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇

 NI DA YAYA  LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144Diditated to ATK

Special gift to Anty Hauwa

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

🅿️23↪️24


Sakin wuyan mei gadi yayi ya nufi motarsa da sauri,key ya mata ya fuzgeta,gudu sosai yake akan titi har Allah ya kaisa gidansu Khairat,

Yanayin yadda yake hun ma kawai ya'isa shaidar isowarsa,da sauri meigadi ya bud'e duk a tunaninsa Khairat ce kartazo ta shuka masa rashin mutumci,

Yana parking ya fito,a fusace yanufi cikin gidan,babu batun ya tsaya a masa iso,

Su kansu suna niyyar fitowa sukayi kici6us dashi domin irin hun d'in da'ake ya basu mamaki,fitowa sukayi suga wanne me tsaurin idon ne,don Khairat tana gida bata fita ba,

Kallon kallo sukawa juna,cikin dakakka zuciya irin tasa da garaje yace"me kake dasuna Alh Kamalu ko me,to inaso kasani wllh idan baka fitomin da mata ba duk wulak'ancin da na maka kai kaja,yinzun nan nakeso ka fito min da mata,

Kallonsa yayi sannan ya kalli Khairat,juya fuska tayi tanaci gaba da taunar cingam,

Gabanta Lameer yazo ya kalleta sama da k'asa sannan ya tofar da yau gefe yace"koda mata sun k'are bazan ta6a dubanki ba balle har nace zan soki natsaneki Khairat banta jin zan iya sonki ba balle na aureki,ku futomin da matata kafin na kassara rayuwarki,

Hawaye ne ke zuba afudskar Khairat tace"Lameer ban ta6a son wani a duniyata ba saikai meyasa katsaneni ni ba mace bace ko ya kad'auke ni,meye ajikin wannan 'yar ficiciyar yarinyar da kake mgn nidai nasan ba'abinda zata nunamin saidai na nuna mata kum.....

Wani kyakkyawan marin da ya zuba mata yasata yi shuru ta rik'e kunci da sauri,Alh Kamalu yayo kan Lameer d'aga masa hannu yayi yace"karka kuskura kazo kusa dani don kai zan maka abinda yafi na Khairat,chak ya tsaya sai kuma ya fara fad'a,

"Wannan wanne irin cin mutumci ne kaxo har cikin gidan ubanta ka mareta wallahi jami'an tsaro zan kira maka,

Yace"ai hakan nakeso maza ka kirasu,wallahi sunanka yana hanyar 6aci daman kai 6ataccen ne,komai dakakeyi nasan komai wllh sai na tona maka asiri matsafin banza namana da na Matata yafi k'arfin kaci idan ma dodonka kakaiwa Matata maza ka dawomin da mata kafin sunanka yanzu ya fara zagaya gidajen tv radio da jaridu nasan kasan koni waye,tabbas ni likita ne amma ina da abokanai 'yan jaridu da yanzu idan nabasu kanun labarai zasu yad'ashi duniya taji damansu kullum jira suke su sami kanin sabun labarin dazasu yad'a duniya taji,

Takefa jikin Alh Kamalu  ya hau rawa,bai ta6a sanin yaron nan yasan komai gami dashiba,yace"Ni bansan komaiba gami da 6atan matarka wallahi ban sani ba,

Hjy Luba taja tsaki"wai Alh meye haka jikinka yake rawa akan wnn 'yar barazanar tasa,kallo Lameer tayi tace"idan baka yad'a ba baka haihuba don ubanka,

Kafin ta rufe baki yasakar mata wani zazzafan mari,ai nan take jinta da ganinta ya d'auke na wucin gadi,cen na hango luba ta xube gefe guda,

Duk'awa yayi saitinta yace"ke tsohuwar kilaki nifa wanda baiba kansa girma baija girmansa maganinsa nake,ke har zaki zageni kada ku fitomin da mata kuga abinda zai faru ki kuka dakanki,

Mik'ewa yayi ya kalli Alh Kamalu,"Ina MATATA,rantse-rantse yakama "wallahi tallahi bansan inda take ba,

Kallon Khairat yayi wacce fuskata kumbura tayi jawur sbd marin datasha kunsan meyin bilicin nan take fuskar tayi wani ja,

Yace"tana ina,shuru tayi,matsowa yayi kusa da ita,ganin zai sake marinta tace"nifa ban sani ba,

********

Zainab da Boss sosai suke danbe,ganin yarinyar ta burkice masa kamar me aljanu yasa yarabu da itayace"nabarki yau amma gobe wllh duk tsiyarki sainasha romanki,

Ta murgud'a baki tace"la'ananne d'an iska Allah bazai baja sa'a ba,Kanta yayo "wakike zagi,

Daram ta tsaya tare da rik'e k'ugu tace"an zagekan wallahi ka k'araso gurin nan sai kaga abunda zai faru d'an iska kawai wllh kayi asara dai,

Tsayawa yayi yajasa k'arasawa aransa yace"anya yarinyar nan ita d'ayace,duba da danben dasukasha shi duk yagaji itako ko alamar gaji babu atare da ita gashi yadda take masa magana kai tsaye kamar mai iskokai,

Dariya tasaka tace"uhmm harnaga yadda zan gullisuwa da wani a gurin nan,zakutayani ko?naga tana kallon gefe,tana jujjuya idanuwa,ai da gudu boss ya fita yana al'ajabi wannan yarinyar anya mutum ce,

Bayan fitarsa dariya tasaka tace"matsorancin banxa kawai wallahi zanyi maganinka kaibaga d'an iska ba,

..........................................

Lameer ya galla mata harara"zaki fad'amin gaskiya ko yanzu saina illataki,kuka tasaka"ni wallahi bansan inda aka kaita ba,

Juyawa yayi yabar gidan,yasan maganinsu,baiso itayensu suji wannan abunba yaso ne kawai ya magance matsalar nan da kansa,yana zuwa ya tadda su Ammi basa nan,tunowa yayi da maganar da sukayi da Ammi da safe inda take cewa"Lameer idan ka d'auko Ummi kuwuce gidan Malam yaucen zamu wuni sai dare zamu dawo,

Juya motarsa yayi sai gidan Kakar tasu,

Iskesu yayi suna da hira cikin raha,ganin yanayin da ya shugo yasa Ammi tace"Lameer lafiya kuwa?,Umma ta dafe k'irjinta tace"wani abu yasami Ummi ko?tun safe gabana ke fad'uwa abu kad'an saita fad'omin arai,

Zama yayi,baice musu komaiba saida ya kira Abbu da Baba,domin yasan halin mata yanzun samayar da gidan na mutuwa😜,

Bayan yasanar kuwa ilai nan Kaka Ammi da Umma sukahau kuka,damansu mata raunine garesu duk girman mace kuma duk tsufanrta haka duk yarintarta raunine da ita,

Abbu ya Mik'e ransa 6ace yace "wllh sai nayi maganin Alh Kamalu zai gane ruwa ba sa'an kwando bane,siyasarshi ta banxa nikeda 'yan siyasa duk da banayi zai gane ya ta6o 'yar gata.......


My Mumcyna Ameenat Ibrahim Meenat ina miki fatan alkhairi tare da addu'ar Allah ya baki lafiya ya raya mana Hassana da Hussaini Ameen,


Muje zuwa😂


Ummu Affan✍️✍️✍️

❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
         
                *NI DA YAYA  LAMEER*

                              ❤❤❤❤
                               🧡🧡🧡💓
GAJERAN LABARI


Story and written

By

Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

         

________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇

 NI DA YAYA  LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144Diditated to Fans

Special gift to Anty Hauwa

_Masu cewa na turo musu daga farko har k'arshe don Allah suyi hak'uri na fad'a muku wnn book d'in sabo ne sai nayi typing snn nake turowa don Allah kuyi hkr ni bakina har ya gaji da wnn mgnr,idan na kammalasa duk meso xan turo masa amma yanzu nake typing d'insa da ftn masu tambaya zasumin hkr hakan harna kammala_


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


🅿️25↪️26


Fita Abbu yayi yana waya,dame girma gwamna domin babban abokinsa ne,tare sukayi karatu,

Duk wanda ya dace yasanar mawa,zuwa wani lakaci,jahar Kaduna ta d'auka gidajen tv da redio cewa Senator Alh Kamalu ya saci 'yar wajen,Babban d'an kasuwarnan Alh Ibrahim Halilu babba,

Zuwa wani lokaci matune sunfi d'ari sun taru a k'ofar gidansa suna "bamayi"bamayi,a fiddo mana da yarinya,

Hankalin Alh Kamalu yayi mugun tashi haka Hjy Luba,Khairat kuka kawai take,Dad d'inta yace"Khairat idan ke kika d'aukar musu 'ya ki rufamin asiri ki fiddota kafin wnn mutanen su shugo sumana duka,

Tace"Dad yanzu me kake nufi kana nufin bazaka bani Lameer ba kasan shine frn cikina,idan har baka bani shiba wllh xan kashe kaina babu abinda nata6a saka kayimin bakayimin ba sai wnn karon duk wani abinda nakeso ko ba naka bane sai kayi yarda kayi na samesa me yasa ka kasa samomin soyayyar LAMEER?,

Numfashi yaja yace"tunda har kinsan kome kika nema ina iya bakin k'ok'arina na samar miki to kiwa Allah ki fito musu da 'yarsu wllh abin nan yana iyasa na rasa muk'amina,ni danake nema nan gaba na zama gwamna kinga wnn abun zaisa na rasa,

Kuka sosai tasaka "ni wllh sai na auri Lameer ko kuwa na kashe kaina,Hjy Luba ta rik'e d'iya tata tace"Khairat kiyi hkr ni zan miki abinda ubanki ya kasa miki ko zanyi yawo tsirara sai na nemo miki soyayyar Lameer,

Kallonsu yayi cike da takaici yace"Luba baki da hankali meye kike cewa haka baki tunanin yadda rayuwarmu zata koma idan narasa muk'amin nan,kinsan bani dashi ban ajeba ban ba wani ajiya ba,duk kud'in gwamnati dashi muke komai wllh ranar da asirinmu zai tunu muna cikin garari,

Tsaki taja mtsuuuww "kaidai tunda ka kasa ni zanyi ta kama hannun Khairat sukayi ciki,

Shi kuwa ya kasa futa sai tunani yake kar su k'ona masa gida,

******************

A hankali ya lalla6o duk a tunaninsa Zainab barci take sai sakin murmushi yake,ya hayo kan katifar a hankali,ya fara shafa bayanta yana lashe le6e da had'iyar yawu,

Cikin barcinta wanda ba sosai ya d'auketa ba takejin kamar ana shafata a furgice ta tashi tana salati,turesa tayi tantan k'arfinta kunsan abinku ga sauran sigari ba wani k'arfine dashiba,nan ya wuntsila,

Mik'ewa tayi tace"waikai wanne irin maye ne?,me jikina ya maka?wllh zan kassaraka yanzun nan,

Rarume-rarume ta kama kamar wata mahaukaciya sabon kamu,kome ta samu ta jefa masa,

Shima a fusace ya mik'e yace "wllh duk haukanki yau nima zan nuna miki mahaukacin kaina ne yau duk tsiyarki sai nasami abinda nakeso a jikinki,tace"chaffff wllh ni dakai shege ka fasa d'an halak sai yanka,kujimin katon banza mahaukaci d'an shaye-shaye anya kuwa iyayenka basu cemaka jeka ka gani ba?,

Yace"maganarki hakkun haka take hakan yasa dole yau na san abinda ya yaga ajikinki,tace"to zo gani sai kayi mugani,

Yadda kawai take kallonsa abin sai ya baka mamaki,hakan yasa ya juya yace"zamu had'u ne,

Bayan fitarsa jagab ta zauna kankatifa tare da rik'e kanta,meke shirin faruwa da rayuwarta?hawaye ne kebin fuskarta daman haka rayuwarnan ta koma,sai taji jikinta duk yayi sanyi Yaya Lameer Umma Baba,Abbu Ammi da Kaka kawai take tunani,

Snn makaranta ta fad'o mata yadda take rayuwa da kowa,K'awayenta Hafsa da Maryam,malamanta da ta raina ta mayar dasu kamar wasu abokanan wasanta,

Hawaye yazubo mata ta share "Allah sarki yayanah me sona dason nayi karatu,gashi yanzu inason nayi karatun babu hali,yayanah kazo ka tafi dani kar mutumin nan ya kassara rayuwata,ta fashe da wani kuka mai ban tausai,

Daidai lokacin fitowar Yaya Lameer kenan daga masallaci,tunda abon nan ya faru ko aiki ya dena zuwa kullum tunaninsa Zainab d'insa,

Kwantawa yayi saman bed d'insu dasuke kwana shida Zeey d'insa ya k'amk'ame zanin gadon yana shinshinar k'amshin zeey d'insa yanzu shi kad'ai yake kwana bayajin d'umin jikinta hawaye suka xubo masa,da sauri ya mik'e key ya d'auka bai zame ko inaba sai gidansu Khairat rashin sa'ar da yataka yana zuwa me gadi yasanar masa ba kowa gidan sun fita,

Juyawa yai cike da 6acin rai,ransa na suya,

.........................................................

Zainab ce shuru tana tunanin me yadace tayi,wani tunani ne ya fad'o mata,alwala tayi bayan ta idar da sallah ta cire hijabin makarantar daman kullum dashi take wuni dashi take sallah,batayin wanka sai ta tabbatar boss yafita tunda akwai toilet d'akin da take kuma akwai fanfo,

Ko tayi wankan kayan jikinta na mkrnt take mayarwa,wnn tunanin ya fad'o mata yasa tace"ko wacce mace da irin kissarta nasan maganinka insha Allahu yau sai na koma gurin ahlina,

Zaune ta iskesa a farlour,da sauri ya mik'e ganin yadda ta taho gabansa tana wani rausaya da girgiza........

🤣🤣🤣
_Shin me Zee zatayi?kai nimafa zanso nasha kallo😉😜_

_Nasan Ummu Inteesar nacen na tunanin tome kishiyarta zatayi hhhhhhhhhhhhh_

_Mu had'e a page na gaba donjin ya zataci gaba da kayawa acikin littafin nan nidai burina kuci gaba da biyoni sannu a hankali har ku fahimci abinda nake son isarwa_

_MUJE ZUWA_


Ummu Affan takuce masoyana nah✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
         
                *NI DA YAYA  LAMEER*

                              ❤❤❤❤
                               🧡🧡🧡💓
GAJERAN LABARI


Story and written

By

Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

         

________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇

 NI DA YAYA  LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144Diditated to yaran albarka AHMAD(Affan),ABDULRAHEEM(Haneef)and AYSHA(Ikhram)Allah ya rayamunku bisa tafarki nagari ku da sauran yaran al-ummar musulmai amin😂

Special gift to my yayu na gari Anty Sadeeya,Anty Aisha,and my k'anwa Jameela😜🤣

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

🅿️27↪️28


Tana k'arasowa tace"me hakan ya naga ka mik'e,zaunawa yayi yana cigaba da kallonta,kusa dashi ta zauna warin da taji da hamami natashi jikinsa yasa ta kauda fuska sai kuma ta basar tace"na yarda xan baka abinda kakeso ajikina,

Ai da sauri ya kaimata wata chakuma,ta dakatar dashi,tace"ni ba hauka nace kamin ba ina da sharad'i idan ka amince to saina yarda dakai,

Da sauri yace"ki fad'i ko meye zan amince idai kema zaki amince da abinda nakeso,tace"karkaji komai nama amince,

Yace"to inajinki fad'i abinda kikeso nayi,tace"ba komai bane daman inason shiga kasuwa ne akwai abinda zan saya idan har zaka kaini ni kuma damun dawo zan baka abinda kakeso,

Shuru yayi zuwacen yace"ki fad'i kome kikeso ni kuma dakaina zan sayo miki,gabanta ne ya fad'i karfa abinda take niyyar d'aurawa ya kwance,tace"a'a ni dakaina nakeson zuwa ai bance ni kad'ai zani ba tare dakai zamu fita,numfasa wa yayi yace"shi kenan babu damuwa kije ki shirya sai muje,

Mik'ewa tayi gabanta na fad'u don ba k'aramin k'arfin hali tayiba,donma kar yace'wani abu cikin kayan da yasayo mata bata ta6asa ko d'ayaba ta d'auki wata doguwar riga,tasaka,ta yane kanta da kallabin rigar,ta dad'e zaune sannan tayi k'undun bala ta fito,

Shima ya cenza kaya,amma da ka kallesa abin ba tsari,murmushi yasakar mata,itama yak'e tayi yazo yakama hannunta suka fita,ya bud'e mata mota ta shiga,sannan shima ya shiga yana ta sakin murmushi yaja motar sukabar gidan..

*****************

Hjy Luba ta kalli k'asurgumin bokon da suke zaune gabansa bayan ta gama fad'a masa komai ta d'aura da cewa,boka inaso kayi min aikinda ko uwarsa sai yamanta da ita bare wata matarsa kasa duk duniya yajibaya k'aunar ko wacce mace sai 'yata Khairat,

Buge-bugensa ya fara da surgullansa,wata k'warya ya d'akko me ruwa yaciki yace"kalli nan,cikin muryarsa mara dad'in sauraro da sauri ta kalla,fuskar Lameer ta hango cikin ruwan yace"shine wnn,da sauri ta gyad'a kai"k'warai shine,wata muguwar dariya yasaka snn wacce saida dajin gana d'aya yad'au amsa kuwwa ya ajeye k'waryar yace"wnn yaron da kike gani tun yana yaro an wankesa da addu'o'i da rubutun addu'o'i don haka yana cikin tsari snn ko da yaushe yana cikin ibada aikinmu bazai yi tasiri akansaba don yanzu hk na aika aljanu amma sun dawomin a waharce asiri bazai kamasa ba,

Khairat taja wani mugun tsaki tace"mum tashi mubar gurin nan wannan baisan aikinsa ba,rik'eta mum tayi amma ta fincike hannunta tace"idan bazaki tashiba mi xan wuce kema kya kawomi gurin irin wanda basusan aikinsu ba ni mai aiki kamar yankan wuk'a nakeso kikaini,

Mik'ewa Hjy Luba tayi tace"boka sai anjima,dariya ya kece da ita yace"duk gurin wanda zaku abinda na gani shizai gani saidai yamuku k'arya don yaci kud'inku,ke kuma da kika gaya mana mgn aljani d'an kilu ya fusata don haka zaki gani,yasake kecewa da dariya yana cewa "zaki gani"zaki gani"zaki gani"hhhhhhhhhhhhhhhh 6at ya 6ace,

Hjy luba tace"kin ganiko kinjawa kanki wannan bokan da kike gani k'asur gumin bokane,duk wani aiki danake sa sa yanamin wnn tunda kikaji yace hk to akwai matsala,

Tace"kinga mum zo muwuce shine zai gani matsiyacin boka kawai,haka suka wuce suna tafiya hjy luba na waige don yasiin ta tsorata,😉

*************

Alhj Kamalu ne yadawo daga wajen tsafinsa,sai kaiwa yake da komowa zucoyarsa ji yake kamar zata tarwatse,abinda dodonsa ya fad'a masa ke masa amsa kuwwa,"Kamalu watan da dodo zaisha jini ya tsaya don haka jinin 'yarka Khairat nake buk'ata hakan zaisa kaci gaba da samun nasara kud'i kuwa saidai aganka dasuuuuuuuuuuuu"

Toshe kunnansa yayi hawaye nazuba,duk duniya babu abinda yakeso da kauna sama da 'yarsa khairat meyasa bai za6i wataba a danginsa ko mutanan gari sai tilon 'yarsa abin sonsa ita kad'ai ya mallaka kuma yasan bayan ita bai k'ara haihuwa domin tuni aka masa abinda bazai k'ara haihuwa ba,don a tsarin dodonsu kowa haihuwa d'aya zaiyi,kuka yake sosai yana tausayin kansa a haka Hjy luba da Khairat suka iskesa,

Hjy luba ta fara tambaya "Alh lfy me ya faru kake kuka haka kamar k'aramin yaro?,

K'amk'ame Khairat yayi yanaci gaba da kuka,turesa take "Dad lfy meye hakan?,sakinta yayi yana share hawaye,yace"babu komai,kallonsa sukayi amma ganin baice masu komaiba sai suma suka sharesa,

................................................

"Haba Lameer meyasa zaka saka damuwa irin haka aranka kazama wani iri kamar ba Lameer jarumi me karsashi da jarumta ba,tabbas muma abin nan nadamunmu domin 6atan mutim bashi da dad'i 6atan mutum sai kace 6atan takalmi amma fa dolene kayi hakuri tunda iyayenku meye basayi kullum sai an sauke Qur'ani me girma ga addu'o'in da akasa,manyan malamai nayi ga wanda mukeyi insha Allahu an kusa ganin Zainab jikina na bani Ummi na kusa damu,

Umman Zainab ce ke wa Lameer wnn mgnr,numfashi yaza sai kuma ya mik'e baice komai ba,Ammi ta girgixa kai tace"Husaina dama kin barsa kullum cikin haka  muke da yaron nan amma ko kulani baiyi,Umma taja numfashi kawai tare da tagumi,

Bayan sun iso kasuwar k'auyen yace"To wanne guri zai kaiki,kallomsa tayi tare dajan numfashi tace"uhmm uhmm,da sauri ya kalleta cike da rashin yarda yace"uhmm me?tasaki wani murmushin k'arya tace"naga banga shagon siyar da kayan kwalliya bane,yace"nima ba sanin k'auyen nan sosai nayi ba yanzu ya za'ayi,

Kalle kalle ta fara sai tace"to ko zaka fita kayi mana tambayane,yace"ok haka ne bari nayi tambaya ina zuwa kawai ya fice.........Wallahi yau da kamar bazanyi ba,😏😏
Amma gashinan kunsan ance jiki da jini sai a sulo yaudai haka nakejin jikin nawa sai a hankali don Allah kusani a addu'a,


Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
         
                *NI DA YAYA  LAMEER*

                              ❤❤❤❤
                               🧡🧡🧡💓
GAJERAN LABARI


Story and written

By

Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

         

________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇

 NI DA YAYA  LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144Diditated to Fans

Special gift to Anty Hauwa

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

🅿️29↪️30

Tana ganin ya fice,itama ta sad'ad'a a hankali ta bud'e murfin motar ta fice da sauri,

Sauri-sauri take tafiya,ganin kamar yana binta tasaka gudu,yana dawowa yaga bata ciki gabansa ya buga,keiiii!ya furta a gigice,da sauri yabi bayanta,yana ta waige-waige amma kome kama da ita bai gani ba,cike da takaici ya koma gurin motarsa,

Ita kuwa Zainab babban titi ta koma duk motarda tagani sai ta fara d'aga hannu tana tsayarwa kamar wata mahaukaciya,haka motoci sukai ta wucewa sunk'i tsayawa,duk'ewa tayi a gurin tana kuka sosai don gani take boss ya kusan zuwa inda take,ji tayi ana danna mata wanu uban hune,a furgice ta d'ago zuciyarta na raya mata shi kenan tata ta k'are tunda boss ya isu..

Saleem shine aminin Lameer wanda suka taso tun lokacin k'uruciya tare sukayi karatunsu,ba'abinda Saleem bai sani ba gami da gidansu Lameer shima Lameer d'in yasan komai na gidansu Saleem domin dukkansu kai tsaye suke shiga gidan iyayensu,shima Saleem Doctor ne,

Lameer yace"me kake cewa?,kallon aminin nasa yayi cike da tausayi yace"yanzu duk uban surutun nan da nayi cewa zakayi bakaji abinda nace ba,sosa kai Lameer yayi yace"uhmm wllh Saleem tunda abin nan yafaru nifa kallon mutane kawai nake mgn ma ba damuna tayi tunani duk yana gurin halinda k'anwata take ciki,

Saleem yace"ai hkr ya kamata kayi wnn ma wata jarabawarce ta Allah sai kayi hkr kaci jarabawa,yace"hakane,Saleem yace "daman Jos nace maka zani akan mgnta da Hannah iyayenmu sun matsa ita sukeson na aura,kasan d'iyar yayan Abbanmu ce zanje zance tunda a Jos suke da zama,Lameer yace"kamusu biyayya sai kaga al'amuranka na tafiya ta daidai bare Hannah batada wata makusa,bazan iyaba da na rakaka,

Saleem yace"na sani ni daman bance ka rakani ba bari na wuce don a yau insha Allahu nakeson dawowa,

Har bakin motarsa ya raka sa yamasa fatan alkhairi snn ya juya,girgiza kai Saleem yayi cike da tausayin aminin nasa snn ya ja motarsa ya wuce,

To akan hanyar dawowar Saleem daga Jos,tundaga nesa ya hango ta tana d'agawa moto hannu har zuwa lokacin da ta zube tana kuka,bai ta6a kawowa Zainab bace har ya wuce ya dawo don tabasa tausai besan meyasa tayi hakamba don hk ya dawo da niyyar temaka mata yasakar mata hun,

Shinefa ta d'ago agigice a tunaninta boss ne,ganin ba motar boss bace yasa ta taso da gudu ta bud'e tace don Allah bawan Allah ka temakamin Kaduna zani,

Jin kamar muryar zainab yasa yace"Ummi,a d'an gigice,da sauri ta d'ago ganin Saleem ta fashe da kuka tace"Yaya Saleem mubar gurin nan wllh xai biyomu,ai da sauri ya tada motar ya fuzgeta,

Suna tashi Boss ya zo gurin,sai dube dube yake ransa a jagule amma bai gantaba,yace"wllh zaki gane ne koda na barki Khairat tunda tayi niyyar kasheki to saita kasheki wawiyar yarinya,ai bai gama rufe baki ba,wata babbar mota dake ta aikin danna masa hune don ya tsaya bisa hanya tayi ciki da motarsa domin me babban motar yakasa sarrafa burkinsa,aikuwa motar boss tayi ta wuntsilele luwa a daji zuwa cen ta kama da mota,shi kansa me babban motar da sauran mutane biyun dake ciki da k'yar aka curosu d'aya cikinsu ya rasu,boss kuwa ai tuni ya gama k'onewa haka 'yan kwana-kwana suka ciroshi da kyar aka nufi asibiti dashi da sauran biyun waccen motar,suka hau kashe wutar,

Kuka kawai Zainab keyi hakan yasa Saleem bai iya cewa komai ba har suka isa Kaduna kai tsaye gidan malam babba ya nufa da ita tunda acen sukayi sallama da Lameer,

Ai tun kafin ya gama parking,ta fita a guje tana "yayah Lameer Ummana Babbana Abbuna Ammina Kakaaaaaa!,

Da sauri dukansu suka mik'e dukansu sukayi waje da sauri ai tana ganinsu ta ruk'umk'ume Ammi tana kuka,suma duka suka saka kuka,suka ciki suna tambayarta ta kasa bada amsa sai kuka,

Shi kuwa Saleem jin ana sallahr magrib shiga yayi masallacin k'ofar gidan,bayan sun fito ne ya yaga sun fito gaba d'aya tare da su Abbu Baba da Lameer,nan ya gaishesu,suka amsa cikin fara'a,

Lameer yace"kadawo kenan,yace"aikuwa,ya d'aura da cewa mushiga kaga abinda xaka gani yau har tukwici sai ka bani,

Da sauri ya kallesa tare da murmushin yak'e yace"aini yanxu ba abinda ke burgeni idan ba Zainab zaka dawomin da itaba,yace"kaidai abokina mushiga ka gani,haka suka shiga gidan suma su Abbu suna addu'ar Allah yasa suga alkhairi......


Nace muku banjin dad'i kuyi hak'uri da wnn,wad'anda sukamin addu'a na gode sosai ana mugun tare🤝😍


Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
         
                *NI DA YAYA  LAMEER*

                              ❤❤❤❤
                               🧡🧡🧡💓
GAJERAN LABARI


Story and written

By

Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

         

________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇

 NI DA YAYA  LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "NI DA YAYA LAMEER page 21 to 30"

Post a comment