Results

NI DA YAYA LAMEER page 31 to 40 end

Diditated to ATK

Special gift to Anty Hauwa

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

_Wad'anda sukemin addu'a nagode sosai ana mugun tare Alhamdulillah naji sauki nagode da addu'o'inku gare ni ana mugun tare_

πŸ…Ώ️31↪️32

Shiga sukayi ciki haka nan Lameer yaji gabansa na fad'uwa,da sallama suka shiga farlourn Kaka,

Duk hijabaine jikinsu da alama suma basu dad'e da idar da sallah ba,

Zainab kuwa na jikin Ammi har zuwa lokacin kuka take don gani take kamar boss zai sake zuwa ya tafi da ita,

Tajin sallamarsu ta mik'e da gudu ta ruga ta k'amk'ame Lameer,ai shi suman tsaye yayi bai ta6a tunanin Zainab d'insa zai gani ba,kasa magana yayi sai rik'eta sosai da yayi ajikinsa yana sauke ajiyar zuciya,

Abbu da Baba,kuwa Alhamdulillah kawai suke maimaitawa,Abbu ya d'aga hannu yace"godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai Allah kaine abin godiya mun gode maka,gaba d'aya gurin sukayi salatin Annabi,

Bayan duk sun zauna,Saleem ya musu bayanin komai yace"bayan na dawo Jos daidai k'auyen nan Fanbeguwa anan naganta tana tsaida mota ba motar da ta tsaya har na wuce sai tabani tausayi ban d'auka Zainab bace saida tashugo,

Kallonta sukai idanuwansu cike da alamar tambaya,cikin kuka ta sanar musu duk abinda ya faru har zuwa yau da ta gudu,

Ai wani mek'ewa da Lameer yayi kowa saida ya dubesa,idanuwan nan nasa tuni suka cenza launi zuciyar 'yan maza ta tashi cikin wata irin murya me had'e da kishi yace"maxa kitashi muje ki nunamin inda mutumin nan yake wllh yau sainaga bayansa,

Saleem ne ya kamashi ganin yadda yake fuzgar hannun Zainab yana"ki tashi muje nace,yace"haba abokina wnn duk ba naka bane tunda Allah ya ku6utar da ita daga hannunsa ai sai mugodewa Allah snn Allah zai mata sakayya ita da sauran mutanan da yacuta har yakashe don hakkin rai ai babba ne,

Baba yace"wnn haka yake karka damu d'ana Allah zaiyi ikonsa akansa,da k'yar ya zauna donji yake da zaiga mutumin nan zai iya kashesa sbd 6acin rai,

Kallon Zainab yayi yace"to ke bakiji yace wani yasashi ya d'aukekiba,shuru tayi tana tunani zuwa cen tace"eh naji dai yana yawan ambaton wata wai cewa tayi akasheni,gaba d'aya suka d'au salati yace"bai fad'i sunanta ba,tace"ko Khairat yace kome?,da sauri ya mik'e yace"Khairat ko daman na dad'e ina zargin dasa hannunta a 6atanki yau zata gane kuranta,

Da sauri ya fice,suna kiransa amma ina xuciyarsa ayi zafi,

......................................................

Acen gidan Alh Kamalu kuwa,rigima ake sosai domin an amshe Senator da aka basa daman ba mutane ne suka za6esa ba murd'iya ce,to asiri ya tuno don haka gwamna me adalci ya amshe anbawa wani ruk'on k'warya kafin ayi za6e,nan fa hankalinsa yatshi inda ake ta d'auki ba d'ai d'ai domin gidan Redio yaje yana ta zagin gwamna,

A hanyarsa ta dawowa dunduzun matasa suka taresa sukai masa tsinannan duka,snn suka kona motarsa,nan suka barsa kwance rai a hannun Allah,

Da k'yar wasu masu tawakkali suka kaisa asibiti,lokacin da aka sanar da Hjy luba da Khairat tsaki sukaja,sukace babu ruwansu aisaida sukace kar yaje snn yaje dama kashesa sukayi,

Cikin dare kuwa gidansu ya kama da wuta domin d'akin da dodonsa yake ya faraci,zuwacen gidan ma ya faraci,sosai suke ihu suna neman temako,kafin 'yan kwana-kwana suzo ai tuni sun galabaita,

Mutanan unguwa aka taru domin ihun da akeji a gidan yayi yawa,wani d'aki da aka bud'e anan akaga kawunan mutane da gangar jikin mutane,nanfa aka dunga tsine masa da Allah wadai,'yan jarida tuni suka hallara da 'yan gidajen tv kai abinfa ba kyan gani,

A wnn halin Lameer yazo,ganin abinda ke faruwa yasa jikinsa sanyi da Allah wadarai da halin Alh kamalu,

Su Khairat kuwa anji jiki,Hjy luba tuni ta amsa kiran Allah,khairat kuwa duk ta k'one ta cenza kamannin babu kyawun gani,abin da abin tausayi,

Haka Lameer ya koma gida yasanar da iyayensa nan suga dunga Allah wadai da wnn abu,

Alh Kamalu kuwa ai asibiti ihu ya dungayi yana fad'ar mugayen abunda yayi harda uwarsa da k'annansa da yabawa dodonsa da duk wasu da yakama,

Zuwa wani lokaci akaga cikinsa yayi girma sosai irin naban mamakin nan,uhmm kai abin fa babu kyawun gani da haka yarasu yana ihuuu,(Ya Allah kasa muyi kyakkyawar mutuwa kagara halayenmu ka hanamu aikata alfasha,don Allah yanzun ina amfanin bad'i ba rai Allah ya kyauta),

Alh kamalu dai an tafi cikin wani mayuwacin hali,ya Allah ka shirya masu hali irin nasa amin,

*************

Zainab kuwa tun bayan abinda ya faru,duk tadawo wani irin sanyi ta natsuwa kai bazakace ita bace,sosai yanzu ta mayar da hankali akan karatunta,

Babu wasa da shirme,ga girmama malamanta,

Akwana atashi babu wuya a gurin Allah,Shekaru hud'u kenan,a yau Zainab ta kammala jarabawarta ta SSCE ta kammala secondry,shekarunta sha takwas yanxu xuwa lokacin tayi girma sosai kyawunta yafito tazama cikakkiyar budurwa mai kyau da tsari ga natsuwa da kamala,

Kyakkyawar yarinya me manyan idanuwa ga hanci bak'inta mekyau da zubin hak'oranta farare tass,gashinta kuwa bak'i wuluk ga tsawo da yawa,

Idan tayi mirmushi kumatunta biyu sai sun lotsa kai da ka ganta saita burgeka,

Yaya Lameer ma an k'ara kyau,uhmm abin sai wanda ya gani cikakken namiji kenan da ko wacce mace zatayi alfahari ya zamo miji a gareta,sunyi kama sosai da Zainab d'imsa yanasonta so na hak'ik'a,gaskiya Yaya Lameer k'arshe ne wajen kyau da tsaruwa,

Tana zaune a farlourn Ammi ya shugo sanye yake da k'ananun kaya gaskiya yayi kyau,zuba masa ido tayi tunda yashugo aranta take aiyana kyau da had'uwa na yayan nata ji take inama ace shi,mijinta ne gaskiya tana k'aunar yayan nata,

Hura mata iska yayi cike da shagwa6a ta turo baki gaba yace"wnn irin kallo karfa ki cinyeni d'anye,tace"kai yaya Lameer kullum fa naga kyau kake k'arawa wllh,

Dariya yayi me k'ayatarwa yace"duk kyauna ai ban kai sarauniyar mata ba,yanzu,ma tad'i zani ko zaki raka nine,tuni ta zaro ido sai kuma ga yawaye sun taru mata tace"tad'i,kuma yaya,sai ta fashe da  kuka tayi ciki da gudu murmushi yayi yabi bayanta da kallo aransa yace"dole in amshi matata hannun Ammi don yanzu ne lokacin da nafi buk'atarta,

Jikin Ammi ta fad'a tana kuka Ammi tace "lafiya me yafaru Ummi,cikin kuka tace"Ammi ba Yaya Lameer bane wai tad'i zashi don Allah kice kar yaje wajen wata,

Zaro ido tayi Tace"ehye,sai tasa dariya tace"ki kwantar da hankalinki Ummina kin kusan tarewa gidan,mijinki don yanzu haka shirye-shirye muke,tace"miji kuma wanne mijin?,nan Ammi tasanar mata duk abinda ya faru a baya na auransu da akayi da yayanta,

Ai tsalle ta buga ta rungume Ammi tace"kai amma naji dad'i Ammina gaskiya kun kyauta mana,da gudu ta fita cikin jin dad'in daman yaya Lameer mijinta ne lallai tafi,ko wacce mace sa'ar miji a duniya

(ni kuwa Ummu Affan nace a'a zee nimafa nafi ko wacce mace sa'ar miji😜😜)

Ammi murmushi tayi cike dajin dad'in Ummi ma tanason Lameer,Hussainarta takira tasanar mata wato Umman Zainab nan sukai ta dariya sukace yaran zamani kenan.......Mu had'e gobe don jin k'arshen labarin

Taku a kullum meson faranta muku,

Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
πŸ§‘πŸ§‘πŸ§‘πŸ’“
         
                *NI DA YAYA  LAMEER*

                              ❤❤❤❤
                               πŸ§‘πŸ§‘πŸ§‘πŸ’“
GAJERAN LABARI


Story and written

By

Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

       

________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And nowπŸ‘‡

 NI DA YAYA  LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144
Diditated to Fans

Special gift to Anty Hauwa

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ…Ώ️33↪️34


Sosai Ammi ke gyaran d'iyar tata,duk wani abu da yadace tana mata,

Tun lokacin da Zainab taji cewa yaya Lameer mijinta ne,suka dawo wasan 6uya don bata bari su had'u,wata irin kunyarsa takeji sosai,

Shi kuwa d'an anacin,kullum yana cikin gidan inda yadawo daga aiki,sai ta shige d'akin Ammi idan xai bita Ammi ta hana,tace"waiku yaran yanxu meyasa ne baku da kunya,

Sai yasosa keya kawai ya fita aransa yana cewa amma Ammi ai kinsan nayi k'ok'ari shekarun kusan bakwai ina renon matata aikuwa a jinjina mini,

Sosai aka shirya taron tarewa,inda akayi hidima sosai ta 'ya'yan gata,

Daman tuni Lameer ya gama gininsa anjerawa Zainab komai gidan ya had'u iya had'uwa ya tsaru,

Inda a ranar tarewar aka kaita d'akin mijinta kuma Yayanta _LAMEER_

Fad'ar farin cikin da Lameer yake ciki 6ata baki ne,shidai yasan yana cikin tsantsar farin ciki da annashuwa,yarasa wanne irin sone yakewa k'anwar tasa,

Sosai iyayensu suka had'asu suka masu fad'a nasu xauna lfy sudai sunsan tamkar hanta da jini suke,Zainab bataji komai ba don tasan yayanta zai rik'eta amana hakan yasa ko kukan nan da amare keyi idan za'a kaisu ita batayi ba,

Wata abokiyar wasansu tace"kai Ummi ko kuka babu,tace"to mezanwa kuka nidaza'akai gidan yayana abin sona,nasan zanyi kewar su Ammi amma nasan danace yakaini zai kaini,dariya tasaka tace"ni gaskiya banta6a ganin amarya irinkiba kona k'aryarnan bazakiyiba,murgud'a baki tayi tace"to bazan ba,

Haka aka kaita gidanta,Wajen takwas na dare kowa ya watse itama tashi tayi ta d'auro alwala taxo tayi isha'i tayi shafa'i da wuturi,tana addu'a taji motsin shugowarsa,da sallama,addu'a ta shafa tayi saurin komawa kan gado ta rufe fuska,

Shi abinma dariya yabasa yayi murmushi snn ya ajiye ledar dake hannunsa ya zauna bakin gadon yace"amarya kinsha k'amshi,sake sadda kai k'asa tayi cike da kunya,

Yace baza'a bud'emin fuskar in ganiba ko saina biya,tace"a'a,tare da d'aga mayafinta kanta na k'asa,tafin hannunsa yasa ya d'ago fuskarta yace"Zainab kalleni,d'ago kwayar idanuwanta tayi,suna had'a ido ta sake k'asa da idanuwanta sbd kwarjininsa dayacika mata ido,

Yace"ki kalleni nace,da kyar ta iya kallonsa suka xubawa juna ido,yace"me kika gani cikin idona,turo baki gaba tayi cike da shagwa6a tace"ni banga komai ba,

Jawota yayi jikinsa yana sakin ajiyar zuciya yace"bakiga tsantsar sonki da k'aunarki ba acikin idanuwana,

Tace"nima ai ina k'aunarka yayanah,ajiyar zuciya yayi yace"Zainab tun ranar da aka haifeki nake kaunarki ke bugun numfashi nace ina sonki ina kaunarki Zainab don Allah nima kisoni,

Tace"inasonka yayanah a tun lokacinda na mallaki hankalin kaina nakejinka cikin jini da tsokata,

Murmushi yayi yace"tunda naga kin idar da sallah yanxu kina da alwala kitashi muyi sallah don nuna godiyarmu ga sarki Allah da ya nuna mana wnn babbar ranar,ba musu ta tashi,shima alwala ya d'auro yazo yajasu sallah raka'a biyu,bayan sun idar ya rik'e goshinta ya dunga kwararo mata addu'o'i,daga bisani ya jawo ledar da yashugo da ita,

Fulat ya d'auko da kofina ya dawo ya zuye musu kazar snn ya yago tsoka yace"bud'e bakinki,mak'e kafad'a tayi alamar a'a,ya janyota jikinsa yace wllh kici,ko namiki d'ure,

Turo baki tayi cike da shagwa6a,da sauri kuwa ya chafke bakin yana aika mata wani hut kiss,zaro ido tayi cike da tsoro😳,

Ganin haka yasaki bakin nata,wata irin kunya taji aranta tace daman haka yaya Lameer yake,ashe a fili ta fad'a saiji tayi yace"yarinya na wuce nan,ai dama kin dad'e kinamin yanga da bakin nan naki ko?,

Da sauri ta sake k'asa  da kai tana murmushi,a hakadai sukaci naman tare dashan fresh milk snn suka shiga toilet suka wanke baki,

Tunda ga toilet ya kinkimota sai kan gadonsu,nan fa ya fara sarrafata son ransa,ganin da gaske yake sai lokacin Zainab ta fara kad'uwa,tace"don Allah yaya Lameer kayi hakuri ka barni,

Cikin wata irin murya yace"bazan iya ba Zainab shekaru nawa ina jiran wnn ranar kinsan hkr da juriyar danayi a kanki kuwa?wllh nasha bak'ar wahala donni nasan kaina daurewa kawai nayi alokacin da kuma alkhawarin danawa su Abbu amma kin wahalar dani,

Nan fa ya fara aika mata zafafan sak'onni wad'anda takasa fassara su,

Lallai yaya Lameer k'arshe ne,ta nan fannin saida ya gama jagulata da kissing d'inta ta ko ina snn ya nufi babbar harkar,

Ai tunda Zainab taji ya fara laluban k'asanta hankalinta fa yatashi nan ta fara kuka,amma ina shi hankalinsa yayi nisa bayajin zai iya saurara mata,

Gaskiya Zainab taci bak'ar wuya gurin yayan natan,tun tana cizonsa ya kushinsa har takasa,

Tun tanajin abinda ke faruwa har ta fara galabaita kai daga k'arshema sumewa tayi sbd azaba,

Shi kuwa ina yasani,hankalinsa yayi nisa baima san ta sumenba,

Saida hankalinsa yadawo jikinsa,ganin halin da take da sauri yashiga bathroom,ya had'a mata ruwa mai zafi snn yazo ya d'auko ruwa mesanyi yana shafa mata a fuska,wata irin ajiyar zcy taja,

A hankali ta bid'e ido,jin irin zafin da k'asanta ke mata yasa ta saki kuka,sorry kawai yake cemata d'aukarta yayi sai ckn bath,k'ara ta saki jin zafin ruwan ta k'amk'ameshi shidai hkr yake bata,har tayi shuru ruwan nashiga jikinta,

Bayan ya zubbada yasake tara wani yamata wanka,tare dana tsarki,d'aukota yai saikan sallaya don sallah ake ta kira,ya dauko kaya yasake mata,sannan ya yaye xanin gadon ya wanke shima yayo wankan snn yadawo yajasu sallah don baison fita yabarta,

Suna idarwa barci ya kwasheta anan,k'urawa fuskarta ido yayi yanajin wani maganad'isun k'aunarta na fuzgarsa,addu'a ya tufa mata,najin dad'in kawo masa mutuncinta da yayi,

Yakinkimeta ya mayar da ita gado shima ya kwanta tare da jawota jikinsa ya k'amk'ame yaja musu bargo nan take kuwa barci ya kwashe su,


A wnn page d'in nace muku zan dakata amma hakan bai samu ba,insha Allahu ku tsumayeni da yamma donjin k'arshen labarin idan hakan bata samuba kumin uzuri zuwa gobe,


Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
πŸ§‘πŸ§‘πŸ§‘πŸ’“
         
                *NI DA YAYA  LAMEER*

                              ❤❤❤❤
                               πŸ§‘πŸ§‘πŸ§‘πŸ’“
GAJERAN LABARI


Story and written

By

Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

       

________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And nowπŸ‘‡

 NI DA YAYA  LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144

πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š


Diditated to ATK

Special gift to Anty Hauwa

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ…Ώ️35↪️36


Basu suka farka ba sai wajen tara na safe,ita ta fara bud'e idanuwanta aiko suka sauka akan fuskarsa,gabanta ne ya fad'i da ta tano abinda ya faru,sai kuma tasaki murmushi ta fara shafa sajen fuskarsa,

Bud'e ido taga yayi,da sauri ta janye hannunta tare da k'amk'ame idanuwanta,

Dariya yayi,yace"to meye hakan keda fuskar mijinki,da sauri ta tashi cike da kunya zata ruga,amma ina sai taji ta kasa tafi ga jikinta da ya hau rawa,

Da sauri ta zauna,mik'ewa yai yace"sorry dear na mance ban baki mgn ba,zuwa yayi kitchin ya had'o mata tea me kauri yazo yace tasha,girgixa kai tayi"banyi fa brush ba,ajewa yayi yad'auko brush ya matsa makilin yad'auko wata roba da ruwa yace tayi,

A haka tayi snn yaje ya zubda,da kansa ya bata tea tasha kamar rabi snn ya bata maganin,k'ara kwanciya tayi yaja mata bargo,shi kuma bedroom d'insa ya wuce,ya yi wanka jinsa yake yazama wani sabo,jin ana buga k'ofa yaje bayan yagama shiryawa direban Ammi ne ya kawo musu abinci,amsa yayi yamasa godiya snn yajera kan dinning table,

Wajen sha d'aya na safe ta farka sai taji duk zazza6in jikin nata ya sauka,toilet ta fad'a tayi wanka,tazo ta shirya cikin wata doguwar riga sosai tayi kyau tafito amaryarta sakk,

A hankali ta tako zuwa farlour yana ganinta yasaki murmushi tare da bud'e hannayensa ta fad'a jikinsa,

To haka rayuwar wad'an nan masoya taji gaba da wakana cikin so da k'aunar juna,Lameer na k'aunar Zainab itama tana k'aunar mijin nata yayanta,

Watansu biyu da aure taci gaba da karatunta a Kaduna university sosai ta mayar da hankalinta 6angaran da yayan nata ya za6ar mata,

Uhmm rayuwa kenan haka taci gaba da wakana,inda yanzu shekararsu biyu da aure alokacinne kuma Zainab ta haifi kyawawan yaranta 'yan biyu duk maza,Ibarahim da Ahmad sunan Abbu da Baba sai ake kiransu Aayan da Aryan,yara kenan 'yan gata,bayan haihuwarsu da shekaru uku ta haifi d'iyarta mace,Aka mayar mata da Zainab sunanta sai suke kiranta Heebba,

Soyayya mai tsabta suke gabatarwa Lameer na k'aunar familynsa,

Boss kuwa tuni aka mutu a wulak'ance,Khairat kuwa bata mutuba da kyar dangin uban suka amsheta saidai gatanan dai a wulak'ance taza ma wani iri,

Zainab ta kammala karatunta cike da nasara,inda tazama cikakkiyar doctor kamar yadda Lameer yake mafarki abaya,anan asibitinsa duka suke aikinsu cike da nasarar rayuwa,

Yau gidan Kaka sukakai jiyara abin kamar had'in baki suma su Ammi duk suna cen,yaran suka ruga jikin kakanninsu,suka rik'esu cike daso da k'auna,

Lameer yace"Kaka jifa mukayi ance kin cika shine mukazo amsar gaisuwa,Zainab tace"ai kuwa amma ya mukaganniki,

Abbu yace"kunci k'aniyarku uwar tamu kukeso ta mutu,cikin muryar tsufa kaka tace"Rabu da ja'irai ai ko yanzu na mutu alhamdulillah tunda naga jikokin Lameeru da Abulle,

Harara zainab ta banka mata tace"ki dena cewa mijina Lameeru sunansa yaya Lameer ni kuma Zainab,inda so samune kicemin NIDA YAYA LAMEER,

Gaba daya gurin akasa dariya,Lameer yace"Kai amma Alhamdulillah,

Nima anan gurin nikecewa ALHAMDULILLAH,

Allah na gode maka dakasani kammala littafin nan lafiya Allah kamani ikon fara wani lafiya kuma na ida lafiya,

_ABIN LURA_

A duniyar nan karkace komai kakeso sai kasamesa,duba da irin tarbiyyar da iyayen Khairat suka d'aurata akan duk abinda takeso sai sun mata,iyaye yana da kyau mu d'aura yaranmu akan tarbiyyar akwai samu da rashi ba lallai bane komai kakeso kasamesa,

A gaskiya soyayyar wasu iyayen da suke nunawa yaransu tayi yawa,bance karkaso d'anka ba a'a kasoshi daidai gwargwado ba soyayyar da zai kangare har ka kasa d'aurasa bisa tarbiyya ba,don ance kaso naka duniya ta k'isa,

Sannan inaso ku fahimci wani abu cikin labarin nan,kuda fa LAMEER cikakken namiji d'an gata me kyau hnkl kwarjini ga kud'i uwa uba ilmi,amma sai Allah ya jarabcesa da soyayyar wawiyar mace mara ilmi ga sakarci,ABIN LURA A NAN,

Shi so ba ruwansa da kyau ilmi ko duk wani kyalekyalen duniya,Allah na d'aurawa mutum k'aunar mutum batare da dubi izuwa yadda d'ayan ya kasance ba,

Ina addu'a Allah ya shirya masu hali irin na Alh Kamalu da matarsa da kuma khairat da masu hali irin na boss wad'anda suka maida rayukan mutane ba abakin komai ba karfa kuce hakan bai faruwa wllh yana faruwa sosai,

Da fatan zamu amfana da abubuwa na gari muyarda marasu kyau,


Jinjina ga duk wani wanda ya tayani yad'a wannan littafin nagode sosai,


Wayyo dad'i masoyana a duk inda kuke wllh ina k'aunarku fiye da tunaninku burina akullum naci gaba da nishadantar daku da fad'akar daku harda ilmantarwa,nagode sosai da gwoyan bayan dakuke bani,da fatan zaku amshi sabon novel d'ina fiye da yadda kuka kar6i wnn,

Gaisuwa ga 'yan kungiyata ta Arewa writer's association,ina jinjina muku Allah ya k'ara had'a kammu,

Gaisuwar ban girma ga shugabar kungiyarmu Anty Hauwa Mmn Uswan,Allah ya k'ara girma da d'aukaka,

Domin gyara k'orafi yabo ko shawara saiki sameni a numberta ta WhatsApp 08104335144


Karku manta takunce
Fateemah Sunusi Rabee'u
UMMU AFFAN

Nagode nayi nanπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸƒ‍♀️πŸƒ‍♀️πŸƒ‍♀️πŸƒ‍♀️πŸƒ‍♀️πŸƒ‍♀️πŸƒ‍♀️πŸƒ‍♀️πŸƒ‍♀️πŸƒ‍♀️πŸƒ‍♀️Sai mun had'e a samun Novels d'ina😁😁😁

Ummu Affan✍️✍️✍️

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including  your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "NI DA YAYA LAMEER page 31 to 40 end"

Post a comment