Results

SARKIN SADAUKAI 1


SARKIN SADAUKAI
Lokacin da wannan badakare ya dora KAIFIN TAKOBIn sa akan wuyan yaron da nufin yayi masa yankan rago kwatsam! bazato babu tsammani sai wani mahayi yayo fitar burgu daga cikin duhuwar bishiyoyin daji kafin badakaren yayi wani yunkuri mahayin ya zare wata sharbebiyar takobi agadon bayansa ya sare wuyan badakaren kansa yayi futar burgu gangar jikin ta fadi kasa rikica sa.adda sarkin yaki lahmar yayi arba da gawar badakaren sai ya dakawa sauran dakarun tsawa yana mai yi musu nuni dasu afkawa mahayin alokaci guda dakarun sukayi dauki kan mahayin ana haduwa da juna aka kacame da azababban yaki mai matukar muni ban tsoro daban al,ajabi nan take karar karafniyar karafa ta cika dodan kunne ihu da kururuwar mazaje ta cika dajin gaba daya

duk inda badakaren yasanya agaba sai dai kaga mazaje na zubewa kasa matattu tamkar ana sassabe agonar auduga dakarun suna kaina mahayi miyagun hare hare cikin matukar zafin nama, sa,adda wannan yaro makaho yaji wajen ya kacame da artabu sai kawai ya durkusa kasa ya kama rarrafe ya boye abayan wani dutse, kafin shudewar dakika saba,in mahayin ya kashe fiye da kaso shida bisa goma na dakarun, al,amarin da yayi matukar firgita sauran dakarun kenan suka fara kokarin cika wandonsu da iska shi kuwa sarkin yaki lahmar

koda yaga irin muguwar barnar da mahayin yayi masa sai ya fusata ainun duk wannan fafatawa da akeyi saurayin dake kokarin ceto rayuwar yaron yana kwance magashiyan yana kallon abinda ke wakana tsakanin mahayin dasu sarkin yaki zuciyarsa cike da matukar mamaki yana mai cewa acikin ransa ya.akayi wannan mahayi yasan cewa ina cikin bukatar taimako? amsar tambayar daya kasa bawa kamsa kenan lokacin da sarkin yaki yaga cewa mahayin ya kusa karar da dakarunsa sai kawai ya sai kawai ya dako wawan tsalle daga inda yake tsaye

tamkar an harboshi daga cikin baka yana saman ya zare wadansu zaratan takubba agadon bayansa ya dira adaf da inda mahayin yake alokacin da sauran dakarun sukaja da baya aka fara kallon-kallo tsakanin sarkin yaki da mahayin koda sarkin yaki yayi arba da idanun mahayin sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi abinda ya fado masa azuciya shine duk da cewar bai ga fuskar mahayin ba amma yaji ajikinsa cewa tabbas ya taba ganin fuskar mahayin sai dai abin tambaya anan shine a,ina yataba ganin mahahin kuma mace ce.ko namiji

amsar tambayoyin da sarkin yaki ya kasa bawa kansa kenan kawai sai ya daga takubbansa sama ya falfala da azababban gudu izuwa kan mahayin yana kwarara ihu koda ganin hakan sai mahayin ya dako wawan tsalle daga inda yake ya kaiwa sarkin yaki lahmar wawan sara da takobinsa da nufin tsinke masa wuya cikin zafin nama sarkin yaki yasanya takobinsa ya kare saran sannan suka rugunntsume da masifaffan yaki suka wanzu suna kaiwa kaiwa juna sara da suka cikin matukar zafin nama juriya da bajinta ta gaban kwatance


wohoho! tabbas jarumtaka da sadaukantaka baiwa ce daga Allah komai hassadar mutum idan yaga yadda gwanayen biyu ke tsallakewa.miyagun hare-haren juna dolane ya jinjina musu ya tabbatar da cewa sun cika GWARAZAN JIYA azahiri ga wanda yake kallon yadda artabun yake wakana zai fahimci cewa sarkin yaki yafi mahayin karfin damtse sai dai mahayin ya fishi tsagwaron sanin salon yaki nanfa yazamana cewa jaruman biyu har daka tsalle sama su keyi suna kaiwa jhna hari wohoho! tashin hankali ba.a samaka rana GOBARAR ANNOBA kuwa idan ta taso babu mai dauke ta face Allah,

Nanfa yazamana cewa bama bishiyoyi da duwatsun dake dajin ba hatta sauran dakarun suna cikin matukar tashin hankali domin bishiyoyi dake karairayewa sakamakon artabun jarman biyu suna yunkurin murkushesu bashiri suka kama guje-guje gami da ifice-ifice ana cikin wannan artabu ne mahayin yayi tunani tunanin kuwa shine matukar aka cigaba da wannan artabu wannan jarumi dake kwance magashiyan zai iya rasa rayuwarsa koda gama tunanin hakan sai kawai ta shammaci sarkin yaki ya gabzamasa wawan naushi a kirji saboda karfin naushin

sai da yayi katantanwa asama sau hudu sannan ya kife akasa
Kafin yayi yunkurin mikewa mahayin ya karanto wadansu dalasiman tsafi ya rikida izuwa wata bakar guguwa ya tashi izuwa sama ya keta gajimare ya bace bat! sarkin yaki ya mike tsaye zumbur kawai sai yaga wajen wayam babu mahayin da saurayin da wannan karamin yaro cikin matukar takaici gami matsanancin fushi ya takarkare ya kwarara wawan ihu acikin wannan hali ne kwatsam! sai sarki

shazwan,sarkin bokaye Dargaz,waziri Rufyanda wadansu zaratan dakaru suka rugo izuwa wajen abisa dawakai sukayi tirjiya
Daga mai debe muku kewa ako yaushe
MANSUR USMAN SUFI
08137237071

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "SARKIN SADAUKAI 1"

Post a comment