Results

SARKIN SADAUKAI 2


SARKIN SADAUKAI 2
Lokacin da su saurayi Hizmal su ka shigo cikin wannan kofa sai su ka tsinci kansu a cikin wani daki kofar dake takasance makekiya mai tsawo da fadi kuma anyi tane da zallar mulmulallan bakin karfe inda za,a sanya karti majiya karfi mutum hamsin bazadu iya tureta ba daf da bakin kofar an ajiye wani teburi na azurfa mai tsawon kamu hudu teburin yana dauke da wadansu manyan kubobi guda biyar da akayisu da karfen yakuti da walwali da sheki komai kallon kurillar mutum bazai iya tantance kubobin ba saboda kamannin su daya yayin da su kayi arba da kubobin sai mahayin ya daga kansa ya kalli saman kofar nan take yaga anyi wani rubutu da tawadar za,afaran ajikin wani allon karfe kamar haka.

yakai ma'abocin wannan gida kayi sani cewa wadannan kubobi guda biyar dake ajiye abisa wannan teburi dake kasa acikin sune zaka samu.mabudin wannan kofa ta biyu sai dai fa kayi sani cemwa matsawar ka.dauki kubar da ba itce mabudin kofar zaka fada cikin mummunar musiba mai makon shiga izuwa gidan tsira
Sa'adda mahayin yazo dai-dai nan a karatunsa sai hankalin sa ya dugunzuma ainun,Abinda ya dugunzuma hankalin nasa shine shin taya ya zai iya gane mabudin kofar cikin gaggawa kafin su sarki shazwan su cimmiusu wannan kuma tabbas tsafi bazai taba yin tasiri awannan waje ba,

Koda mahayin yazo dai-dai nan atunaninsa sai hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye dako yaushe ya kura kubobin dake kan teburin idanu yana nazarin su na tsawon wani lokaci ,
Ana cikin wannan hali ne sai sukaji wani irin kara ya cika gaba daya dakin bashiri suka waiga bayansu domin suga ko menene ,Aikuwa koda waigawarsu sai sukaga ashe kofar farko da suka baro abayace take kokari budewa

Daganin hakan sai mahayin ya dimauce bai san sa'adda ya dauki daya daga cikin kubobin ba ya zira a cikin wani dan kwaroron rami dake tsakiyar kofar ya shiga murdawa da dukkan karfinsa domin ya bude kofar amma shiru kakeji babu labari har tsawon dakika hamsin kwatsam sai akaji karar budewar

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "SARKIN SADAUKAI 2"

Post a comment