+2348140419490

Keffi Nasarawa State, Nigeria

Download and read free hausa novels

SARA DA SASSAKA complete hausa novel document


 

SARA DA SASSAKA Complete
Name SARA DA SASSAKA
Size 436kb
Author rashidat usman
File Type TXT
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 27 September, 2020
descriptionLITTAFIN SOYAYYADOWNLOAD DOCUMENT


MIJIN YARINYA complete hausa novel document


 

MIJIN YARINYA Complete
Name MIJIN YARINYA
Size 193kb
Author Faty Afreen
File Type TXT
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 27 September, 2020
descriptionLITTAFIN SOYAYYADOWNLOAD DOCUMENT


MARYAMA SARAUNIYA complete hausa novel document


 

MARYAMA SARAUNIYA Complete
Name MARYAMA SARAUNIYA
Size 361kb
Author Ummi Aisha
File Type TXT
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 27 September, 2020
descriptionLITTAFIN SOYAYYADOWNLOAD DOCUMENT


KAWAR 'YATA CE complete hausa novel document


 

KAWAR YATA CE Complete
Name K'AWAR 'YATA CE
Size 596kb
Author Sumayya A Shehu
File Type TXT
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 27 September, 2020
descriptionLITTAFIN SOYAYYADOWNLOAD DOCUMENT


JENNIFER complete hausa novel document


 

JENNIFER Complete
Name JENNIFER
Size 596kb
Author Umme Garkuwa
File Type TXT
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 27 September, 2020
descriptionLITTAFIN SOYAYYADOWNLOAD DOCUMENT

DOWNLOAD NOW

MI WASMITI Nayi nadama complete hausa novel document


 

MI WASMITI Nayi Nadama Complete
Name MI WA MISWATI Nayi nadama
Size 596kb
Author Aisha Ali Garkuwa
File Type TXT
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 27 September, 2020
descriptionLITTAFIN SOYAYYADOWNLOAD DOCUMENT


FATU A BIRNI complete hausa novel document

FATU A BIRNI complete
Name FATU A BIRNI
Size 661kb
Author Mrs Aslam Haidar
File Type doc
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 25 September, 2020
descriptionhausa FICTIONDOWNLOAD DOCUMENT


FYADE complete hausa novel document

FYADE complete
Name FYADE
Size 310kb
Author Mamanm Nurool; Hudah
File Type doc
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 25 September, 2020
descriptionhausa FICTIONDOWNLOAD DOCUMENT


RUDIN SHAIDAN complete hausa novel document

RUDIN SHAIDAN complete
Name RUDIN SHAIDAN
Size 200kb
Author Shuraih Usman
File Type doc
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 25 September, 2020
descriptionhausa FICTIONDOWNLOAD DOCUMENT


SOORAJ complete hausa novel document


 

SOORAJ Complete
Name SOORAJ
Size 2MB
Author Fatima Sardauna
File Type DOC
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 25 September, 2020
descriptionLITTAFIN SOYAYYADOWNLOAD DOCUMENT


AUREN BAZATA complete hausa novel document 

AUREN BAZATA Complete
Name AUREN BAZATA
Size 859kb
Author Zainab Yakasai
File Type DOC
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 24 September, 2020
descriptionLITTAFIN SOYAYYADOWNLOAD DOCUMENT


YAR BARIKI book 1 & 2 complet android apk novel


 

YAR BARIKI Book 1 & 2
Name YAR BARIKI
Size 9MB
Author Rufaida Omar
File Type Apk
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 24 September, 2020
descriptionLITTAFIN SOYAYYADOWNLOAD ANDROID APP


MAKAUNIYAR SOYAYYA complete hausa novel document


 

MAKAUNIYAR SOYAYYA Complete
Name MAKAUNIYAR SOYAYYA
Size 1MB
Author Princess Maryam Ahmad Paki
File Type DOC
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 20 September, 2020
descriptionLITTAFIN SOYAYYADOWNLOAD DOCUMENT


A YINI DAYA complet Hausa novel document


 

AYINI DAYA Complete
Name AYINI DAYA
Size 283KB
Author Princess Amrah & Rabi'atu Sk Mashi
File Type DOC
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 20 September, 2020
descriptionLITTAFIN SOYAYYADOWNLOAD DOCUMENT


WAYE SHI complet hausa novel document


 

WAYE SHI Complete
Name WAYE SHI
Size 2MB
Author Aisha Shafee'i
File Type DOC
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 20 September, 2020
descriptionLITTAFIN SOYAYYADOWNLOAD DOCUMENT


AJALI na Shafi'u Dauda Giwa complet Hausa Novel document


 

AJALI Complete
Name AJALI
Size 527 KB
Author Shafi'u Dauda Giwa
File Type DOC
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 20 September, 2020
descriptionLITTAFIN SOYAYYA DA ARTABUDOWNLOAD DOCUMENT


ABDULMAJEED complete hausa novel document


 

ABDULMAJEED Complete
Name ABDULMAJEED
Size 1.2MB
Author Meryam Abdool
File Type DOC
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 20 September, 2020
descriptionLITTAFIN SOYAYYADOWNLOAD DOCUMENT


ABBAKAR complete Hausa Novel documen


 

ABBAKAR Complete
Name ABBAKAR
Size 859kb
Author Fatima Aminu Ya'u
File Type DOC
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 20 September, 2020
descriptionLITTAFIN SOYAYYADOWNLOAD DOCUMENT


KWANA SITTIN littafi na biyu 2 complet hausa novel document


TSOKACI


“May be Safeenah ta taba ganinka a fili ko a hoto, ka kawatu a ranta. May be kuma surarka ta zo mata ne cikin ‘delusion’ dinta bayan ta ji ka a kafafen yada labarai wani abu naka ya zauna a ranta ya haifar mata da imaginarysoyayyarka cikin ‘delusion’. ‘Delusion’ kamar ido biyu yake, wata rayuwa ce dan Adam din da kwakwalwarsa ta motsu yake yi a cikin kwakwalwarsa da wasu mutane daban-daban wadanda shi yana ganinsu yana jin muryoyinsu, amma mu masu lafiya ba ma ganinsu, ba ma jinsu. ‘delusion’ shi ne ‘illusion’, ‘deception’. Oxford dictionary ya fassara shi a turance da; ‘a senseous perception of an external object involving a false belief’. 


 

Karanta a kan ₦ 300.00

KWANA SITTIN littafi na daya 1 complet hausa novel document


TSOKACI

Babban farin cikinsa da Allah ya yo shi musulmi, cikakken Hausa-Fulani. Ya yi masa baiwa da wata irin UWA mai yawan jin qai da kyautatawa, tausasawa,karfafawa da tausayawa a gare shi. Mai yi masa addu’a a kan dukkan al’amuransa, Ya yi masa baiwa da rayuwa da masoyiyar da yake da yaqinin har abada ba zai samu makwafinta ba. Masoyiya ta haqiqa, wato marigayiya SUHAILA. Wadda har abada ta ke koriya sharrr cikin tsokar zuciyarsa, sannan abar tunawa da kewa mai yawa. Ta yadda ya alqawarta wa zuciyarsa ya gama aure a duniya, a dalilin ya rasa suhaila. 

MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN book 1 to 6 complet Audio hausa novel


littafin MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN tun daga na daya 1 zuwa na shida 6 a karkashe,
littafin daya samu karatu daga shaharrarren makarancin nan Muhammad Umar Kaigama
ga littafin nan a kasa sai ku downloading


kashi na daya 1
kashi na biyu 2
kashi na uku 3
kashi na hudu 4
kashi na biyar 5
kashi na shida 6
kashi na bakwai 7
kashi na takwas 8
kashi na tara 9
kashi na goma 10
kashi na sha daya 11
kashi na sha biyu 12
kashi na sha uku 13
kashi na sha hudu 14
kashi na sha biyar 15
kashi na sha shida 16
kashi na sha bakwai 17
kashi na sha takwas 18
kashi na sha tara 19
kashi na ashirin 20
kashi na ashirin da daya 21
kashi na ashirin da biyu 22
kashi na ashirin da uku 23
kashi na ashirin da hudu 24
kashi na ashirin da biyar 25
kashi na ashirin da shida 26
kashi na ashirin da bakwai 27
kashi na ashirin da takwas 28
kashi na ashirin da tara 29
kashi na talatin 30
kashi na talatin da daya 31
kashi na talatin da biyu 32
kashi na talatin da uku 33
kashi na talatin da hudu 34

duka duka gabadayan Audio din malikussaifi dan ziyazzanun kenan za mu kawo maku cigaban littafin mai taken SAISABANA wanda shima Muhammad Umar Kaigama ne ya karanta 

ku kasance da wannan shafin na WWW.DLHAUSANOVELS.COM.NG do min samun zafafan littatafai


TAKOBIN IZZA littafi na takwas 8 complete hausa novel document

TAKOBIN IZZA littafi na takwas 8
Name TAKOBIN IZZA
Size 25kb
Author Ismail Abdullahi
File Type TXT
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 19 September, 2020
descriptionLITTAFIN YAKIDOWNLOAD DOCUMENT


TAKOBIN IZZA littafi na bakwai 7 ccomplete hausa novel document

TAKOBIN IZZA littafi na bakwai 7
Name TAKOBIN IZZA
Size 23kb
Author Ismail Abdullahi
File Type DOC
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 19 September, 2020
descriptionLITTAFIN YAKIDOWNLOAD DOCUMENT


TAKOBIN IZZA littafi na shida 6 complete hausa novel document

TAKOBIN IZZA littafi na shida 6
Name TAKOBIN IZZA
Size 23kb
Author Ismail Abdullahi
File Type TXT
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 19 September, 2020
descriptionLITTAFIN YAKIDOWNLOAD DOCUMENT


TAKOBIN IZZA littafi na biyar 5 complet hausa novel document

TAKOBIN IZZA littafi na biyar 5
Name TAKOBIN IZZA
Size 24kb
Author Ismail Abdullahi
File Type TXT
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 19 September, 2020
descriptionLITTAFIN YAKIDOWNLOAD DOCUMENT


TAKOBIN IZZA littafi na hudu 4 complet hausa novel document

TAKOBIN IZZA littafi na hudu 4
Name TAKOBIN IZZA
Size 35kb
Author Ismail Abdullahi
File Type TXT
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 19 September, 2020
descriptionLITTAFIN YAKIDOWNLOAD DOCUMENT


TAKOBIN IZZA littafi na uku 3 complet hausa novel document

TAKOBIN IZZA littafi na uku 3
Name TAKOBIN IZZA
Size 19kb
Author Ismail Abdullahi
File Type TXT
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 19 September, 2020
descriptionLITTAFIN YAKIDOWNLOAD DOCUMENT


TAKOBIN IZZA littafi na biyu 2 complet hausa novel

TAKOBIN IZZA littafi na biyu 2
Name TAKOBIN IZZA
Size 35kb
Author Ismail Abdullahi
File Type TXT
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 19 September, 2020
descriptionLITTAFIN YAKIDOWNLOAD DOCUMENT


download NI DA PRINCE complete hausa novel document


 SHIMFIDA

Mikewa tai azabure tare da kallan agoggon bango na dakin dasauri tamike ganin takusa makara, mamaki take yanda bacci yadauketa akan sallayar datai sallar asuba,kaya ta cire tai saurin fitowa tsakargida taja ruwa a rijiya tafada toilet, wankan minti 5 tai tafito tafada daki tazura doguwar riga baka tasa hijab fari tare da daukar nikaf dinta da jakar makarantarta, dama ita sam kwalliya bata dameta ba.


Dakin ummanta tashiga azaune taganta tana ninke kaya tashiga da sallama tare da gaidata ta amsa cikin daure fuska Salmah kam tasaba da wannan hali na ummanta dan yanzu abin baya damunta, mikewa tai tare da cewa umma banga Abba ba koya fita ne? Kara hade rai umma tai tace ki wuce kigaida Goggo dan shikam ya fita tadan tabe karamin bakinta tare da karasawa dakin goggon ranta duk ba dadi, sam batasan matar.


Sallama tai Goggo dake kwance ta amsa mata cikin gadara salmah tashiga tare da gaida ta goggo ta amsa tare da cewa yawan banzan za'a tafi? Salma tadaure tace goggo nidai makaranta zani😞.. Goggo tai tsaki tace oho dai tunda ke da kamal kunfi karfin iyayenku ai sai kuyi tayi tace goggo yaza'aikifadi haka? cikin zafin rai goggo ta mike zaune tace karya aka muku?


Wayasani ma ko kamal din yamanta dake yayi auransa acan kasar dayake ke ya barki nan kina yawon nuna jiki😏? Idanun salma? Idanun salma suka ciciko da kwalla tadaure ta mike tace natafi makaranta goggo tace ke kika sani munafuka mudai kika kuskura kika dauko mana abun kunya sai kinsha mamaki, Salmah tai saurin yin waje tana share kwalla umma tagani a tsakar gida alamar duk zancen dasukai taji dasauri ta wuce dan tasan umma baxata taba sa baki a wannan maganar ba, nikaf ta daura takarasa waje.Titi ta fita tasamu bus din dazatai Buk tahau, acikin mota kanta kawai ta jingina a kujera tana tunanin wannan al'amari wai ace tsakanin ta da mahaifiyarta bawata shakuwa? Wai 'yar fari😟? Ita atunaninta tin? Ita atunaninta tin yaushe aka dena wannan abun? Intayi magana sai Abba yace mata uwarta ai bafullatanace tai wata ajiyar zuciya tare da dauko hoton kamal cikin jakarta takuramai ido aranta tace yaya yaushe zaka dawo? I really miss you, lissafin kwanan wata tashigayi yaci ace yaya kamal yadawo dan ayanda yafada mata randa sukai waya saura 3wks su taho to yanzu gashi taga harda durin kwana 5 😞. lalai yaya kamar bai matsu yaganta ba? Rabonsu da juna tun shekara 3 dasuka wuce, maida hoton tai ganin sun iso tafito daga motar ta shiga makaranta.
Lalai yau tayi late cikin hanzari tafara tafiya

sam bataji motsin mota a bayanta ba sai da

motar tazo daf da ita dasauri ta juyo cikin

razana tare dayin gefe amma ina motar

gudu takeyi gashi kamar dan koyo ne ke

tuka motar sam ba'a seti take tafiya ba

motar sai data gogi jikinta hakan yasa tafadi

kasa tim🙆🏻Tabi motar dakallo idanta taf da kwalla dan

mutane sun taru suna kallanta abin haushi

bawanda yataimaka mata, ahankali motar

tafara yowa baya sai alokacin takalli

number motar Prince 1 ne rubuce a jiki.

Sai da motar tazo daf da ita dan harta

runtse ido tadauka murkusheta za'ayi jin

shiru yasa ta bude idanta ahankali kafar

mutane uku tagani ahankali tafara dago

idanta har ta dure su akan nagaban wanda

tasani shine Prince Salman dan tanaganin

rashin mutincin dayake yi a school din wani

wahalalen yawo ta hadiya.Salman yakashe mata ido sannan yace

limamiya bakya gani ne? Aranta tace

limamiya? Yacigaba kosai muntaimaka miki

da glass ne? Salmah tamakamai harara

sannan tadaure tace ku bugeni maimakon

kubani hakuri sai kuce me? Amir dake baya

yai wata dariya yace hakuri? Oh prince

kagane metake nufi ai😆? Salman yace ohh ai? Salman yace ohh ai

kaji halin talakawa sannan yaciro bandir din

dari biyar yacilla mata yace sune matsalarki

I know😏? Idanun salma

Najib dayai shiru abaya dan shi yake koyon

tukin motar azahiri shikam baijin dadin

abinda ke faruwa amma yazaiyi?

Salma tai wani murmushi tare da daukan

kudin sannan takaraso kusa da Salman ta

mikamai ganin yaki amsa ta daura akan

motar sannan ta matso kusa da salman tace

maza irinku masu daukan mutane banza

sannan suke tunanin kudi na maganin

komai suna matukar bani tausayi😏? Idanun salma tana

gama fad'ar haka ta juya tafara tafiya,

mutanen dake gun suka shiga gulma, ran

salman yagama baci yamaimaita afili

Tausayi? Sannan yakalli kayan jikinta yaga

gaba daya kayan datasa basu wuce kayan

2000 ba amma takalleshi tace yanabata

tausayi?

 


Dasauri yakara kusa da ita ta baya ya fizgo

hijab dinta, jikintane yafara rawa ganin bata

taba shigowa makarantar ba nikaf bama

bare hijab ahankali hawaye yafara gudu a

idanta salma yadawo ta gabanta dasauri ta

tsugunna tare da kankame jikinta, ya firgita

ganin yanda Allah yamata kyau amma

rashin mutuncin dake idananunsa sun

rinjayeshi yatsugunno kusa da ita sannan

yace tausayi? Nidake yanzu waye mai kalar

tausayi? Hawaye kawai takeyi yai wata

dariyar mugunta sannan yace banza 'yar

tallakawa ya mike yafara tafiya tace kai da

kake d'an masu kud'i fin wasu kai? Tsayawa

yai chak sannan ya juyo yace ke kinsan niko

waye ma? Tace why should I know? Yace be

careful dan zan iya ruguza miki rayuwarki

mark my word ya juya ya tafi.Amir yashiga tafamai yace woo Man kana

burgeni, salman yai tsaki yafada mota yace

najib zokaja cikin sanyin jiki najib ya shiga.

Salma kam suna tafiya tadau hijab dinta

tasa da nikaf dinta tamike tare da kallan

agogon hannunta shikenan tayi missing

lectures dan kusan 40mins kenan dashiga

class ahanakali take tafiya tana jin wata

muguwar tsanar salman jitake daza'a bata

wuka ace anmata uzuri takashe mutun daya

data tsana a duniyarnan to lalai ba shakka

salman zata lumawa wannan wukar😡..Salma kam yaci alwashin sai ya nunamata

shi basa'an yinta bane dan tunda aka

haifeshi bawanda yataba fadamai maganar

banza irin wannan banzar yariyar dabai

masan ta ba, Amir yakalla yace adubomin

ko ita wacece, Amir yace wannan yarinyar?

Salman yace yes I can't live her like this.

Amir yace angama prince....

DOCUMENT INFONI DA PRINCE complete
Name NI DA PRINCE
Size 211 KB
Author Ayusher Muhammad
File Type doc
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 17 September, 2020
descriptionhausa FICTIONDOWNLOAD DOCUMENT


download A'INDO TANTAGARARRIYAR YAR AIKI complet Hausa novel document


 SHIMFIDA


Tinkim  wani  kauye ne dake wajen jihar Zinder ,a kasar Niger ,kauye ne wanda kusan zan iya cewa tsaka tsakiya yake tsakanin Nijeria da Niger. 
  Kauyen yanada kyau da dadin zama,mutanen garin akoy karamci da son bako,gidan Ado Mai saida kifi kowa yasan sa a kauyen,tunda ya taso yake sana'a saida kifi,har ya zama samari ,ya hadu da kuluwa mai bakin masifa,kowa yasan kuluwa da masifar ta,hakan yasa duk wanda yake son ta da aure yanzu ne zakaji an zuge shi.ace Masa ai batada da'a bata san darajan yan Adam ba,masifafa ce,sai kaji an fasa auren. kauyen auren wuri ake ma yarinya daga kin kai shekaru sha uku sha hudu yanzu za'a aurar dake,yayyin da kuluwa saida takai shekaru goma sha takwas kafin  Ado mai  saida kifi ya gani yace yana so kuma yana iyawa Saida akasha duru kafin  a bari ya aureta.


   Bayan anyi Aure kuluwa tana masa ladabi da biyaya da duk wani abinda ya danganci sauke hakki ne na mijin ta ,saide fa ko kadan batada hakuri ,idan ya mata abinda bashi ba,yanzu ne zata juye masa buhun bala'i.....


   A haka suke zaune,yau dadi gobe ba dadi,Ado yanada daidai abin rufin asirin  sa,domin dai abinci bai gagaresa ba,sanan sutura batafi k'arfin su ba,da sauran abinda ba'a rasa ba,saida sukayi shekara daya kafin Allah ya Albarkace su da samun yan tagwaye duka mata,masu matukar kama da juna,kyawawa dasu bazaka taba gane su ba,ranar suna za'a sa musu sunan su na hassana da husseina  anma Kuluwa ta zuba masifa dole fa sai ansa ma daya sunan mahaifiyar ta da ta rasu,Allah ya jikan Mahaifiyar ta itama masifafa ce ta bugawa a jarida,dan kuluwa dai gado tayi......


   ba yanda Ado ya iya yace"tayi hakuri asa musu hassana da husseina sai a dinga Kiran Hassanar da sunan A'indo ,anan kawai ta yarda,aiko akasa ma hassana sunan A'indo.
    Tunda suka taso halinsu yadan banbanta,a halayen su kadai zaka iya banbanta su,dan ko mahaifin su saide ya Kira  da sunan su tukon yake ganewa, mahaifiyar su kadai take ganesu,watarana, anma ranar da suke jin iskancin sai suyi kicin kicin ko kai waye bazaka ganesu ba.
  ,,,,,,,,,, Husseina mafadaciya ce ta gidan gaske,yanzu ne ta zage ku danbata da ita,bata wargi kai ko fada taga anayi idan taga ba'a danbata ba yanzu zata saye fadan ayi da ita,gata tantiriya .yayyin da Hassana A'indo ta hada kusan duka A'indo dai  itama tana masifar ,saide akway ta da wauwta irin ta yan fari,ga tsiwa,ga karambani,kome ita ta iya,ga karambani yi ba'a sa ta ba,ga keta,uwa uba kauyenci saide matsoraciya ce ta gidan gaba, tunda suka taso kowace da burin ta ,A'indo batada buri sai taje birni aikatau,ita duk yanda take ganin yan mata daidai ita na kauyen in sunje aikatau wasu har a wuleliyar mota ake kawo su,to sai ta d'auki wanan tasa a ranta cewar Yar aiki baban matsayi ne da ita ,wanda ko a birinin da wuya a samu mai matsayin Yar aiki.


   Sun adabi mutanen gari,kowa fata yake suyi auren nesa,saboda duk kyansu ba Mai zuwa wurin su saboda masifa irin tasu da ta uwar su,a yanzu haka sunada kusan shekaru goma sha bakway anma ba mijin aure Mahaifin su har ya gaji ya zuba ma sarautar Allah ido,A'indo kuwa a kauye ba Wanda baisan sunan ta ba,da ta biyo guri kace  sai kinyi A'indo sai tace Tantagariyar Yar Aiki ba."


   Ana cikin haka kanwar Mahaifin ta tazo daga birni wada take a birnin zinder tana zuwa ta samu yara ta d'auke su ta kaisu Aikatau a birini duk wata ana biyan iyayen su,itama tana samu.   A wani zuwa ne da tayi A'indo ta aza bala'i itama fa sai taje aikatau dinnan,ba yanda Mahaifin ta ya iya yace suje ,wata kila ta samu miji ita in ta fita daga kauyen tunda dai wanan kauyen ba Wanda ke son su da aure,suna kuka haka suka rabu ita da yar uwarta Husseina,tun daga lokacin da A'indo ta tafi  husseina   ta Kara zama masifafiya,ta adabi mutanen gari tace ai ta dalilin su yar uwarta ta tafi,saide fa tace itama dan lokaci take jira,anma in lokacin yayi duk inda yar uwarta ta tafi a birni itama sai ta bita.       Ranar da aka shigo birni da A'indo duk Wanda ke cik'in motar Saida ta cika cikin sa da dariya,ana tsakar tafiya ta fido kanta ta window mota tana ihu wai ga bishiyoyi can na gudu,akayita dariya.       
       kusan gidan biyar  aka kaita aikatau anma duk inda taje sai tayi ta'asa,su korota.
  A karo na shida ne aka kaita gidan wani dattijo Alhajin Sanmani Hamshak'kin Dan kasuwa ne Mai kudi,yayan sa biyar Mata biyu Maza uku.
   Alhassan shine da na farko dan kimanin shekaru talatin da biyar a duniya (35years) Yan biyu ne yar uwar tagwaitakar sa bata  zo da rai ba sai shi,a yanzu haka yana kasar waje aiki yake sodja ne baba na kasa da kasa Wanda duniya keji dashi kuma take takama dashi,saboda ilimin sa kwazo ,basirar sa,uwa uba yasan kan aikin sa .baya dariya ko kadan,babu Wanda zaice ya taba ganin dariyar sa,saide murmushi , murmushin ma iyakar sa lebo . Mai bi masa shine idrissa dan kimanin shekaru ashrin da biyar,sai khalipha dan kimanin shekaru ashrin da uku suna karatu,sai halissa Yar shekara ashrin da biyu tayi aure a Niamey shekara biyu da ta huce,sai auta   khalissa, yar kimanin shekaru goma sha bakway su suna karatu ne.
  Sai mahaifiyar su Hajiya saude datijuwa Yar kimanin shekaru arba'in da biyar.    Katon gida ne sosai tsarare ,Wanda aka kashe masa naira wajen tsara sa ,ginin ma ginin   turai ne, yan aiki gidan kusan ma'aikata goma sha tara ne,kowace da ranar aikin ta, bayan masu gadin gidan da masu tsaron lfy masu gidan su ba'a sasu a lisafi ba,Hajiya saude duk masu gyaran falon da ake kawo mata Sam bata wani ganin kyan akin su ita tafi so in ta fito falo taga ko Ina kal kal yana walkiya,hakan yasa tasa a Nemo  mata Yar aiki ta kauye a cewar ta su suka fi aiki domin basa Wasa da aiki suna sakin jikin su suyi aiki basa gajiya.


   Hakance yasa Anty najin irin Yan aikin da Hajiya keso ta kawo A'INDO gidan yau ai tun a k'ofa ta tatare siket zata arta a guje Saida Antyn tata da ta gane nufin ta ta rike hanun ta kam,tayita lalaba ta sanan suka shigo..

DOCUMENT INFOA'INDO TANTAGARARRIYAR YAR AIKI complete
Name A'INDO TANTAGARARRIYAR YAR AIKI
Size 483kb
Author Maimuna AbdullahI
File Type doc
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 17 September, 2020
descriptionhausa FICTIONDOWNLOAD DOCUMENT


download KUYANGA complete Hausa Novel documentSHIMFIDA


Sarki Abdallah Adalin Sarki ne mutum me kamala da Son talakawansa Wanda yake da mata Uku sai yara biyu matarsa ta farko uwar gidan itace Hauwa,u Anace mata *UMMAH*


Mebi mata itace Saratu *MAMAH* sai ta Uku amaryar sarki itace Fatima Amma *FATU* akece mataUMMAH macece me tsananin kishin gaske Tanada gadara da iko ita din yar gidan Sarautace tana buga ikonta agidan sarki domin sarki Abdallah yanaji da ita don haka take buga sha,aninta ackn gidan kowa shakkarta yakeyi tundaga fadawa,Bayi maxa da Kuyangin gidan da duk wanda ke cin gidan har kishiyoyinta D'anta Daya jal Yarima Anwar Wanda aka shagwaba shi da Gata Awaje yayi karatunsa Tundaga Sakandare har tagaba da Sakandaren wanda ba karamar tabarbarewar tarbiyya zamansa acan yaja masa ba don tun daya gama karatunsa yaki dawowa Yasamu guri xan babu kwaba babu harara 


Har saida labarin abinda yakeyi yadawo kunnan me martaba yai masa aike takakkiya aka taho dashiYayi masa fada sosai har kurari yaimasa yace inhar baidaina ba zai yi masa Aure ackn dangi zai laluba yadaura masa Aure da koma wacece

Aikin Anwar acan neman matan banza turawan nan sun sassanshi haka abokan banza yake mu,amula dasu basu da aikin komai saibin club club ana lolewa da mata anashan Giya ana raye raye Amma yafi Ronce da wata baturiya data nace masa mesuna RIHANNA wacce duk wulakancinsa takan shanye Abu daya yasa yake d'anshan mintinta tasan takan iya kulawa da d'a namiji duk luggar yaudara da iya Romance ta kware

Inda tayi musu zarra kenan gata da kishin tsiya tasha zane mata masu kawo masa hari Amma ahakan yake yakiceta yaje yashana da wacce yakeso danma tana shakkarsa da bazata bari yasakebaAnwar yanada isa da jinkai jinsa yake tamkar sarkin wani zubin to kullum azuciyarsa yana jin kome zaiyi babu wanda ya isa yakawo masa cikas tunda shi din dan sarkine me jiran gado

Mahaifiyarsa ke kara sakawa yaji izxa aransa akullum takan nusarsa cewar shine sarkin gobe duk da shi bawani son yazama sarki yakeyiba tunda yasan inya zama sarki dole yazauna guri guda kuma yabar duk abinda yakeyi knn.Sarki Abdallah akullum cikin bakin cikin Abinda dansa Anwar yakeyi yakeji aransa wanda yarasa yadda zaiyi dashi don yakintsu tunda shine babban dansa wanda wataran dole shine sarki agarin

Yasan da cewar Mahaifiyarsa ke xugashi tunda yahaneshi da zaman turai tace abarshi yahuta acan kafin wani lokaci bata son abinda zai bata masa raiSauran matan Sarki su idone nasu domin ta tsakiya MAMAH bata taba haihuwa ba itako Amaryar sarki FATU ta haifi Danta namiji tsiransu shekara biyar da Anwar yaron sunansa LAMIDO

Ummah bata kaunar FATU da D'anta sbd Fatun bata dade da zuwa gidanba ta samu ciki 

Ko MAMAH data rigata xuwa bata qullaci fatun ba domin MAMAH macece me tawakkali duniya bata dametabaKowane d'a  daga cikinsu tadaukeshi tamkar ita ta haifeshi

Amma tun tasowarsu da suka girma sai tafi kaunar Lamido domin shi yarone me hankali magana ma bata dameshiba a Nigeria yayi karatunsa

Lokacin daya isa shiga jami,a alokacin Sarki yaso turashi Turai shima Amma sai FATU taki amincewa sbd a ganinnta xaman turai ga yaro ba uwa ba uba na bata yaro da canza masa halinsa mekyau zuwa mara kyau tunda shima Anwar dayaje ba haka yakeba ada daga baya yakoyo wasu dabi'unSarki bai bata rai akn hknba domin takawo masa kwararan hujjojinta akan rashin son zuwan nata Turai yakuma gamsu

MAMAH ma bataga laifin taba domin tasan komai kuma kansu ahade yake su biyun

Sautari UMMAH takance wai sun hade mata kai 

Sukuwa shakkarta da sukeyine yasa basa shiga Sabgarta******

Tun Dawowar da Anwar yayi Nigeria kusan wata biyar yaji yagaji da zaman atakure yake baya futa club balle korawa da neman mata sbd babu dama duk inda yayi ido akansa suke inma yayi awajen gari Sarki zai iyaji azo ace yabatawa gidan suna shiyasa yafison yafita awayRihanna tayi ta damunsa akan inhar bai dawo Turai ba zata hado kayanta ta biyoshi ta nemi inda yake 

Hankalinsa yadaga dan yasan zata iya shiko yasan inhar tazo kashinsa yagama bushewa ackn gidanBa shiri yahau hada kayan dazai tafi dasu domin yai mata Alqawarin zaitaho cikin Satin domin ma kwana biyu yabata zaitafin

Da tunanin yanda zaishawo kan Sarki yabarshi yatafin yashiga cikin gidan Bangaren Mahaifiyarsa domin yafara kai mata zancen su samo mafita tukunYana tafe afarfajiyar gidan yana tafiyar Jinkai da wani shankamshi da Rangaji ackn Shigar Alfarma ta sarauta

Bayi maza Da kuyangu mata nata aiyuka suna wuceshi tareda durkusawa suna kai gaisuwarsu ga Yarima sarkin gobe

Wata *KUYANGA* Yakurawa idanu dayaga tanata sharar gurin ajiye dawakai kanta ba dankwali dan gyalen data yane kanta ya xame bata sanibaFarace shar gata da hips ga nashanu suncika  mata kirji

Ta dago zata bar gurin yakwalla mata kira

Aguje takaraso gareshi da biyayya ta durkusa tana gaidashi

Yakara kallonta na sakanni kana yace ckn shanqamshi "me kikeyi acan?

Da rawar murya tace "ina..,ina yin..,Shara nakeyi...

Yace "Dama Sharar gurin Dawakai nakune mata kona Bayi Maza?

Tayi kasa da kai tace ckn rage murya "Allah yataimaki Yarima tuba nakeyi ba aikina bane MAHBUB nake tayawa yatafi wani uzurin.

Yace "MAHBUB!wanene kuma *MAHBUB?* Tahau kame kame tazaci ko laifi tayi

Tace "Abokin shawaratane tamu tazo daya.shima yana tayani Aiki shiyasa nake tayashi

Ayanda take maganar yabashi Sha,awa bakinta me kama da anzana heart yatsurawa idanu yaga tana motsashi ahankali

Koda tayi shiru shima shirun yayi yana kallonta kawai

Wani abu yaringa ayyanawa aransa

Dataji shi shiru saita dago kanta dasauri tayi tsammanin yatafine saitaga ashe yana gun Tayi saurin yin kas da kanta don gudun kada suhada idanu

Yace mata "meye sunanki?

Tace " sunana *KUYANGA* !!

Yace "ke Sunanki nace zaki fadamin na gaskiy KUYANGA ba suna bane aguna wannan kalmar larabcine abangaren hausa kuma ace Baiwa.

Tace "Sunana *ZEENATU* 

Ya gyada kai kawai yawuceta yana kara ayyana abubuwa ackn ransa

Koda yashiga cikin Dakin Mahaifiyar tasa tararta yayi hadimanta na mata hidima daga me matsa mata kafa ana mata tausa sai meyi mata furfita saikuma masu bare mata ayaba tana karba tanaci
Yana shiga hadiman suka miko tasu gaisuwar xuwa gareshi 

Ya amsa da ka

Ta nuna musu kofa tareda alamun sufuta subasu guri

Saida suka futa kana yagyara zama yace "UMMAH Barkanki da warhaka

Tayi murmushi " Yawwa barkanka Abin faharina yarima Mejiran gado sarkin gobe da yardar Allah.Yayi murmushi yace "Uwata maganin kukana yauma gani gabanki nakawo kukana nasan banda matsala tabangarenki zaki sharen hawaye Mai martaba kawai nakeji 


Tace "fadi ko meyeshi zanmaka zankuma saka ayi maka 

Yace "Ummah inaso inkoma Turai nagaji da zaman Nigeria niba aiki nake futaba kusan kullum nake gida bana motsa jiki kewa ta dameni kitaimakamin kisa baki me martaba yabarni intafi.
Tayi murmushi "Angama Yarima yaushe kake son katafin?

Yace "Jibi nashirya tafiyar

Tace "Jibi jibin nan? Amma baiyi kusaba kuwa nikaina bason kayi nesa dani nakeba gashi kaida akeso kahaye karaga wataran yaxa,ayi aga baka xama abaka.Yace "kada kidamu da Wannan Ummah na wataran ai dole inxauna din nidai yanzu kiyimin kokari intafi

Tace "kada kadamu kamar katafi kagama zanyiwa TAKAWA maganar ayau.


Yayi murmushi yace "Yawwa nagode Ummah saidai kuma.……

yai shiru yana sosa keya

Tace "ehe!fadi mana yakai shiru kafadi komeye in akwai bazai gagara ba zanmaka.Yace ckn rage murya "Saidai naga wata yarinya awaje ackn KUYANGU  zanso mutafi da ita tayimin Rakiya domin ta hidimta mini acan.


Murmushi tayi tace "bakada wannan matsalar kowannensu akarkashinka suke kanada ikon kowanne bawa agidannan ko kuyangu dan haka kasa aranka kamar ka tafi da ita kagama yatake yarinyar?

Take yahau kwatantata

Tagano ko wa yake nufi domin KUYANGA Zeenatu tafi kaf kuyangun gidan Nutsuwa  dakyawun yanayi tanada kyau nagani afurta 

Jin mahaifiyar tasa ta Amince masa yasa yaita xuba mata godiya


Shiyasa yake matuqar son mahaifiyar tasa baitaba neman abu ta bangarenta yarasaba tana son akullum tafaranta masa bata son laifinsa

Koda yafuto farfajiyar gidan baza ido yaitayi ko zai sake ganinta

Amma baiyi sa.ar ganin kome kamartaba
Tsaki yaja Aransa yace "to meye nawa nadamuwa da son ganinta Alhalin ita zata zamo gadon baccina ita xata xamo jin dadina ita zata zamo komai nawa sai yadda nayi da ita

KUYANGA complete
Name KUYANGA
Size 179kb
Author Nabilancy
File Type doc
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 17 September, 2020
descriptionhausa FICTION


download MURMUSHIN ALKAWARI complet hausa novel document


DANDANO

Nas acikin duk kyawawan matan dana taba baka labarinsu abaya irin su tani da kyakkyawa ummi kawar mabaruka gurguwa babu wacce takai koda rabin kyawun FALMATA. Sidi mai jaka yace dani yana dubana.

Wacece kuma Falmata?

Itace mace ta farko da nake son saka maka zaren labarinta yanzun nan idan Allah yaso. Sidi mai jaka ya amsa min kai tsaye. Nikuwa sai na girgiza kai cikin tsananin shakkar jin abinda yace kana nace dashi a tausashe.

Yanzu ashe baba sidi har akwai wata mace wai ita falmata da za'ace wai tafi ummin nan kawar mabaruka kyawu? Haba baba jifa sunanta wai falmata saikace wata hula. Ni sunanta ma baiyi kama da sunayen kyawawa ba. Baba sidi ya kalleni cikin murmushi kana ya dada karyar goro ya jefa bakinsa yace.

Nas kenan to ai abinda nake so ka gane shine kyawun fuska daban kyawun suna daban kuma abinda nake so ka sani shine falmata tana daya daga cikin kyawawan mata na wannan zamani. Ayadda na sami labari ita kanta falmata tana kiran kanta da kyakkyaw haka nan alokacin da take budurwa kafin ta auri SAIFULLAHI wani saurayinta ya taba cewa da ita.

Kai falmata wallahi kyawunki yafi kyawun kudi akan doron kasa. Gashi idan kika bata rai sainaga kin kara kyawu idan ko kikayi murmushi Wallahi numfashina har daukewa yakeyi saboda shauki...

Kana nufin kasa dani ita falmatan matar aure ce? Na katse shi da wannan tambayar. Baba sidi ya gyara zama akan tsohuwar kujerar kana yayi gyaran murya yace.

Haba Nas me kake ci na baka na zuba kaidai bani aron kunnuwanka kasha labari.

Na gyara zama nace Naba Ka.

Yauwa to kamar yadda nace dakai tun farko inason ka dauki zuciyarka cancak ka mayar da ita cikin wani kayataccen dakin shakatawa wanda ke dauke da kayan alatu acikin garin Borno.

Na mayar da zuciyar tawa. Nace dashi ina mai tunanin irin zaren da wannan tsoho zai saka min awannan rana. Sidi mai jaka ya dada gyara zama sannan yafara cewa.

.

Karfe biyar da biyar na yammacin wannan lahadi wata farar kofa ta bude sannan wata kyakkyawar halitta tafito daga cikin bandaki sannu ahankali tana rausaya kamar bishiyar turare ta ratso kan tattausan kilishin dake lullube da dandasheshen dakin shakatawar tana tafe tana wakar wani fitaccen fim na hausa. Alokacin data kawo tsakiyar dakin shakatawar tana wake tana rausaya ji takeyi kamar itace ainihin yarinyar dake wannan waka acikin fim din data Gani.

Wannan kyakykyawar halittar sunanta Falmata fadin kyawunta kauyanci ne kokuma bata lokaci domin za'a iya asarar takardu da ruwan alkamali masu yawan gaske kafin a zayyane surar wannan kyakkyawa.

Kamar yadda ta saba yau ma falmata daga ita sai daurin kirji da wani tattausan shudin kyalle mai taushi haka ta shigo falon in ka dauke wannan daurin kirjin jikinta tik take kamar dankali. Kanta babu dan kwali sai gashin kana yalo yalo baki sidik yana sheki ya kwanto mata har gadon baya. Tun da take ba'a tabayi mata kitso ba domin koda anyi ma anyi a abanza don ko rabin sa'a bayayi zai warware saboda tsabar santsin gashinta.

Sannu ahankali falmata ta nufi jikin katon madubin sannan ta janyo wata yar kujera mai doron baya ta zauna sannan ta dubi kyakkyawar halittarta ajikin madubin tayi murmushi.

Sannunki yarinya falmata... Kyawu dai kam Allah yabaki.... Saidai kuma bakiyi dacen miji ba. Tace da kanta lokaci guda kuma tana kokarin goge ruwan dake diga daga cikin lallausan gashinta falmata ta dubi fararen idanunta sannan sai jajajaja bakake bakaken lebben bakinta suka fadada da murmushin alkawari ga wanda yayi dace take kaunarsa sannan saitaci gaba da rera wakar fim dinta tana kwalliya abinta. Alokacin babu wani mahaluki aduniya daya isa yace wai acikin bakin ciki mara misaltuwa take domin na farko dai fuskarta a washe take lebbanta dauke da murmushi gashi kuma tana rera waka abinda harda rausayawa.

Tsahon kusan sa'a guda ta share tana shafe shafe da goge goge daga karshe dai ta dubi kanta duba na karshe ajikin madubi saitayiwa kanta murmushi domin tayi farin ciki da abindata gani takuma riga tasan cewa ko iblishi ne shi bai isa yaganta ya dauke kai ba. Dole ne hankalinsa ya kwanta da ita. Dolene ya amince da ita ayammacin wannan rana mai kunshe da manufarta ta aiwatar da boyayyen sirrin dake zuciyarta yana ci ganga-ganga kamar wutar makera.

Falmata ta shige wani dan daki ba'a dade ba sai gata ta fito da wasu shudayen kaya riga da wando dinkin fakistan wadanda sukayi matukar matse jikinta gamgam. Suka kuma fito da boyayyiyar halittar da Allah yayi mata afili wannan shiyasa falmata kurawa jikin katon madubin idanu akaro na biyu ta sake nazarin kanta.

Falmata tariga tasan ita kyakkyawa ce domin tun tana yar kankanuwa mahaifinta ke kiranta da kyakkyawa uwarta ma kyakykyawa Take kiranta dashi yan ajinsu ma yan uwanta mata a fimare sun sha cewa da ita kyakykyawa ce amma a fakaice. Domin wata sa'ar sai daya daga cikin daliban mata ta dubi falmata tace kai Allah yaban gashi irin na falmata wata babbar kawar falmata ta taba cewaWata babbar kawar falmata ta taba cewa ba abinda take son falmata dashi sai tsayinta.

Irin wadannan batutuwa su saka sa tun falmata bata kula har dai ta ankara da cewa ashe dai itama kyakkyawa ce.

Dan haka ayanzu data dada kallon kanta jikin madubin saita dauki turare ta fesa ta dada daukar wata kalar daban ta fesa sannu ahankali saida ta fesa sama da kala bakwai sannan saita wuce kai tsaye ta zauna akujerar dake kallon kofar katon dakin shakatawar ta fara zaman jiran maigidanta saifullahi.

Karfe shida saura kwata na yamma saifullahi ya karaso gida tun kafin ya shigo dakin shakatawar yaji kamshin turare ye bugi hancinsa abin yabashi mamaki domin ya riga yasan ayadda matar tasa ta tsane shi batayin kwalliya don shi sai in zata fita unguwa wannan duk bata dame shi ba domin ya riga yasan ko matarsa tayi wanka ko kada tayi ko tayi kwalliya ko kada tayi ko tayi direshin ko kada tayi kai aduk halin datake ciki kyawunya bai taba gushewa ba kamar yadda kaunarta bata gushewa cikin zuciyarsa ada.... Dacan kafin idanunsa su kai kan babbar aminiyarta INYAMI.

Cikin tsananin mamaki saifullahi ya shigo cikin dakin sanye da babbar riga da yar ciki da wandonta kansa matse da rantsatstsiyar hula tangaran hannun na dauke da bakar jaka wacce awani lokaci daya wuce babban direbansa MUDI ne ke rako shi da jakar har cikin dakin amma tun daga ranar daya auri falmata sai ya haramtawa direban shigowa musamman ma dayake direban ya fishi dan kyawun gani. Afuska nesa ba kusa ba. Saifullahi baki ne dogo kakkaura yana sheki kamar an shafa masa shuni saboda baki yanada tarin gashin baki kamar tsohon soja hakanan yanada tarin gashin kai duguzunzum kamar shekar ungulu adan sa'ar dayake saurayi sosai ashekarun alif tari tara da tamanin cinyewar kenan da burgewa ka ajiye suma duguzunzum babu ko tajewa wannan tsohuwar al'ada ita ke biye da saifullahi har zuwa wannan lokaci dayake dan shekara arba'in da biyu kaida ka dube shi ka dubi falmata saika ga kamar hasken fitilar kwai ne da na hasken rana. Dayawa daga cikin mutane sunyi ittafakin cewa in banda al'amari na masu gidan rana saifullahi bai isa debowo falmata ruwa wanka ba ballantana na sha.

.

Falmata ta mike tsaye cikin fara'a tana rausaya ta tare shi.

Sannu da zuwa Saifu. Tace dashi kana ta karbi jakar dake hannunsa. Saifullahi yayi tsaye sororo cikin tsananin kaduwa da wannan sauyin yanayi na bazata domin shi a tunaninsa bayan abinda yafaru a yammacin jiya yau idan suka fara rikici sai makwabta sunzo rabiya. Amma abin mamaki sai gashi ta karbe shi da murmushi harda ce masa SAIFU.

Rabon dayaji ta kira shi da sunansa tun ran daren amarcinsu na farko awannan ma sunansa ta kira ta zaga.

Yaya naga ka zuba min idanu. Cire rigar mana kasha iska. Tace dashi kana ta kashe masa idanu cikin rausaya ta dora jakar akan kujera kana ta matso kusa dashi ta cire babbar rigarsa da hularsa ta jefa kan kujera sannan ta kama hannunsa ta janyo shi daf da kirjinsa tace a tausashe.

Ko kaifa. Yanzu bakafi jin iska ba?

Saifullahi ya gyada kai kamar jangwalangwadan kadangare, domin yana cikin tsananin kaduwa falmata ta kama hannunsa shikuma yana biye da ita kamar tunkiya lokaci lokaci yana satar kallon jikinta wanda ke ta faman rawa acikin matsatstsun kayan kamar roba. Ga mamakinsa saiyaji kwarjininta da kamshin dake tashi daga jikinta duk sun ruda shi rabon da hannunsa ya taba hannunta anfi wata biyu.

Sannu ahankali har takaishi dakin kwanansu ma'abocin kawa da wani fankadeden gadon alfarma mai kamar filin wasan kwallon kafa. Gadon dauke yake da wata jijjigegiyar katifa mai numfashi wacce ko kobo ka jefa akanta sai yayi tsalle ya fadi kasa. Suna zuwa daf da gadon sai falmata ta kama kafadarsa a tausashe ta zaunar dashi sannan ta dube shi da tattausan MURMUSHIN ALKAWARI tace... Ina zuwa saifu. Cikin sauri ta fice daga dakin saifu yabita da kallo sannan iya kumshe idanu yana Allah Allah tayi sauri ta dawo azuciyarsa yana cewa da ace kullum haka takeyi min me zai hadani da kawarta Inyami? Ba'a dade ba saigata dauke da wani farin faranti mai dan fadi wanda ke dauke yankakkun tufa dakuma kofi mai dauke da sassanyar tataccen ruwan ya'yan itatuwa dangin zaki. Falmata ta ajiye farantin agefen gadon sannan ta matsu kuda da mijinta ta dora cinyarta akan tasa tace a tausashe.

Duk ka gaji dubi idanunka yadda sukayi jajur da alama barci kakeji?

Akaro na farko sai saifullahi ya jefeta da murmushi sannan yace. Wallahi kuwa kamar kin sani murmushin falmata yafadada lokaci kuma ta dauko tataccen ruwan ya'yan itatuwa ta mika kusa da bakinsa. Jikinsa na rawa ya karbi lemon wani farin ciki da bege gamida kunyar cin amanar da yayi mata suka taru suka narkar da zuciyarsa ko daya dubi kyakkyawar matar dake zaune ajikinsa tana bashi ruwan zaki abaki kamar wani karamin yaro sai zuciyarsa ta karye nan da nan wani zazzafan hawaye ya fara sartu akan fuskarsa idan har falmata taga hawayen to bata nuna alama ba.

.

Falmata ya kira sunanta a sanyaye.

Meyasa ki sauya irin halayyarki agareni? Falmata ta dubeshi da murmushi tace.

Gani nayi lokaci yayi daya kamata na rungumi mijina hannu bibbiyu na shayar dashi ruwan kauna. Saifullahi ya dubeta cikin shakka.

Yanzu duk bayan cin amanar danayi miki jiya bakiyi fushi dani ba saikika kara kaunata? Falmata ta lumshe idanu cikin murmushi sannan saita langwabe kai ta kwanta akan kafadarsa kamshin mai da turaren dake jikin gashinta ya bugi hancinsa.

Kwanta ka huta saifuna. Kabar wani tone tone abinda yafaru ya riga ya wuce saidai kawai a kori gaba. Falmata tace dashi a sanyaye sannan saita tura shi ahankali da kyawawan hannunta saifullahi ya kwanta akan gadon idanunsa akan kyakkyawar fuskarta.

Tun da nake aduniya falmata ban taba sanin abinda ake kira da SO kulawa da kuma dadin aure ba. Sai yanzu da kika sadaukar da kanki agareni. Falmata ta matsa daf dashi ta kwanta agefen jikinsa akusa dashi sannan ta dora hannunta akansa tafara shafa gashin kansa mai taurin tsiya kamar ciyawar kan iyaka. Tana cewa dashi a tausashe.

Kada ka dami zuciyarka da tunanin shudadden al'amari ka kwanta ka huta idan ka tashi ma tattauna... Kaji saifuna. Saifullahi yaji tamkar amafarki yake ganin wannan al'amari dan haka sa'ar da ya lumshe idanunsa sai ya sake bude idanunsa domin a tunaninsa tabbas mafarki yakeyi. Koda ya bude idanun sai yayi ido biyu da falmata har yanzu tana nan kwance akusa dashi ta kura masa idanu cikin murmushi, hannunta akan kirjinsa.

Ina matukar son murmushin nan naki falmata. Falmata ta saki wata tattausar dariya mai kamar busar sarewa sa'ar dataji abinda ya ce. Sannan saita dada matsawa jikinsa kana ta kara bakinta agefen kunnensa tace.

MURMUSHIN ALKAWARI ne nakeyi ma. Saifullahi ya lumshe idanu yace. Murmushin alkawarin me? Falmata ta shafi fuskarsa tace.

Murmushin alkawarin daga yau din nan har abada bazamu sake fada ba da juna. Wannan batu shi ya dada tausasa zuciyar saifullahi ga mamakinsa saiyaji duk gabobin jikinsa sunyi lakwas ba'a dade ba sai ya fara wani kwakkwaran munshari kamar rago barci ya daukeshi.

Tsahon mintuna goma falmata na jikinsa tana kallon fuskarsa azahiri amma abadini bashi take kallo ba.

Can saita fara janye jikinta a hankali har saida tabar jikinsa sannan saita tashi zaune akan gadon akwai sauyin yanayi na lokaci guda akan kyakkyawar fuskar ma'abociyar murmushin alkawari. Cikin sanda saita dage rigarta sannan ta tura siraran yan yatsunta kamar budar idanu saita zaro wata sharbebiyar wuka mai baki biyu kamar bakin damo ta juya wukar ahannunta ahankali kamar mai wasa da yar tsanar kashi kana saita dubi Saifullahi ta kuma dubi katon dumbinsa tayi murmushi sannan saita runtse idanu ta rike wukar da karfi da hannu biyu ta daga sama sannan ta soka wukar da karfi atsakiyar tumbinsa Cus! Saifullahi ya farka a gigice adaidai lokacin da falmata ta zare wukar sannan ta sake caba masa aciki saifullahi ya kwalla kara sannan yafara haure haure falmata tayi tsalle daga kan gadon ta diro kasa sannan ta dubi Saifullahi wanda tuni har ya daina motsi harshensa ya zaro waje tace cikin murmushi.

Ai na fada ma daga yau bazamu sakeyin fada ba. Tana gama fadin haka saita juya cikin sauri ta fice daga dakin sannan ta rufe kofar da karfi ta nufi cikin falo jikinta na rawa.

.

Sidi mai jaka yayi shiru sa'ar dayazo nan ya dubeni da murmushi yace.

Nas kaji me kyan dan maciji ko? Bakina na rawa na dube shi nace.

Kada dai kace dani har zaren labarin wannan ya kare? Sidi mai jaka ya fashe da dariya yace.

Kaida kace bazaiyi dadi ba? Menene kuma na damuwa da ya kare ko bai kare ba?

Haba baba sidi don Allah kaci gaba....wai kana nufin wannan marar imanin mayaudariya kashe shi tayi da gaske? Sidi mai jaka ya furzar da duddugar goron data taru abakinsa kana yace.

Tun daka fara jin dadin labarin bari mu koma cikin falon muga abinda falmata keyi ai baka ma ji komai ba awannan labarin me akayi da maza inji karya? Abin ma da yanzu muka fara ai labari saima tubanina ya karaso tukunna. Ya danyi shiru sannan sai yace.

.

Nas sa'ar da falmata ta shigo dakin shakatawar jikinta na rawa saita wuce kai tsaye zuwa bandakin datayi wanka dazu aciki tana zuwa saita kalli mudubi. Tsoro da fargaba suka damki zuciyarta sa'ar data ga duk kammninta sun sauya kwalliyarta ta baci fuskarta tayi fari fat. Kamar taga fatalwa. Cikin sauri ta dauke kanta daga kan madubin sannan ta nufi inda komin wanka na tangaran yake jikinta na rawa ta cire kyawawan kayan dake jikinta ta watsar gefe guda domin amfaninsu agareta ya wuce. Jikinta na rawa tsirara saita shiga cikin komin wankan sannan ta kunna shawa.

Sassanyan ruwan ya fara wanke kanta sannan sai gangar jikin.

Wannan shi yafara dakushe kaduwar dake jikinta domin kaduwa ce kawai amma ko kusa ko alama bata nadamar abinda tayiwa mijin nata domin maci amana ne... Maci amana wanda yaci amanata duk kuwa da aurensa danayi alhali bana kaunarsa falmata.

Koda sassanyar ruwan shawar yaci gaba da kwaranya atsakiyar

Koda sassanyar ruwan shawar yaci gaba da kwaranya atsakiyar kanta da bayanta sai zuciyarta ta tafi dofon tunanin wani shudadden lokaci shekara kusan guda kenan kafin ta auri Saifulahi.

.

Tun sa'ar da wannan kyakkyawar mata tafara kaiwa munzalin 'ya mace nas sai Allah ya jarabce ta da kaunar wani saurayi wanda bata taba ganinsa azahiri ba sai acikin akwatin talabijin.

Wannan saurayi shi Falmata ta fara kauna aduniya kuma akanta ta kare kauna haka nan har zuwa lokacin data soke mijinta Saifullahi da wuka babu wanda wutar begensa ke ruruwa akullum kwanan duniya sai wannan saurayi.

INFO 

MURMUSHIN ALKAWARI complete
Name MURMUSHIN ALKAWARI
Size 85kb
Author Nazir Adam Salih
File Type doc
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 15 September, 2020
descriptionhausa FICTION
Hey, we've just launched a new custom color Blogger template. You'll like it - https://t.co/quGl87I2PZ
Join Our Newsletter