Main menu

Pages

A ta dalilin Fim na koyi Hausa - Amina Amal

A Ta Dalilin Fim Na Koyi Hausa – Amina Amal

Fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood Amina Muhammad, wacce aka fi sani da Amina Amal Kuma yar asalin kasar Kamaru, ta bayyana cewar, kokarin ta na son ta yi fim ne, yasa ta baro kasar ta, duk da cewar ba ta jin Hausa ta shigo Nigeria, kuma har ta samu kanta a cikin harkar fim, wadda a yanzu tana cikin fitattun jarumai da a ke dama wa da su.

Jarumar tun da farko ta bayyana cewar “kafin na zo Nigeria ban iya Hausa ba, don yaren da na ke ji fulatanci ne, da faransanci sai turanci, amma a yanzu ta sanadiyyar fim na iya Hausa.” Inji ta.

Also read Na so Yusuf Buhari kamar na mutu amman na rasa shi saboda mahaifina talaka ne

Ta ci gaba da cewar “A lokacin da zan fara fim na gamu da Matsaloli sosai, na farko ba na rashin jin Hausa, kuma fim din da Hausa a ke yi, sabida haka sai da na shafe wata shida ina koyon harshen Hausa, kuma gaskiya na yi farin ciki da hakan, kuma ina alfahari da fina-finan Kannywood, ga shi ta dalilin su na koyi Hausa, da al’adar wani gari da ba namu ba.” Inji shi.

Ta kara da cewar” Da aka zo za a fara fim din, sai aka ji Hausa ta ba ta gama Isa gangariya ba, don haka sai da aka kara mun watanni. Cikin ikon Allah na koyi Hausa na yi fim din farko Mai suna “Amal”, wanda da shi ne a ke yi mun lakabin Amina Amal,” a cewar ta.

Kazalika ta ce, “Kuma daga wannan lokacin na ci gaba da shiga fina-finai, har na zama fitacciyar jaruma, don haka ina godiya ga Allah da na samu wannan matsayin. Babu abin da na ke buri yanzu sai na yi rayuwa da kowa Lafiya. Iyaye na kullum suna yi mun addu’a, suna sanya mun albarka. Ina godiya ga masoya na bisa irin soyayyar da su ke nuna mun, Ina kuma addu’a Allah ya saka wa kowa da alheri. “Inji Amina Amal

Daga MuryarYanci

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Comments

table of contents title