Main menu

Pages

dalilin daya sa bama kama 'ya'yan masu kudi - hisbah

Hukumar hisba ta jihar kano ta fito ta fadi dalilin daya sanya ake yi musu korafe-korafe akan basa kama ‘ya ‘yan masu hannu da shuni, kana da masu mulki cikin wani zantawa da Freedom radio tayi da Babban Daraktan hukumar Dr. Aliyu Musa Aliyu Kibiya.

Dr. Aliyu Kibiya ya ce, Hisbah tana yin da’awa ga kowa da kowa, sai dai a bisa mataki-mataki. Saboda haka, irin salon da ake yiwa gama-garin mutane, ba shi ne wanda za a yiwa manyan mutane ba

Ya ci gaba da cewa “Mu yadda mu ke yiwa kallon abin, in aka ce shugaba ya yi laifi ba tarbiyyar musulunci ba ce, a je masallaci ana faɗa a lasifiƙa”.

“Akwai waɗanda suna da hanyar da za su samu shugaba su da shi, kuma dama aikin shi ne isar da saƙo, shi kuma Allah shi yake shiryarwa”.

Dr. Kibiya ya ƙarara nanata cewa, “Akwai irin da’awar da za a yiwa normal mutane (gama-gari), akwai kuma da’awar da za a yiwa shugabanni”.

sannan Freedom radio sun kuma tuntubar  Babban Kwamandan hukumar ta Hisbah Malam Muhammad Haruna Ibn Sina.

Ya ce, hukumar ta kama da yawa daga ƴaƴan masu kuɗi, kuma suna kan kamawa a kowane lokaci.

“Mun kama ƴaƴan masu kuɗi da yawa, kuma muna kamowa a koda yaushe”.

Comments

table of contents title