Main menu

Pages

Gaba daya 'yan matan fim karuwai ne - Tanimu Akawu

Jarumin Fina Finan Hausa Tanimu Akawu Yayo Magana Akan ‘Yan Matan Fim, A Cikin Wata Hira Da Akayi Da Shi A Wani Gidan Rediyon Dake Abuja.

jarumin ya bayyanawa gidan rediyon babu wani abun da matan Yan fim keyi ayanzu face bibiyan maza attajirai da Sarakai.

ya kuma cewa motar da hadiza gabon kadai ke hawa ta sayi motocinsa guda goma, yace shi yana hawan EOD ce da kudinsa na halal ya siyeta.

jarumin ya kuma bayar da misali da jaruma Maryam Yahaya inda yake cewa “Kallo kawai ta zo yi aka sanyata a cikin fim din Mansoor, amma yanzu wayoyin dake hannunta sun kai na kimanin dubu dari takwas, kasan kuwa ba a fim ta samu wannan kudin ba, saboda nawa ne duka ake biya a fim din?”

kana jarumin ya kuma cewa ” “Ko ni yanzu ka bani ‘yar fim na aura bazan aure ta ba, saboda na san abinda ke tafiya a harkar, yarinya tun ba ta da wayo take kallon mu muna yin fim amma yanzu ta zo cikin shekara daya ta samu kudin da bamu taba tunanin zamu samu ba, yaya za ayi ta dinga ganin girman mu.”

duk da mai gabatar da shirin ya Sabitu garba Mustapha, yayi mishi nuni da girman maganar da yake, inda yai masa nuni akan ya kamata ya tabbatar da sahihancin maganarsa, jarumin tanimu akawu ya ce da shi ai wanann maganar kowa ya santa.

Source ArewaBlog

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Comments

table of contents title