Main menu

Pages

Gwamnatin jihar kano zata dakatar da haska fim din aduniya

Gwamnatin jihar kano zata dakatar da haska fim din aduniya,

Gwamnatin Jihar kano zata yi wa fim din aduniya garambawul fim din da shahararren Jarumin nan na kanyywood Tijjani Asase ke daukar nauyi.

sanarwar ya biyo bayan da mujallar fim ta ruwaito cewa mai baiwa gwamna shawara a fagen makarantun tsangaya Sharif Ahmad Shu’aibu yayi sanarwar a jiya laraba inda yace sun yanke wannan hukuncin ne a bisa wasu korafe korafe da mutane suka shigar akan fim din

A cikin wata takardar sanarwa da mujallar ta samu, ofishin ya ce a taƙaice, “A sakamakon takardar da aka rubuta wa wannan ofishi mai albarka ta ƙorafi a kan shirin fim mai dogon zango ‘A Duniya’ mai dogon zango na kamfanin Brainscope, takardar mai kwanan wata 1/1/1443 9/08/2023, domin haka na ke rubuta wannan takarda don sheda wa al’uma da Gamayya mun karɓi saƙon takardar ƙorafi a kan wani sashe daga wannan fim. Gwamnati za ta yi umarni wajen kawo gyara a cikin wannan fim ‘A Duniya

“Mu na fatan za a ci gaba da ba wa gwamnatin Jihar Kano goyon baya da addu’a wajen cigaban addinin Musulunci da harkokin ilimi free education da makarantun mu na tsangaya masu albarka, da samar da tsaro a Jihar Kano baki ɗaya.

“Daga ƙarshe, mu na yi muku fatan alheri. Allah ya ba mu albarkar Ƙur’ani mai girma, amin. Mun gode.”

Gwamnatin jihar kano zata dakatar da haska fim din aduniya,

sai dai haryanzu ofishin na mai baiwa gwamna shawara bata shelanta takamaiman korafin da aka kawo musu ba akan fim din na Aduniya, hakanan basu fadi wani hukunci zasu yi ba.

A Duniya’ dai shiri ne da ake nunawa a wata tashar YouTube mai suna Zinariya wadda ta ke mallakin Asase.

Also Read Rahma sadau ta yi magana akan shigar Yar sarkin Kano

Shirin ya na nuna wasu daga cikin halayyar son zuciya da matasa su ke nunawa ta hanyar mutuwar zuciya tare da yin sace-sace wanda har ta kai su ga da-na-sanin rayuwa.

Idan kun tuna, mujallar Fim ta taɓa kawo wani rahoto na yadda wasu masu kallo a Kano su ka yi kukan cewa fim ɗin ya na ɓata tarbiyya ta hanyar koyar da muggan ɗabi’u ga matasa da su ka haɗa da tallata harkar daba da ƙwacen wayar hannu.

A lokacin, an yi raɗe-raɗin cewa wai har hukumomin tsaro sun dakatar da nuna fim ɗin.

Sai dai a labarin da mu ka wallafa, Asase ya ƙaryata zargin da ake yi wa fim ɗin, ya ce kawai ana yi masa hassada ne tare da rashin son ganin cigaban sa da wasu ke yi.

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Comments

table of contents title