Main menu

Pages

Hukumar hisba sun kama Umma shehu

Biyo bayan Kama sadiya haruna Da hukumar hisbah ta kano tayi bisa zargin ta da yada vlbidiyon batsa da kuma kalamai na batsa da sunan tallan magani.

Jaruma umma shehu ta fito ta kalubalanci hukumar hisbah inda ta bayyana cewa ba’a son shiga tsakanin Allah da bawansa inda ta nuna cewa suma hukumar hisbah akwai mazinata kar a sa ta kama sunan su.

Also Read Kotu ta tura Sadiya haruna makarantar islamiya na watanni shida

Sai dai Wannan kalamai nata sun batawa al’umma rai Musamman masu kishin addini inda suke ganin a cikin maganganun umma shehu akwai karancin fahimtar Addini inda aka mata raddi kala kala a shafukan sada zumunta har ya kai ta goge rubutun a shafinta.

bayan wannnan raddi da Jaruma Umma Shehu tayiwa hukumar ta hisba, Labari ya iso mana cewa hukumar sun kama jaruma Umma shehu akan wayannan kalamai nata garesu na kiransu da mazinata.

ga cikakken rahoton cikin bidiyo

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Comments

table of contents title