Main menu

Pages

Kotu ta tura Sadiya haruna makarantar islamiya na watanni shida

A jiya ne Litinin Hukumar Hisba ta gabatar da Sadiya Haruna Shahararriyar Mai sai da kayan mata a shafukan sada zumunta.

An gurfanar da ita ne a kotun Dake karkashin hukumar hisba inda aka tuhumeta da amfani da kalaman batsa a shafukanta na sada zumunta.

daga karshe dai alkalin kotun mai sharia Ali Dan zaki Ya yanke mata hukuncin a tafi da ita makarantar Islamiya na tsawon watanni shida domin ta koyi addinin islama.

kana mai sharia Ali dan zaki ya kuma tabbatar da cewa hukumar ta hisba zasu ke rakata har zuwa makarantar na Islamiya.

Sadiya Haruna dai kusan duk wani mai amfani da kafafen sada zumunta ya santa inda tayi fice a dukkan shafukanta musamman na Instagram wurin hawa wakokin hausa da kuma sai da maganin maza ga mata.

A watannin da suka wuce ta taba yin wani bidiyo rike da azzakarin roba tana nunawa mabiyanta tana fada masu alfanunshi, nan da nan wasu daga cikin mabiyanta sukai mata caa, inda daga karshe ta fito ta basu hakuri kuma tun daga wannan rana ba a kuma ganinta da Azzakarin roba ba.

hallau Sadiya haruna tana kiran kanta da sayyada sadiya haruna kasantuwar tana hawa wakokin yabon manzin Allah SWA.

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Comments

table of contents title