jarumi Mustapha Naburaska shahararren Mai wasan barkawanci ne a masana’antar Kannywood, ya fito cikin fushi don kare mai gidanshi Adam A Zango inda yayi kalamai kausasa cikin hausa.
Naburaska dai ya fito gaba gadi, a shafinsa na Instagram ganin yadda akaiwa maigidansa caa kowa na sukansa da mummunan kalma akan lamarinsa da Jaruma Ummi Rahab.
Also Read Rabuwar uwaka ubanka akayi tsakanin Adam Zango da Ummi Rahab
nan da nan jarumin ya sanya hotonsa dana Adam A zango inda ya rubuta wadanann kalaman cikin manyan baki
RUGUM BABBAN MOTSI KOWA YA GAJI BAI SABA BA. KA YI TAKA KA YI TA YARO. BA KA GOYO BA A GOYA KA. ADAM A ZANGO IKON ALLAH MAIGIDA NA NI MUSTAPHA BADAMASI NABRASKA BA ZAN MANTA DA KAI A RAYIWA TA BA. A KAN KA DUK WANDA YA TAƁA MUHIBBAR KA WLH WLH WLH SAI NA GA GYAUTO NA TSOHO KO NA TSOHUWA.”
Mustapha Naburaska

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel
Comments
Post a Comment