Nafi Bukatar Fitowa A Matar Aure A Fim Inji Jaruma Khadija Mustapha
ga dukkan masu jimirin kallon fina finan jaruma khadija Mustapha zasu tarar tafi fitowa a matar gida, ko matar mai arziki wanda hakan ya sanya da yawan mutane ke kiranta da matar manya.
bisa ga duba da hakan ya sanya jaridar dimokradiya suka tuntubeta akan yadda take ji idan mutane suka kirata da sunan Matar Manya , sannan yawancin fina finan da ta ke futowa a matsayin matan masu hannu da shuni, itace ke zabar roll din ko ko dai direkta ne ke zabar mata.
jarumar ta bashi amsa da cewa “To ni ina ganin masu fim din ne su ke ganin na fi dace wa da wannan matsayin da su ke dora ni a kai. Ba ni na ke zabar wa kai na ba, Amma kuma a matsayin ka na jarumi, sai ka duba ka gani, wane rol ne ya kamata ka yi, idan za a ba ka aiki, sabida wani na zuwa, kai a wajen ka ba wani abu ba ne, amma a wajen masu kallo sai ya zama wani abu, don haka, dole sai mutum ya na kiyaye wa”
jarumar ta cigaba da cewa “Amma ni a ra’ayi na, ina son a ba ni rol din da zai kasan ce matar aure a gidan ta, wannan rol din shi na fi so. Amma kuma babu wani rol din da zan ce ba zan fito ba, sai dai idan ya saba wa ka’idar addini na, in dai ya saba wa addini na, to gaskiya ba zan yi shi ba.”
daga karshe jarumar tayi kira ga masu kallo akan su riga yi musu hakuri da uzuri akan dukkan kuskuren da sukeyi, a maimakon hakan ta nemi da arunga yi musu nasiha bawai caccakarsu ba
Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel
Comments
Post a Comment