Datti Assalafy shahararren mai amfani da kafar sadarwar nan ya yi binciken kwakwaf akan lamarin dake faruwa tsakanin Jarumi Adam A Zango da Jaruma Ummi Rahab.
Datti Assalafy ya gano Cewa mahaifiyar Ummi Rahab ce ta mika Ummi A matsayin Amana ga jarumi Adam Zango tun lokacin Ummi na Karama kawo izuwa girmanta.
ABINDA YA RABA TSAKANINSU BA MAI KYAU BANE
ga abunda Datti Assalafy ya fadi
Ance mahaifiyar Ummi Rahab itace ta damka amanar ‘yarta wa Adam Zango tun tana yarinya karama bata balaga ba
Kuma Adam Zango ya sakata a fina-finai har duniya ta santa, Ummi Rahab tana hannun Adam Zango har zuwa yanzu da ta balaga ta tumbatsa tana ganin ta kai
Mahaifiyar Ummi Rahab ta rasu watanni kadan da suka wuce, sai gashi yanzu an wayi gari Adam Zango ya sallami Ummi Rahab, ita kuma tana masa gargadi da ya dena mata batanci imba haka ba zata tona masa asiri
Also read Zina Adam A zango yayi da ita ko ciki ya mata ya zubar ?
Kamar yadda aka saba Datti Assalafiy ya gudanar da bincike, kuma na samu tabbacin cewa tabbas Adam Zango ya rabu da Rahab, kuma rabuwar banza sukayi, rabuwar uwaka ubanka, na kuma samu bayani akan abinda ya rabasu har ita Rahab tayi barazanan tona masa asiri bayan BBC Hausa sunyi hira da Adam Zango a jiya Alhamis inda ya fadi wata kalma
Na fahimci cewa hakika mahaifiyar Ummi Rahab (Allah Ya jikanta) tayi babban kuskure da ta dauki amanar ‘yarta ta damkashi a hannun wanda shima yana bukatar a bashi tarbiyyah
Gaskiya wannan rayuwa rikon amana tayi karanci, cin amana ya yawaita, ba kowa ake bawa amana ba, wadanda ake ganin suna da tsoron Allah a wannan zamanin suna iya cin amana, balle ‘yan daudu masu lalata tarbiyyan al’ummah
Malaman tarbiyya Islama sunce, ko halal ce akwai wata halal din da ana barinta don kunya, balle abinda bai halalta ba
Shawaran da zan bamu shine:
Duk wanda Allah Ya bashi mata da ‘ya’ya musamman mata, to yayi kokarin basu tarbiyya ta addini, a wannan zamanin ba’a bada amanar mata, walau matarka na aure ko ‘yarka da ka haifa, idan suka samu tarbiyya da juriya suna sana’a ko mutuwa kayi zasu kubuta da taimakon Allah
Allah Ka tsare al’ummar Musulmin Kasar Hausa daga sharrin ‘yan Hausa film Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum
to dama kafin wannan rubutu Datty Assalafy yayi wani rubutu inda yake kira ga Jarumar da ta shiga hankalinta kafin tsoffin kuraye su lalata mata rayuwa kamar yadda sukai wa jaruma Maryam Booth.
daga bisani ya ce yana mamakin yadda Ummi Rahab ta fito duniya tana barazana ga Adam A Zango akan zata tona masa asiri muddin bai daina bata mata suna ba.
daga karshe yayi baiwa jarumar shawara akan ta samu miji tayi aure tun kafin rudin duniya da yan iska suyi mata illa.
Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel
Comments
Post a Comment