Rikici ya barke tsakanin Afakallahu da Falalu A dorayi
Shahararre kuma fasihin Direkta,jarumi kuma mai daukar nauyin fina finan hausa, Falalu A dorayi yayi wani rubutu a shafinsa na Instagram inda yake bayyana cewa, hukumar tace fina finai karkashin jagorancin Afakallahu bata kaytawa a ayyukanta tana zalunci da sonkai.
lamarin dai ya faru ne bayan cire sunan direkta Sunusi Oscar 442 daga cikin wani fim da masu fim din suka kai ga hukumar domin ta tace.
Also Read Gwamnatin jihar kano zata dakatar da haska fim din aduniya
falalu a dorayi ya nemi sunusi oscar daya kai kara kotu a cikin bayanansa inda yake cewa
“Censorship Board & AFAKALLAH
Ni na dauka yadda magriba tayi gari ya kusa wayewa.
Jagoran hukumar zai shiga hankalinsa.
Ni banga a inda dokar hukumar tace idan mutun baya tare da kai, in an kowa films nasa a cire sunansa. Babu a dokarku.
Na dauka wannan kama karyar an yi shi lokacin RABO ta wuce.
Sun bika, sunyi rigistar dole da kai, sun zuba kudi sunyi film, sun dau director sun biya. Sun kawo kace a cire sunan director, har films guda UKU.
Wai Ina hankalinmu yake tafiya ne Idan muna zalinci?
Ko dauka muke babu ranar sauka. Gaskiya cire sunan sunusi oscar 442 a saka na wani rashin adalci ne, da karya dokar kasa da tauyewa hakkin Dan kasa.
sunusi oscar 442 kana damar ka shigar da kara KOTU.
Wallhi ina da Tabbas zakai nasara.
An kafa dokar hukumar ne Domin ta kare Addini da Al’ada da kare muradin gwamnati da kare hakkin Yan masana’antar films.
Me yasa ake cin kare babu babbaka?”
censorship boardkano #Afakallahu
Oscar442 #falaluadorayi
Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel
Comments
Post a Comment