A cikin makon nan ne dai aka dinga ganin hotunan fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan wanda yake bi kasa-kasa domin da’awa da kuma kira ga al’ummar Musulmi, Mufti Menk, da Jaruma mai kayan mata, wacce tayi fice wajen jawo cece-kuce a shafukan sadarwa sakamakon bidiyo, hotuna da maganganu da ta saba yi wadanda ba su dace ba.
A jikin hoton dai an nuno fitaccen Malamin a cikin jirgi tare da Jaruma sun dauki hoto, duk da dai alamun da suka nuna babu fara’a sosai a fuskarshi, amma ita Jaruma an nuno fuskarta cikin fara’a da annushuwa da wannan hoto da ta dauka da Malamin.

Fitar wannan hoto ke da wuya mutane suka yi ta tofa albarkacin bakinsu, inda hakan ya sanya wani ya yiwa Malamin tambaya a wata manhaja ta tambayoyi dangane da wannan hoto
Mufti ya nuna bashi da masaniyaa akan wacece ita Jaruma din ma, ya bayyana cewa shi kawai yana zaune ta zo ta nemi ya dauki hoto da ita, ya ce bayan daukar hoton bai jima a wajen ba ma aka zo aka canja masa mazauni, saboda ma’aikatan jigrin suna ganin wajen bai kamace shi ba.
Akso Read Shin da gaske Rochas Okorocha Zai gina jami’ar Musulunci a Daura?
Malamin ya bayyana cewa sun dauki hoton ne a lokacin da ya taso daga birnin Addis Ababa zuwa Abuja, a jirgin Ethiopian Airlines, inda ya kara tabbatar da cewa shi bashi da masaniya dangane da kowacece ita, ga dai yadda hirar su tta kaya, mai tambayar ya bayyana cewa:

Sheikh, akwai wani hoto da kai da Jaruma, yaushe ne aka dauke shi? ~ Mai tambaya
Wacece wannan? ~Mufti Menk
Budurwa ‘yar Najeriya da ka zauna kusa da ita a jirgi. ~ Mai tambaya
Eh na tuna, a lokacin da muka taso daga Addis zuwa Abuja a Ethiopian Airlines kwanannan, akwai wata mata dake zaune a kusa dani. Bani da masaniya ko wacece ita, amma abinda zan iya tunawa ina zama, ta nemi na dauki hoto da ita. Cikin mintuna kalilan wata ‘yar uwa cikin Hijabi ta zo gare ni ta ce, “Sheikh, akwai kujera wacce babu kowa a layin gaba, zai fi dacewa ka zauna a wajen”, aikuwa haka na koma waccan kujerar. ~ Mufti Menk
Jaruma mace ce da tayi suna a Najeriya ~ Mai tambaya
Tsaya kafin ka kai gaba, bari na sake bayani dakyau akan cewa bani da masaniya akan kowacece ita ko kuma sunan da take dashi. Ma’aikatan jirgin ne suka bani wannan kujerar, kuma daga baya suka canja mini da wata. Ina rokon Allah ya ganar da ita da mu duka zuwa hanya madaidaiciya. ~ Mufti Menk
Ameen, nagode da lokacin da ka bayar da kuma bayani Sheikh ~ Mai tambaya.
Daga Arewablogg
Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel
Comments
Post a Comment