Shin da gaske Rochas Okorocha Zai gina jami’ar Musulunci a Daura?
Daga, Ibrahim M Bawa
Tsohon Gwamnan jihar Imo kuma sanata a
yanzun Rochas Okorocha ya bayyana cewa
zai gina Jami’ar musulunci a garin Daura,
mahaifar shugaban kasa Buhari, sannankuma da karatu da dakunan kwana dukkyauta ne ga daliban da za su yi karatu a ciki.
Za a iya tuna cewa a kwanannan ne Katsina
Daily Post News ta rawaito maku cewa, Mai
Martaba Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar
Faruk ya nada Okorochan a matsayin Maga
Alherin Kasar Hausa.
Also read Farfesa Attahiru Jega Zai fito Neman takarar shugaban kasa 2023.
Kamar yadda majiyar Katsina Daily Post
News ta Premium Times ta rawaito, a wanitaro da ya gudana ranar Asabar da Isah
Halidu ya wakilci Rochas Okorochan, ya
karanta sakon Rochas din da cewa,
“SabodaSarkin Daura ya bani babbar sarauta, donhaka nima zan bayar da babbar kyautar da baza a taba mantawa ba, zan gina Jami’ar
musulunci karkashin gidauniyata ta Rochas
Okorocha Foundation, inda zau dauke nauyin
kudin makaranta, sannan dakunan kwana
duk kyauta ne” Inji Okorocha
Comments
Post a Comment