Main menu

Pages

Sojojin sama sun kashe yan bindiga sama da 50 da suka buya a jejin Zamfara

Jirgin yakin sojojin Najeriya ya kashe yan ta’adda da dama a garin shinkafi dake zamfara.

jaridar Leadership ta ruwaito cewa Sojojin Nigerian basu tsaya iya nan ba inda suka yi shawagi suka je yankin Jammaga da kewayanta nan ma suka kashe yan bindiga.

harin da sojojin saman Nigeria suka kai a ranar lahadi ashirin da tara ga watan agusta, sunyi nasarar karkashe yan ta’addar Kachalla haru dama dukkan mafakansa kuma sun lalata sansaninsa.

daga cikin jami’an da suka fita aikin wani jami’i ya shaidawa PRNigeria, cewa sunyi nasara a dukkan hare-haren da suka kai a ranar.

Also Read Sheikh Mufti menk yayi bayani game da hotonsa tare da Jaruma mai kayan mata

yadda lamarin ya kasance

“A ranar 29 ga watan Agusta, 2021, da kimanin karfe 2:00 na rana, aka samu bayanin cewa ‘yan bindiga sama da 100 sun mamaye wata makaranta a kauyen Gidan Rijaya a garin Galadi, karamar hukumar Shinkafin jihar Zamfara.”

“Nan take jirgin yakin Alpha Jet da ke hannun Operation Hadarin Daji ya tashi, ya kai farmaki a yankin. A dalilin haka ya kashe tulin ‘yan bindiga, ya rugurguza makamansu.”

“Jirgin ya kuma yi barin wuta a tsaunukan Halilu Tubali a jejin Sububu. An ci nasara a duka wadannan hare-hare, ba tare da an yi wata asara ba face wani gini da aka rusa.”

Kimanin ‘Yan ta’adda nawa aka kashe

haryanzu PRNigeria bata tabbatar da adadin yan bindigar da aka kashe ba, sakamakon yawan baburan da aka ruguza a kauyen na gidan rijiya, sai dai ana hasashen sama da yan bindiga 50 ne suka rasa rayukansu.

Source LegitHausa

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Comments

table of contents title