Main menu

Pages

Daga Karshe an sulhunta Adama A Zango da Ummi Rahab

Daga karshe rigimar dake tsakanin Ummi Rahab da wasu daga cikin yaran Adam A Zango an sulhunta shi, rigimar ta samo ne bayan wani ‘ hatsaniyar da ta faru tsakanin shi Jarumi Adam A Zango da ita Ummi Rahab har Ummi Rahab din tayiwa Zango barazanar tona masa asiri, hakan ne ya fusata masoyan shi Adamu Zango da yaran sa, ya sanya suka dinga yiwa Ummi martanin wasu rubuce rubuce, da cikin sautin murya, harda cikin bidiyo,

Sai dai a cikin wadanda martanin nasu yafi tada kura akwai Abdul Babulaye da kuma Umar Bigshow, inda shi Umar ya yi rubutunsa a kasan bidiyon Ummi Rahab, shi kuma Abdul Babulaye yayi Video na raddi ga Ummi din, gami da kara bayyanin abinda ke tsaknin Ummi da Uban gidansa Zango.

Maganganun da Abdul da Umar ba su yiwa Ummi Rahab da masoyan Ummi dadi ba, inda hakan ya sa ta shigar da kara ga hukumar ‘yan sanda bisa zargin su da bata mata suna, da kuma sauran abubuwa da take tuhumar su da shi, a karshe aka gayyace su Ummi Da Adamu aka sulhuntasu tsakaninsu.

Join Our
<a href=”https://t.me/hausavirals”>Telegram Group</a>
Join Our
<a href=”https://twitter.com/hausanovels”>Twitter page</a>
Join Our
<a href=”https://facebook.com/hausaebooks”>Facebook page</a>
Join Our
<a href=”https://youtube.com/c/HAUSANOVELSTV24″>Youtube Channel</a>

Comments

table of contents title