Main menu

Pages

Gwamnatin nijeriya ta karbi sabbin Jiragen Yaki daga amurka

A hukumance gwamnatin Amurka ta mikawa Gwamnatin Nijeriya jiragen yaki na zamani wato A29 Super Tucani a wani bikin mika jiragen da akayi a sansanin sojojin saman nijeriya dake a filin Jirgin saman birnin tarayya Abuja

jawabinsa a wajen bikin mikawa Najeriya jiragen yakin, babban kwamandan Sojojin saman Amurka mai kula da Turai da nahiyar Afirka Genaral Jeff Harrigian ya ce mika wadannan jiragen n nuni da cewa akwai kyakkyawar alakar aiki tsakanin Amurka da Najeriya.

Wadannan jiragen yakin na Super Tucano anyi musu kyakkyawan tsari na sadarwa da sojojin kasa da sojojin ruwa, kasar Amurka hado musy da kayayyakin gyaransu wanda zai kai tswaon shekaru koda an bukaci hakan tsawon shekaru ta sa hannu wajen kara inganta wurare n da suka hada da sansanin jiragen saman sojin Najeriya dake Ka’inji.

Also Read Labari Da Ɗumi Ɗumi yadda Yan banga tare da Yan Sanda sun hallaka shugaban yan bindiga a jihar Neja

Kudi Dalar Amurka milyan (5.000M) ne Najeriya ta kashe wajen siyo wadannan jiregen yakin

Babban kwamandan sojojin saman Amurka dake mai kula da Turai da nihiyar Afirca ya kara da cewa ba ko tantama wadannan jiragen yakin zasu taimaka matuka wajen fatattakar Yan ta adda ganin jiragen na dauke da makaman da in an harbasu basa kuskurewa.

Kimanin matuka wannan jirginn 63 ne kasar amurka ta horas don sarrafa wandannan jiragen sumfurin A 24 Super Tunaco , ministan tsaron nijeriya da Babba hafsan sojin nijeriya sune suka karbi wandannan jiragen a madadin gwamnatin tarayya.

Join Our <a 1href=”https://t.me/hausavirals“>Telegram Group</a>
Join Our <a href=”https://twitter.com/hausanovels“>Twitter page</a>
Join Our <a href=”https://facebook.com/hausaebooks“>Facebook page</a>
Join Our <a href=”https://youtube.com/c/HAUSANOVELSTV24“>Youtube Channel</a>

Comments

table of contents title