Main menu

Pages

Gwamnatin Zamfara ta rufe dukkanin Makarantun Jihar

Labarai da dumi-duminsa na cewa Gwamnatin jahar dake Nijeriya Zamfara ta bayar da umarni da a rufe dukkanin makarantun jihar baki daya,

Kwammishi nan yan sandan jihar Zamfara cp Ayuba N Elkana ya tabbatar da ɗaukar matakin a wani taron manema labarai da akayi ranar Laraba da ta gaba ta, ya ce matakin ya shafi makarantun secondary na primary ne.

Also Read Har yanzu ban samu mijin da ya dace na aura ba Inji – Adama Kamaye

Sannan kuma ya kara da cewa sanya dokar hana fita da dare a dukkanin kananan hukumomin jihar Zamfara su 14.

Dokar dai za ta fara aiki ne daga karfe 6pm na yamma zuwa 6am na safe a kananan hukumomi 13 dake fadin jahar.

A babban birnin Jihar wato Gusau, dokar za hana fita za ta fara aiki daga ƙarfe 8pm na dare har zuwa ƙarfe 6am na safe.

Wannan na faruwane bayan samun labarin sace dalibai da dama a wata makarantar secondary ta Kaya a yankin karamar hukumar Maradun.

Join Our <ahref=”https://t.me/hausavirals“>Telegram Group</a>
Join Our <a href=”https://twitter.com/hausanovels“>Twitter page</a>
Join Our <a href=”https://facebook.com/hausaebooks“>Facebook page</a>
Join Our <a href=”https://youtube.com/c/HAUSANOVELSTV24“>Youtube Channel</a>

Comments

table of contents title