Main menu

Pages

Har yanzu ban samu mijin da ya dace na aura ba Inji – Adama Kamaye

Har zuwa yanzu ban samu mijin da ya dace na aura ba inji Jaruma Adama Kamaye na shirin “Dadin Kowa”

Fitacciyar jarumar nan wacce ta yi suna a cikin shirin mai dogon zango nan wato  “Dadin Kowa”, Series Hajiya Zahra’u Sale wacce kuka fi sani da Adamar Kamaye, acikin shirin.

Jarumar ta bayyana burin da take dashi na yin aure, a kowani lokaci matukar in ta samu irin mijin da take bukatar ta samu a rayuwa.

Also Read Babban Zunubi ne talaka ya dube ni ya ce yana sona, Jarumar Film Nollywood

Fitacciyar jarumar ta “Dadin Kowa” ta sanar da haka ne a wata hira ta musamman da tayi da jaridar Dimokaradiyya, inda suka tambaye ta ko tana da sha’awar yin aure kuwa a halin yanzu, ganin yadda shekarunta suka ja.

Adamar ta ce:

“Ba ni da aure a halin yanzu, sai dai ina da niyyar yin aure, idan Allah ya kawo mun miji nagari irin wanda nake mafarkin samu zan yi aure. To Amma ka san su maza har kullum ba sa yi wa mata adalci, wani lokacin kuma matan suma ba sa yi wa maza adalci to amma ina son, duk wani mai kauna ta da masoyana baki daya da, su taya ni da addu’a Allah ubangiji ya ba ni miji nagari wanda za mu zauna lafiya ni da shi” a rayuwa ta inji ta.

Join Our <a href=”https://t.me/hausavirals”>Telegram Group</a>
Join Our <a href=”https://twitter.com/hausanovels”>Twitter page</a>
Join Our <a href=”https://facebook.com/hausaebooks”>Facebook page</a>
Join Our <a href=”https://youtube.com/c/HAUSANOVELSTV24″>Youtube Channel</a>

Comments

table of contents title