Main menu

Pages

Labari Da Ɗumi Ɗumi yadda Yan banga tare da Yan Sanda sun hallaka shugaban yan bindiga a jihar Neja


Jami’an Rundunar yan sanda ta masu yaƙi da masu garkuwa da mutane, tare haɗin guwiwar ƴan wasu ya  banga sun sheke wani Kasurgumin shugaban yan bindiga,mai suna Jauro Daji, a cikin jihar Neja tare da wasu masu goya masa baya da dama a wani farmakin da aka kai musu a ranar Litinin.

Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa rundunar hadin gwiwar sun hallaka dan Bindiga da magoya bayansan ne a yankin Kontagora dake jihar  Neja a nijeriya.

Also Read Gwamnatin Zamfara ta rufe dukkanin Makarantun Jihar

Waau Majiyoyi, sun shaida ƴan sandan sun yi amfani da sahihan bayanan sirri da suka tattara ne suka yi wa ƴan fashin dajin Kofar rago, a inda suka hallaka Jauro Daji tare da wasu yaransa a yayin da suke ƙoƙarin tsallaka wani rafi cikin dajin, don kai farmakin garkuwa da mutane a wani gari.

Wani jami’in leƙen asiri ya shaida wa majiyar mu cewa: “ Rundunar haɗin gwiwar ta ƴan sanda da ƴan banga na yankin ne suka kashe Dan bindiga Jauro Daji tare da wasu yan bindigan waɗanda ke shirin kai hari wani ƙauye domin yin garkuwa da wasu mutanen.

Mun sanya gwanayen ruwa a yankin da su kwaso mana bindigu dake hannun wasu daga cikin yan ta’addan da aka sheke aka kuma jefa gawarwakinsu cikin kogi.

Join Our <a href=”https://t.me/hausavirals”>Telegram Group</a>
Join Our <a href=”https://twitter.com/hausanovels”>Twitter page</a>
Join Our <a href=”https://facebook.com/hausaebooks”>Facebook page</a>
Join Our <a href=”https://youtube.com/c/HAUSANOVELSTV24″>Youtube Channel</a>

Comments

table of contents title