Main menu

Pages


 *💙🤍BARIKI💙🤍*

        _(Gado nah)_

Book 1

Page 3&4


Oum Aphnan✍️


*Gargaɗi*

Littafina Na kuɗi ne ,ban yarda A ɗaukar mun a saka a kowata kafa ta yanar gizo ba.



           _Gidan Makaman Gari_


Gidane Tafkeken gaske,Na dandaɓaryan ginin laka,amma an masa zanen gidan sarauta da Hannun magini Tundaga fuskar gidan har can sama wajen indaroron da yike fidda ruwan saman soron gidan musamman lokacin damina....., Gidane mai zurfin gaske da sai ka wuce zauruka guda tara masu tsananin duhuwa,wanda tsabagen duhu da rana sai an sakawa zauran tsakiya fitilar aci balbal. Gidane na dangi ɗaya mai ƙunshe da sasuka biyar ,wanda yafi kowanne girma nan ne sasan MAKAMA


Kaf gidan sasan Makamane kaɗai aka mulmule da sumunti ,akayi wa ƙofar ɗakunan matarsa biyu shaye a gaban ɗakunan su ,kaman varenda luwai da sumunti ,amma sauran tsakar gidan dandaɓaryar ƙasa ne tataaa iya ganinka ,sai ƙatuwar bishiyar mangoro da ta cika sassan da rassan ta wanda ya baiwa ilahirin yaran makama inuwa ,nanne wajen daka da sussuke nanne wajen shimfuɗa taburma aci abinci ko hira .



Ɗuƙe take a ƙarƙashin turken dokin makaman sai faman yankewa dokin farata take da abun datsewa ,gefenta munjagara ne ta kwashe rankatakaf dattin dokin ta tara a gefe ,tana jiran ta ida yankan kofaton ta kwashe ta ɗure a buhu 


Ba zato ba tsammani taji an ƙwalla mata kira


"Balkisu?....Balkisu wai kina Ina ne?" 


A furgice ta saki abun yankan ,ta ɗago ta sharce zufan da ya tsatsafo mata a goshi 


Buɗe iya Muryar da ilahu ya bata tayi ta Amsa da "Na'am umma ina zuwa" ta kwasa a guje zuwa hanyar ɗakin su .


Sadiya da Rahma dake zaune ƙarƙashin Inuwar mangoro ,kallonta sukayi ta yanko a karce suka bushe da dariya 


"Wohoho iska na wahalda mai kayan kara ,ƴar na gada ,a gama iyayin dai tas ,ƙarshen alawa ƙasa an tsotsa iskanci dai a nono ko ya kikace sadiya" 


Daganan rahma ta miƙo hannu suka tafa da safiya 

 ɗan jim tayi ta kasa motsa ƙafarta bare ta tafi ,habaicin ƴan ubanta na ɓata mata rai amma ya ta iya? Ji tayi tamkar yau ɗai ta tamka su ,saidai Ummanta ne a wannan karon ta kuma ƙwalla mata kira harda ƙari da mulmuleliyar Ashar. 


Ɗauke kai tayi ta shige ɗakin da sauri "Gani umma"


 Wata ƙosashiyar Hajiya na gani zaune cikin adon doguwar rigar Atamfa ,kan ɗaya daga cikin jerin wasu ƙosassun kujeru zaka rantse da Allah ɗakin nan ba a cikin gidan yike sbd ynda yasha adon manyan dardumai en Saudi da tafka tafkan labulai ,fanka na sama da na tsaye sai wulwuli suke yi suna fidda Iska 


Hannunta riƙe yike da wayarta tana shafa shi a hankali ,tamkar ba itace ta ƙwalla kiran Bilkisu ba da manyan Ashar ɗin da ta zuzzuba .


Ɗan raɓewa Balkin tayi a ƙofa ta riƙe labule,tana kallonta a ido a ido

  

"Na'am Hajiya mama gani"


Kafeta tayi da daƙwa ²n Idanuwarta cikin tsantsan takaici ,A ranta tana ƙissima wai ɗiyata ce wannan??


Hakan ya bani daman yi mata kallon tsaf Ni kaina.


MashaAllah Yarinya ce matashiya da bazata haura shekaru Goma Sha huɗu ba ,saye cikin   wata dark maroon ɗin Abaya da yayi mugun dacewa da kalar fatar jikinta ,farace ,irin tar tar ɗin nan kyakyawace ita tun yanzu kafin maƙerin ƴan mata ya ida zanota ,saidai ƙafafuwan ta da hannunta sunyi futu futu da ƙoran sasan doki


"Balkisu ke wata irin jaka ce? Eyee ?"

Sunkuyar da kai tayi cikin sadaƙarwa tasan yau zata lallasu 


"Jibi jikinki...in ƙici in ƙi sha in siya maki Riga dubu sha takwas kije ki gurfana a turken doki kina ma dawakan ubanki bauta ? "


Karkaɗe hannuwarta ta shiga yi "Umma hannu ne kaɗai na ɓata Allah bansa gwuiwana a ƙasa ba ,kin ma gani" 


Wani malolon takaici ne ya ɗebeta ta rarumi wani kofin gefenta ta cillota dashi .

Tsalle ta daka tayi baya da sauri


"Kina taka ƙofar ɗakin nan sai na lahira ya fiki jin  daɗi ,kinsan ke nike jira da inda zamu ko?"



Cikin rawar jiki ta ɗauki buta taje ta wanko ƙafarta da hannu ta shafa Vaseline ta wuce kwabanta ta ɗauki hijabinta ta saka ,ta fito falon ta sameta tana nan zaune tana aikin shafa waya 


Kallon wutsiyar ido tayi mata ,kana tace "mayafin kayan fa?" 


Idonta fal ƙwalla ,ta sunce hijab ɗin ,ta warware ɗankwalin da ta kindima ɗauri dashi ta ɗan naɗeshi a wuya


Sai sannan ta ɗan sakar mata ɗan murmushi 

"Maza jeki wajen matar audu in ta gama shirya Abdul ta bakishi ,mu tafi" 



Da  "Tohm umma"  ta Amsa ,ta fice zuwa farfajiyar gidan , fuskarta ba yabo ba fallasa ,Su sadiya sai sannan suke karyawa da wata irin tsinkakkiyar koko da ƙuli ƙuli ba sugar,aun barbazu ƙuda sai parade suke a inda suke 


Raɓesu tayi ,ta shige ɗakin matar audu ,wacce ta kasance matar wan babansu ne da ya rasu amma ƴar ɗakin umman bilki ce sosai ,duk wani jugu jugu da yaranta ,hidimar makaranta ,wanke ² itace duk don ta ɗan bata abu mai daɗi 


"Mama Sala wai ki kawo Abdul zamu tafi " washe baki tayi ,ta zabura ta saɓa Abdul a kafaɗa kamar ƙaramin baby 

"Je kira Habu yanzu na gansa zai fice aiki kinga sai ya sauke ku da ɗan sahunsa ' 


Da sauri tayi hanyar sauro saboda kar ya fice basu haɗu ba


"Habu ance ance ka jira mu zaka kaimu hanwa da umma yanzu  gamunan zuwa"  ta faɗa da muryanta mai kama dana shagwaɓaɓun yara 

"tohm banda abinki bilkisa ai aiki zani,wayace ki kirani??" 


"Mamanku"

"To kuyi maza ina jiran ku a bakin garko" 


" uhmmm " ta faɗa tana juyawa da sauri dan gani take kaman lokaci baya tafiya ta juya abinta ta tafi ,Bako  gaisuwa dama bai ɗaura aka ba inji ɓarawon hula....Inda sabo ya saba yaran basa gayar da mutane,itace ma mai saffa saffa tunda ba rashin kunya 


Tana hanyar Juyawa  saiga Mamanta ,ta fito hannunta riƙe da ƙanninta kallonta tayi ta kwasa mata harara ,ɗan nishi ta tsaya yi,kafin tace "Maama wai ya fito dashi mu yike jira " 


"Ke ja can bani wuri ballagaza kawai" daga haka ta wuceta anan tsaye , noƙai noƙai tabi bayanta suka wuce ,kofar gidan shake yike da tsoffi  wanda yawanci iyayen mijinta ne ,amma haka ta shori takalmarta tayi waje da shararan mayafi ta faɗa ɗan sahun Habu  suka bar unguwar.


******

Gidan Commisioner of Police (CP)


Hajiya Ladi wanda Akewa laƙabi da _Ladi Police_ Zaune take a makeken falon ta sanye cikin kayan Barcin ta ɓingilar riga rabin cinya mai jikin Nylon da yabi tsokar jikinta ya lafe ,matace shirgegiyar gaske ,ta ɗaura ƙafa ɗaya kan Table ɗaya ta Aje a ƙasa ,mazan kukunta sai kaiwa da kawowansu suke suna gudanar da Aikace²n Girkin gidan .


Tunda Napep ɗin ta tsaya ita ta fara fita bata jira umman nata ba ta zura cikin gidan da ƴar gudunta 


"Anty Ladi Ina kwana"

Ware  hannu tayi ta miƙo mata alamar ta shiga jikinta ta rungume ta 


"Oh my daughter yakike ,ina mama?" 

Lafewa tayi akan makamakan nonuwan Hajiya ladi sannan ta nuna mata ƙofa daidai sanda su Hajiya binta suke shugowa 


"Aminiya Barka da zuwa " 

A hankali ta zame Balkisu a jikinta ta muskuta ta miƙe sukaje suka rungume juna ,a hankali cikin dubara ta maka ma ɗuwawun Hajiya bintan ɗan marin wasa "Washhh ƙawata ya yau "


"Zuii na faɗa maki, ya week End ɗin" 


"Wallahi lapiya "  daidainan CP ya shiga gangarowa daga stairs yina Amsa waya cikin Shirin fitarshi 


Yina hangota ya shiga washe mata baki tun daga Saman matakalan benen har ya sauko ,sakin juna sukayi da hajiya Ladi ta  koma kan hannun kujera ta zauna ,itakuma yina zuwa ya kashe wayar ya miƙa hannu suka tafa da Hajiya bintan "Baby girl...Baby girl " 


"Alhaji Bala gomnati...Mai Ƴan sanda mai motoci ,to ya ?"

"Wallahi komai daidai ,kin gani ina hanyane mai girma gomna zai shigo zarian zan sorting yarana da zasu taho tare "


"Eh naga Alama ,to bye" kashe mata Ido ɗaya yayi "Baby girl...Baby girl😉",ya sake maimaita Nick name ɗin Hajiya bintar yina nufan hanyar waje ,gamida ɗagawa matarsa Hajiya Ladi da take zaune ,gefensu Bilkis tana jin shirmensu tana masu wasa ,ko A jikinta da irin shaƙuwar da ke tsakanin Mijinta da so call Aminiyarta .

Ɗaga masa Hannu itama tayi daganan suka canjawa yara channel zuwa cartoon ,ta kira maid ɗinta ya kawo ma su Freshyo da cake ,suka barsu a falo ita kuma ta wuce da Aminiyarta inner room ɗinta


Suna wucewa Bilkisu ta cuno baki cikin takaicin rainin wayon da ake mata "Har yanzu fa matan nan kallon yarinya suke mun ,hmmm"


Tana nan zaune,Abdul yina riƙe da freshyo a hannu yina ɗan zuƙa har barci ya sureshi ya daina kallon ,aiko tana ganin hakan itama ta saɗaɗa ta fice .



©Alheri Writers Association




_*O & A ORGANIC SKIN CARE🤏🏻 AND BODY CARE PRODUCTS🥰*_


🪀 09065990265


Menene Burinki?

Burina ,shine , In zama Sarauniyar mata ,Tauraruwa ta gaban goshin me gida ,Babbar babes tsole Idon manyan gayu a town ,Saidai kash Abubuwa da Dama sun mun cikas ,wanda suke dakusar mun da self Images ɗina da self Esteem ,kama daga 

*Black spots*

*Pimples*

*Sun Burn*

*Knuckles*

*Rough skin* Dasauransu 


Ga kuma ni na tafi 1 ɗina 

*Ba Nono*

*Ba ɗuwawu*

*Ba lafiyayyiyar fata,mai laushi ,sheƙi da Glowing*


Hakane?? Sune Damuwarki???


Tom In sune Kakarki ta yanke saƙa dama ga sallah na matsowa mata an fara tanajin Atamfar sallah zoki gyara skin ɗinki shine farkon Gayunki 


Domin kuwa A wajen Oum Aphnan ne kaɗai zamu baki product ɗin mu ba shayi ki amfani dashi kisha mamaki ,ke in ma baiyi ba akwai refund ,ma'ana zan dawo maki da kuɗinki 


Product ɗinmu kala kala ne ,Akwai :



*1)  Mayukan ɓatarda munanan Tabon Fuska, Knuckles na gaɓɓan yatsun Hannu ,da na gwuiwoyin Ƙafa da Hannu Da tabon dake fita silar zafin Rana wato Sun burn☹️*


*2)  Mayukan da zai saki Haske inke fara ce kiyi tar Kalar gaban Mota😉*


*3)  Mayukan Da Inke baƙace zaki zama Chocolate ,kala mai zafi mai bada ciwon kai ga ɗan karan wuyan samu ,Ki shimfiɗa hannu ki zagi Hannun fararen Fata, kiga kowa na ɓoye nata🤦‍♀️🤣*



*4)  Ina da Mayukan da nike Haɗawa yara daga Shekara 1 zuwa 12 years ,Mun sani sarai kula da Fatar yaro shi yafi komai wuya dakin fara ɗanki yayi haske bauuu a fara surutu wance nawa ɗanta bleaching,zo in baki ƙaryar hassadar maƙiyi ,don shi wannan skin ɗin yaronki ne zai ƙashashar ,kalar ƴaƴan turawa ban cire maki fari ko baƙi ba ,ai a gyara ake gane Ajebota da Ajeɓaku🤪*


Bayan Mayuka ,Munada💊 Supplements Kala kala ,Marasa Illa ,Giredi Gangariya Tafiyayyu daga Thailand.....Mun sani sarai jabun kaya sunyi yawa ,Harma ki kasa tantance mai kyau da Fake ,To kukanki ya ƙare ,this 1 Original ne Hajiyar  Allah ,Tafiyayyayyu ne 🛫daga  Thailand  Sai Ƴan Egypt Amma fa na Manyan kai ne ,Ba ina nufin Wacce ta tara dollars kaɗai ba ,uhm uhm harda wacce ta shirya gyara domin fizgo martabarta ,don sarai mun sani wacce ta Isa da kanta itake gyara


 

Inkin shirya siya sai ki tuntuɓeni ta nan 09065990265

[5/31, 22:13] 😘😘😘: *💙🤍BARIKI💙🤍*

         _(Gado nah)_

Book 1

author-img
Talented Aurthor, blogger in fashion and YouTuber in habits, I am living in keffin Magaji Dan Yamusa, Nasarawa state Nigeria, I am specialist at any kind of webdesign,webdevelopment, graphics designer and video editing I can make inpossible to possible with my laptop

Comments

table of contents title